Halayen Imam Sadiq (A.S) daya kamata mu koya a cikin rayuwarmu
Imam Ja’afar al-Sadiq (A.S) a matsayin Imam kuma jagora yana da siffofi masu kyau da za a iya ɗauka a matsayin abin koyi. Kowanne daga cikin waɗannan siffofin na iya zama misali ga masoyansa. Don haka, za mu kawo wasu daga cikin waɗannan siffofi, bisa fatan cewa ko albarkacin samuwarsa, mun sami damar koyi da su, mu kuma tsarkake halayenmu da su a aikace:
Na daya: “Ibada da Ma’rifa da Cikakkiyar Bauta”
Imam al-Sadiq (A.S), kamar yadda kakanninsa suka kasance, ya kasance a matsayin jagoran masu ibada da masu ƙaunar Allah. Yana cikin manyan bayin Allah ta fannin tsoron Allah, addu’a, sallah, da tunawa da Allah – har ya kai matsayi mafi girma daga cikin mutanen zamaninsa.
Wadannan halaye sune kamar haka;
Karanta Alƙur’ani kamar ana masa Wahayi:
An ruwaito cewa Imam al-Sadiq (A.S) yana cikin sallah yana karanta Alƙur’ani, sai aka ga ya fita daga halin zahiri kamar yana cikin halin wahayi daga Allah. Da ya dawo cikin halin zahiri, sai aka tambaye shi me ya faru? Sai Ya ce: “Na maimaita ayoyin Alƙur’ani har na ji kamar ina jin su kai tsaye daga wajan Allah ko daga mala’ika Jibrilu.”
(Bihar al-Anwar, j. 47, shafi na 58)
Tasbih a cikin Sallah:
Aban ibn Taghlib ya ce: “Na shiga wurin Imam al-Sadiq (A.S) yana cikin sallah. Sai na tsaya ina ƙirga tasbbihinsa a ruku’u da sujuda – sai na samu ya yi tasbih sau sittin.”
(Bihar, j. 47, sh. 50)
Salla da Jama’a:
Hamza ibn Hamran da Hasan ibn Ziyad sun ce: “Mun shiga wurin Imam al-Sadiq (A.S) yana sallar la’asar tare da wasu. A cikin ruku’u da sujuda ya maimaita “Subḥāna Rabbī al-‘Aẓīm wa bi-ḥamdih” sau 33 ko 34.”
(Bihār, j. 47)
Ibada a halin rashin lafiya:
Yahya ibn ‘Ala ya ce: “A daren 23 ga watan Ramadan, Imam al-Sadiq (A.S) ya kasance cikin zazzabi da rashin lafiya. Duk da haka ya umarta a kai gadonsa zuwa Masallacin Manzon Allah (SAW), inda ya yi ibada har zuwa asubah.”
(Bihār, j. 47, sh. 53)
wannan kadan kenan daga manya – manyan Halaye ababan koyi na Imam Sadiq (A.S)