Follow us in
Follow us in

MAHIMMANCIN HAKURI A ADDINI

 

SHIN MI AKE NUFI DA HAƘURI?

A cikin amsar wannan tambayar zamu iya ce wa: Haƙuri yana nufin juriya da jimrewa a lokacin wahalhalu da ƙalubale na rayuwa ba tare da rasa natsuwa ba. haka kuma Haƙuri wani babbar abu ne da ke bai wa mutum damar jure abin da baya so a cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

mutane da dama suna ɗauka haƙuri yana nufin yin shiru ko gazawa; amma idan muka duba a cikin haƙiƙanin koyarwar Musulunci, za mu fahimci cewa haƙuri ba yana nufin mika wuya ko ƙyale zaluncin azzalumi ba ne, sai dai yana nufin tsayawa da juriya a gaban ƙalubale da matsaloli da kuma ci gaba da fafutuka da ƙoƙari har sai an cimma nasara.

 

SHIN HAƘURI ƊABI’A CE WADDA A KE HAIHUWAR MUTUM DA ITA; KO KUMA MUTUM KOYA YA KE?

A hakikanin gaskiya Haƙuri na iya  kasancewa ta ko wane ɓangarori biyu, haƙuri yakan iya zama a matsayin hali da ɗabi’ar da mutum ya gada daga halittarsa, amma kuma mafi yawanci haƙurin mutane ana koyon ne ta hanyar horo da ƙwarewa. misali Mutum na iya ƙarfafa haƙurinsa ta hanyar ilimi, ibada, tunani mai kyau da kuma yin mu’amala da masu haƙuri.

Don haka, haƙuri ɗabi’a ce da za a iya koya, kuma a bunƙasa ta da ƙoƙari da horo.

 

Kamar yadda aka sani, haƙuri yana da matsayi da daraja sosan gaske a cikin addini. Akwai ayoyi da ruwayoyi da dama da su ke yi mana  bayyani akan hakuri, kamar yadda yazo daga Allah(t) a cikin  Alƙur’ani mai girma: فَاصْبِرْ کَمَا صَبَرَ أُولُو الْعَزْمِ مِنَ الرُّسُلِ وَلا تَسْتَعْجِلْ لَهُمْ کَأَنَّهُمْ یَوْمَ یَرَوْنَ مَا یُوعَدُونَ لَمْ یَلْبَثُوا إِلا سَاعَةً مِنْ نَهَارٍ بَلاغٌ فَهَلْ یُهْلَکُ إِلا الْقَوْمُ الْفَاسِقُونَ (٣٥) (سورة احقاق/٣٥)

“ka yi haƙuri kamar yadda waɗanda suke da ƙarfin hali daga cikin Manzanni suka yi haƙuri, kuma kada ka yi gaggawa a kansu. A ranar da suka ga abin da aka yi musu alƙawari, kamar ba su zauna (a duniya) ba sai wani lokaci kaɗan na rana. Wannan wata isar da saƙo ce. Shin waɗanda za a halaka sai fasikai ne?”

 

Kamar yadda mu ka sani haƙuri ya na daga siffofi mafi kyau da ya kamata ko wane dan adam ya kasance dashi, sufa ce da dukkanin Manzannin Allah (t) suke da ita kuma suka yi nuni da muma mu siffantu da Wannan sifa, badan hakurin Annabawa ba to da Wannan addinin bai zo gare mu ba.

A duk lokacin da mutum yake so ya cimma wani Al’amari to dole ne sai ya yi hakuri, domin da haka ne zai kai ga nasara.

Yazo daga Manzo (s.a.a.w): Haƙuri dangane da ayyuka  kamar kai ne a jikin mutum. Kamar yadda idan aka cire kai daga jiki, jikin zai lalace, haka ma idan haƙuri ya gushe daga ayyuka, ayyukan za su lalace.”

(Bihar al-Anwar, Jildi na 71, shafi na 73).

haƙuri yana rarrabu ne zuwa gida uku kamar yadda wannan ruwayar da tazo daga Manzo(s.a.w.a):

قال رسول الله (ص): «الصَّبْرُ ثَلاثَةٌ، صَبْرٌ عِنْدَ الْمُصیبَة، وَ صَبْرٌ عَلَی الطّاعَةِ وَ صَبْرٌ عَنِ المَعْصِیَة…».(اصول الكافي،ج ٢، ص ٩١.

    1. Haƙuri wajen bin umarnin Allah

    (الصبر علي الطاعة)

    “Hakuri wajan bin dokokin Allah (t) yana nufin dagewa da juriya wajen aikata duk umarni na Allah (t), da guje wa aikata duk wasu ayyuka na sabo”. lokacin da mutum ke aikata wani aiki da Allah (t) ya wajabta masa, to kada ya gajiya ko ya kasa karasa wannan aikin zuwa ƙarshe ko kuma yadda ya kamata. Alal misali, lokacin da mutum yaso ya aikata wani aiki na ibada kamar: karanta addu’o’i ko  yin nafiloli na mustahabbi, ko kuma azumin watan Ramadan, to Kada ya gajiya wajan neman kusanci ga Allah (t), ko karanta Alƙur’ani da ma wasu ayyukanna ibada.

