Follow us in
Follow us in

Gaza: Cikin Hawaye a Lokacin Farin Ciki

A duk shekara, lokacin Babbar Sallah na zuwa da farin ciki ga al’ummar musulmi. Ana ganin wannan rana a matsayin lokaci na ibada, hadaya, zumunci da yafe wa juna. A Makka, alhazai suna tsayuwa a Arafat cikin kuka da addu’a. A duniya baki ɗaya, iyalai na hada kai wajen yanka dabbobi, rabon nama, da raya zumunci. Tufafi na musamman ake dinkawa, yara suna wasa, manya na addu’a da nuna godiya ga ni’imar Allah.

Amma, ba kowa ne musulmi ne ke cikin wannan yanayi na annashuwa ba. Akwai wani yanki da ya zamto tamkar gabar jini da kuka — Gaza. Wani bangare ne na duniya da ya zamewa musulmi ‘yan uwanmu tamkar ramin wuta a wannan lokaci.

Gaza a Lokacin Babbar Sallah

Yayin da duniya ke murna, Gaza na kuka. Wurin da yaki da harin bama-bamai suka mayar da titi kango, gida kuwa kabari. Ba za ka ga murna ko dariya a titi ba, sai karar jirage masu saukar ungulu, karar harbin makamai, da karar jiniyar motar daukar marasa lafiya.

An hana Gaza iska da ruwa, an katange abinci da magani, an kulle hanyoyin fita da shiga. Yara suna mutuwa ba saboda rashin lafiya,  babu iskar shaka ko wutar lantarki. mutane basu sani ba ko za su wayi gari da rai ko a’a.

A Gaza, Babbar Sallah ba rana ce ta murna ba — rana ce ta ƙara yawan kaburbura.

Yin Bikin Sallah Lokacin da ‘Yan Uwa ke Cikin Wahala

A matsayinka na musulmi, ka taɓa tambayar kanka: Shin ya dace na sha ruwa mai sanyi, yayin da ‘yar’uwata a Gaza ke shan hawaye? Shin ya dace na yanka rago mai ƙiba, yayin da ɗan uwana a can ke fama da yunwa?

Wannan tambaya ce da ya kamata dukkaninmu mu yi wa kanmu. Ba domin mu hana kanmu ni’ima ba, amma domin mu tuna cewa muna da alhakin juna. Manzon Allah (SAW) ya ce:

“Misalin muminai a cikin soyayya da jin kai da tausayi a tsakaninsu, tamkar jiki daya ne: idan wani sashi ya kamu da ciwo, sauran jiki na jin radadinsa”.

Idan Gaza tana kuka, amma duniya tana dariya, to akwai matsala. Ba wai murna ce haramun ba, amma rashin jin tausayin ‘yan uwa ne matsala. Mun rasa tausayi, mun mayar da Gaza kamar wani fim din Netflix — muna kallo amma ba mu ji ba.

Gazawa: Jurewa, da Tawakkali

Gaza ba sabon yanki ba ne. Yanki ne mai tarihi, masu karatu da malamai, masana da marubuta, mata masu juriya da yara masu basira. Amma tsawon shekaru, sun kasance cikin kulle da azaba, saboda kawai sun dage wajen neman ‘yancinsu.

Sun gaji, sun sha wuya, sun rasa dangi da abokai. Amma har yanzu ba su fasa ba. Har yanzu suna sallah cikin kango, suna karatun Alkur’ani cikin duhu.

Me Ya Kamata Muyi?

Wannan lokacin Sallah, idan har zuciyarmu ba ta tuna da Gaza ba, to lallai mun rasa wani bangare na imaninmu. Ga wasu abubuwan da zamu iya yi:

  1. Addu’a: Ka sanya Gaza a cikin kowace Sallah da kowace addu’a. Allah yana jin kukan zuciya.
  2. Bayar da taimako: Akwai kungiyoyi da ke karbar taimako, ko dan kankani, don kaiwa ‘yan Gaza.
  3. Yada gaskiya: Ka yi amfani da kafafen sada zumunta don fadakar da duniya. Kada ka yi shiru.
  4. Nasiha da tunatarwa: Ka sanar da ‘yan uwa a gida da masallaci halin da ake ciki.
  5. Ka taya su da zuciya: Kada ka bar Gaza ita kadai — nuna cewa kana tare da su.

Kammalawa: Idan Gaza na kuka, mu daina dariya

Lokacin da wasu musulmi ke cikin wahala, farin ciki na mu ya kamata ya kasance mai tausayawa. Duk da cewa muna cikin ni’ima, mu tuna cewa ni’ima ba har abada ba ce, kuma Allah yana gwada bayinsa ta hanyoyi daban-daban.

A wannan Sallah, ka tuna da Gaza. Ka saka su cikin zuciyarka, addu’arka, da aikinka. Gaza tana cikin zuciyarmu — idan muka duba.

 

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :