Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka.
Allah ta’alah a cikin suratush-shura aya ta Arba’in yana cewa;
وَجَزَاءُ سَيِّئَةٍ سَيِّئَةٌ مِثْلُهَا ۖ فَمَنْ عَفَا وَأَصْلَحَ فَأَجْرُهُ عَلَى اللَّهِ ۚ (سورة الشورى 40)
Sakamakon ko wane laifi marar kyau dai-dai yake da irin laifin, amma wanda ya yafe kuma ya gyara, to ladan sa na wurin Allah.
Duk wanda aka zalunta yana da zabi ko dai ya yafe ko kuma ya rama (kada ya yafe).
To amma abin tambaya a nan shi ne ko wane mutum ne idan ya yi kuskure ko ya samu zamiya ake iya ramuwa a kan sa kwatankwacin wannan abin da ya yi aki yafe masa? ko kuwa akwai nau’in mutanen da aka fi so a aikata hakan akan su?
Imam Ali (A.S) a ciki littafin nahajul-balaga a hikima ta 20 ya gaya mana irin kalar mutanen da idan su ka yi kuskure ake son a yafe musu, saboda ire-iren wadannan mutanan a duk sanda su ka yi kuskure to Allah ta’ala da kan sa ya ke kama hannayen su ya dago su sama domin kada mutumcin su ya zube.
Imam (A.S) ya yi nuni a cikin wannan hikima mai girma da kurakuran da wani lokacin sukan faru daga mutanen kirki masu mutunci. Ya yi wasiyar cewa a yafe musu, kada ace za’a rama wannan kuskuren da suka aikata. Ya ce:
أَقِيلُوا ذَوِي الْمُرُوءَاتِ عَثَرَاتِهِمْ، فَمَا يَعْثُرُ مِنْهُمْ عَاثِرٌ إِلَّا وَ [يَدُهُ بِيَدِ اللَّهِ] يَدُ اللَّهِ بِيَدِهِ يَرْفَعُهُ.
Ku yafewa masu mutumci da kirki kurakuran su, domin babu wanda ya ke yin kuskure daga cikinsu face (hannun sa yana hannun Allah), hannun Allah yana ɗago shi.
Asalin Kalmar “أَقِيلُوا” an samo ta daga “اقالة” ne, asalin ma’anarta ita ce fasa ciniki bayan an kulla shi, lokacin da mai saye ya yi nadama. Amma daga baya, ana amfani da kalmar ga duk wani abu da ya shafi yafiya da kawar da kai daga laifi a kowane irin yanayi.
Kamar yadda Kalmar “الْمُرُوءَاتِ” jam’i ce ta “المروءة” ma’anarta ita ce mutunci, daraja da dattako.
Kalmar “عثرات” kuma jam’i ce ta ‘عثرة”, wadda ke nufin kuskure ko faɗuwa.
A bayyane yake cewa kowane mutum in dai ba ma’asumi ba ne yana yin kuskure ko zamiya a rayuwar sa, amma idan wannan kuskuren ko zamiyar ya fito daga mutumin kirki mai halaye na gari, ya kamata a yafe masa saboda kyawawan ayyukansa da kyautatawarsa ga al’umma.
Duk wani nau’in yada wannan kuskuren ga mutane, ko suka ko zuzutawa kuskure ne babba da rashin adalci. Domin kuwa Allah da kansa ya ke kare irin waɗannan mutanen.
Imam (A.S) ya ce: Idan ɗaya daga cikin waɗannan mutanen kirkin ya faɗi, da gaggawa Allah ya ke ɗaga shi, kuma ba zai bari mutuncin sa ya zube ba.
Darussan dake cikin wannan Hikimar, Za a iya fitar da abu biyu daga wannan hikima mai zurfi:
Na ɗaya:
Kamar yadda Imam (A.S) ya fada, idan mutum mai kyawawan halaye, tsoron Allah da kyakkyawar niyya ya yi kuskure, ya kamata a yi masa afuwa. Kada mu sauya kyakkyawan zatonmu da shi zuwa mummunan zato saboda kuskuren da ya yi. Wannan yana daidaita da karin maganar larabawa da ke cewa:
“الجواد يكبوا” ko “قد يكبوا الجواد”, ma’ana: “Ingarman doki ma na iya faɗuwa.”
“الصارم قد ینبوا”, ma’ana:” Takobi mai kaifi ma kan iya kasa tasiri wani lokaci.”
Na biyu:
Idan muka bi hanyar tsoron Allah, kyautatawa da mutunci, Allah ba zai bar mu mu faɗi mu kadai ba. Idan muka faɗi, zai ɗaga mu da hannunsa, ya kare martabarmu kuma ya ɗaukaka mu.