Wannan shi ake kira haƙuri da jurewa wajan bin umarnin Allah (t).

 

  1. Haƙuri a yayin aikata laifuka da ayyuka marasa kyau (zunubi).

(الصبر عند المعصية)

Wannan yana nufin tsayuwa da jajircewa wajan ƙin aikata ayyukan saɓo.

 

“Yawancin zunubai da ayyukan da Allah (t) ya haramta suna da daɗi ne wajan aikatawa kuma abubuwan so ne ga zuciyar ɗan Adam. Saboda haka, zuciya tana kwaɗayin aikata waɗannan zunubai, har ma tana amfani da ƙarfin gaske wajen tirsasa mutum wajan  aikata su. Don haka mutum yana buƙatar nuna jajircewa da ƙarfi fiye da yadda zuciyarsa ke kwaɗayi zuwa ga aikata zunubi. Tayuwu saboda haka ne Amirul Mu’minin (a.s) ya ce:

Haƙuri iri biyu ne: ɗaya shi ne haƙuri a lokacin masifa (ko bala’i), wanda yin hakurin a wannan lokaci abune mai kyawun gaske,  amma mafi kyawu shi ne haƙuri wajen kin aikata laifuka da zunubai.’”

Kada mutum ya yarda da zuciyarsa ko shaiɗan su rinjaye shi saboda sha’awa ko kuɗi, ko mulki, ko yin suna da shahara.

Lokacin da mutum yake ƙoƙarin samun wani abu, bai kamata ya wuce gona da iri ba. Mutumin da yaso aikata lafi idanuwan shi suna rufewa ne kuma ya shiga halin gafala ya kasa tantance miye a gabanshi, kamar yaron da yaso kai hannusa kan kwanon kayan zaki, burin shi kawai ya kai ga wannan kwanon domin ya dauki abinda ke ciki ba tare da lissafin abin da ke gaban shi ba.

Don haka, sai mutum ya lura sosai da yin taka tsan-tsan wajan sanin me yake aikatawa ko kuwa me ya kama ta ya aikata  domin gujewa aikata sabo, saboda wannan bangaran a cikin  rabe-raben hakuri yafi ko wanne wuyar aikatawa.

  1. Haƙuri a kan jarabawa da musibu wanda suke faruwa ga bawa mumuni.

mutum ya kan  fuskanci ƙunci ko masifa a Al’amaran rayuwa kamar: mutuwa (rasa wani daga cikin makusanta), rashin kuɗi, rashin lafiya, damuwa, da sauran matsaloli na yau da kullum. Bai kamata wannan ya karya wa mutum kwaiwa ba, ko ya sa ya yi tunanin cewa komai ya ƙare. Haƙuri a irin wannan lokaci yana da matuƙar muhimmanci.

Abin da ya kamata mu sani shi ne jarabawar a kan bayi matakin-mataki ce, Allah subahanahu wa ta’ala ya na jarabtar ƴan adam daidai da imanin su ne, amma abinda yake mafi muhimmanci shi ne mutum ya yi kokari ya ci jarabarawar ubangiji ta hanyar yin hakuri da jajircewa.

Haƙuri be taƙaitu ba a kan abubuwan da su ka shafi mutum a kan kanshi kadai wani lokacin yana iya komawa a cikin al’amuran jama’a ko ƙasa baki ɗaya.

Misali, lokacin yaƙin kare ƙasa ya zo to dole ne mutum ya tsayatsayindaka gurin bada gudummawr da ta kamata saboda bin umarnin Allah (t), wannan abu ne da ya shafi ƙasa baki ɗaya Ba wai mutum ba akan kan shi.  Idan mutum ya tsaya tsayin daka wajen kare ƙasa, hakan yana nufin tsan-tsan biyayya ga umarnin Allah (t).

Haka ma, aikata wasu laifuka ba kawai mutum ɗaya suke shafa ba, suna iya shafar jama’a gaba ɗaya ko ƙasa. Idan wani shugaban ƙasa ya sa hannu a wata doka ko mataki mara kyau, sakamakon hakan na iya shafar rayuwar mutane da dama. Wannan ya fi laifin karɓar rashawa ko kallon abin ƙyama. Don haka, tsare kai daga irin waɗannan laifuka yana da girma matuƙa.

Haƙuri a cikin bala’o’in jama’a ma haka yake:

Lokacin da ƙasa ke fuskantar matsin lamba daga makiya, ƙarya, zargi, da ɓatanci daga kafafen watsa labarai da ƙasashen waje – wannan ma bala’i ne. Kuma haƙuri a irin wannan lokaci yana da wahala. Wasu shugabanni a duniya, sun gaji da irin wannan matsin lamba kuma sun sauka daga tafarkinsu saboda haka. Amma haƙuri a irin wannan yanayi na daga cikin manyan fannoni na haƙuri.

Saboda haka, haƙuri yana da matuƙar muhimmanci a kowane fanni na mutum da kansa ko na jama’a da ƙasa gaba ɗaya.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :