Follow us in
Follow us in

FALALAR ZIYARAR ARBA’IN

Ziyartar Imam Husain (A.S) musamman a ranar Arba'in tana da tarin falaloli masu yawan gaske. gafarar zunubai,alamar imani, makwabtaka da Ahlul-baiti a aljanna, na kadan daga cikin wannan falaloli.

 

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Allah ya yi dadin tsira ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka.

Matsayin ziyarar Arba’in

Magana a kan ‘Ziyarar Arba’in’ ta samo asali ne tun zamanin Imam Ja’afar Sadiq (A.S). wani abin mamaki shi ne, duk da cewa akwai tsoro da razani na mulkin azzaluman lokacin, mutane sun kasance suna tambayar Imam cewa duk da tsoron ‘yan leƙen asiri da wakilan gwamnati, shin za mu iya tafiya ziyarar Sayyidush-Shuhada? Amma Sai Imam ya ce ‘Eh’ za ku iya tafiya.

Lallai wannan ba karamar Magana bace wadda take karfafa tafiya zuwa ziyarar Arba’in din Imam Husain, saboda tana nuna muhimmancin ziyarar Imam Husain (A.S), abin la’akari a nan shi ne cewa malaman fikihu na Shi’a a batun aikin Hajji suna cewa daya daga cikin sharuddan samun ikon yin aikin Hajji shi ne ‘aminci; wato sai an sami tsaro da aminci, idan babu tsaro, ikon yin Hajji ba ya tabbata. Amma dangane da ziyartar Sayyidush-Shuhada (A.S), ko da babu tsaro, Imam Sadiq ya karfafa tafiya ziyarar.

karfafa a kan ziyartar Imam Husain a ranar Arba’in

akwai babi guda da yake Magana a kan karfafawar ziyarar Arba’in da ya zo a cikin littafin Wasa’ilush-shi‘a, «باب تاکّد استحباب زیارت الحسین (علیه‌السّلام) یوم الاربعین من مقتله و هو یوم العشرین من صفر» ‘Babin ƙarfafar mustahabin ziyarar Imam Husain (A.S) a ranar Arba’in daga shahadarsa, shi ne ranar ashirin ga watan Safar’.

A kwai ruwayoyi da dama da ke bayyana wannan ƙarfafawar amma saboda nufin takaita rubutun za mu kawo kadan daga ciki.

Ya zo a cikin littafin kamiluzziyara cewa Imam Sadiq ya ce;

عنْ أَبِی عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ: «حَقٌّ عَلَى الْغَنِیِّ أَنْ یَأْتِیَ قَبْرَ الْحُسَیْنِ ع فِی السَّنَةِ مَرَّتَیْنِ وَ حَقٌّ عَلَى الْفَقِیرِ أَنْ‏ یَأْتِیَهُ فِی السَّنَةِ مَرَّةً.» (کامل الزیارات، ص 293)

An karbo daga Imam Sadiq (S.A) ya ce; hakki ne a kan mai arziki ya ziyarci kabarin Imam Husain (A.S) sau biyu a shekara, kuma hakki ne a kan talaka ya ziyarce shi sau ɗaya a shekara.”

Falalar ziyarar Imam Husain (A.S)

Ziyarar Imam Husain tana da tarin falala mai yawan gaske kuma akwai ruwayoyi masu yawa a kan haka, ga wasu daga cikin su;

Alamar imani

Hadisi na farko daga Imam Hasan al-Askari (A.S), ya ce:

علامات المؤمن خمس، صلاة الخمسین، وزیارت الاربعین، والتختّم فی الیمین، وتعفیر الجبین، والجهر ببسم الله الرحمن الرحیم

‘Alamomin mumini guda biyar ne: yin raka’a hamsin (har sallolin nafila) a kowace rana, ziyarar Arba’in, sanya zobe a hannun dama, da dora goshi a ƙasa (yayin yin sujjada), da bayyana faɗar Bismillahir Rahmanir Rahim (a sallah).

Zama makwabcin Ahlul Baiti (A.S) a Aljanna:

عَنْ أَبِی عَبْدِ اللَّهِ ع قَالَ مَنْ أَرَادَ أَنْ یَکُونَ فِی جِوَارِ نَبِیِّهِ وَ جِوَارِ عَلِیٍّ وَ فَاطِمَةَ فَلَا یَدَعْ زِیَارَةَ

الْحُسَیْنِ ع (کامل الزیارات، ص 293)

Daga Imam al-Sadiq (A.S) ya ce:  Duk wanda yake so ya kasance makwabcin Annabinsa (S.A.W) da makwabcin Ali da Fatima (A.S), to kada ya bar ziyarar Imam Husain (A.S).

Gafarar zunubai

رُوِیَ : «أَنَّ اللَّهَ یَخْلُقُ مِنْ عَرَقِ زُوَّارِ الْحُسَیْنِ ع مِنْ کُلِّ عَرَقَةٍ سَبْعِینَ أَلْفَ مَلَکٍ یُسَبِّحُونَ اللَّهَ وَ یُهَلِّلُونَهُ وَ یَسْتَغْفِرُونَ لِزُوَّارِ الْحُسَیْنِ‏ إِلَى أَنْ تَقُومَ السَّاعَةُ.» (جامع الأخبار، ص 25)

An ruwaito cewa; Allah ya na halitta daga gumin maziyartan Imam Husain (A.S) Mala’iku dubu saba’in daga ko wane gumi, suna yin tasbihi da tahleel ga Allah, kuma suna roƙon gafara ga masu ziyara har zuwa ranar kiyama.

A taƙaice, ziyartar Sayyidush-Shuhada (A.S) a ko wane lokaci mustahabbi ce, amma a wurare na musamman da lokuta na daban an ƙarfafa shi wannan mustahabbin, kamar ziyarar Arba’in kuma Ahlul Baiti suna so a ci gaba da tunawa da kuma raya suna da rayuwar Imam Husain (A.S) ta hanyoyi daban-daban. Saboda haka ne, Ahlul-bait (A.S) su ka yi abinda  mutane a duk shekara za su kasance suna tuna Sayyidush-Shuhada (A.S).

Halartar  wannan wuri mai tsarki (karbala) yana da tasiri da albarkatu na musamman; har ma Imam Hadi (A.S), lokacin da ya yi rashin lafiya, duk da cewa shi ne Imam kuma hujjar Allah, amma ya aika mutane zuwa Karbala domin su yi masa addu’a.

A ƙarshe, yanayin lokaci da wuri tabbas suna da tasiri, shi ya sa ranar Arba’in wannan mustahabin ya fi karfi; saboda ya samo asali ne daga shiryatarwar Ahlul Baiti (A.S) kuma a hankali ya zama alamin Shi’anci da soyayyar Ahlul-bait (A.S).

 

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :