Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da amincin Allah su kara tabbata ga Annabi Muhammad da Iyalan gidansa tsarkaka.
Da farko yana da kyau mu san cewa ma’anar jarabawar Allah tana da banbanci da ma’anar jarabawa a wajan Dan-Adam, shi dan Adam yakan jarraba abu ne domin neman sanin wani abu wanda ya shige masa duhu, wanda shi kuma Allah ta’ala duk lokacin da ya jarabci mutum hakan ba ya nufin cewa Allah yana so yasan wannan mutumin ko yasan halayensa ko mu’amalolinsa domin shi Allah masani ne akan komai tun asali.
Idan kaga Allah yana jarabtar bawa to yana jarabtar sa ne domin ko wane mutum ta hanyar ayyukansa ya bayyana matsayinsa da martabar da yake da ita a cikin Dan’adamtaka.
Saboda kada Dan-Adam ya kafawa Allah hujja da cewa da ka jarrabani da na aikata kyawawan ayyuka,( لِئَلَّا يَكُونَ لِلنَّاسِ عَلَى اللَّهِ حُجَّةٌ).
Allah ta’ala ya yi nufin mutane su zo wannan duniyar ne domin bautarsa (وَمَا خَلَقۡتُ ٱلۡجِنَّ وَٱلۡإِنسَ إِلَّا لِيَعۡبُدُونِ) Ban halicci mutum da Aljan ba sai dan su bauta mini. wanda ta wannan hanyar ne bawa ke ginawa kansa Aljanna ta hanyar kyawawan ayyuka (انَّ ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ وَعَمِلُواْ ٱلصَّـٰلِحَٰتِ لَهُمۡ جَنَّـٰتُ ٱلنَّعِيمِ) Lallai wadanda su kayi imani kuma suka yi kyawawan ayyuka to za su sami aljannar Na’im.
ko kuma akasin haka, idan bawa bai yi kyawawan ayyuka ba zai gamu da mummunan sakamako (إِنَّ ٱلۡمُجۡرِمِينَ فِي عَذَابِ جَهَنَّمَ خَٰلِدُونَ) Lallai masu laifi za su kasance a cikin Wutar jahannama suna dawwamammu.
Allah ta’ala ya san duk irin aikin da Dan- Adam zai aikata a wannan duniyar tun asali, amma sai ya bari ko wane Dan-Adam ya bada jarabawa a cikin rayuwarsa domin kowa ya fahimci wane irin mutum ne shi.
Allah ya san komai amma kuma bai amshe damar bada jarabawa daga hannun Dan-Adam ba.
SIRRIN DA KE CIKIN JARABAWAR DA ALLAH KE WA BAYI
Allah Ta’ala masani ne wanda ta hanyar iliminsa ne tin fil-azal ya ke da masaniya a kan duk wata halitta,kuma tun tuni yake da masaniya a kan cewa wane ne zai bi madaidaiciyar hanya kuma wane ne zai bi mummmunar hanya, saboda da haka tambayar da zata bujuro a nan ita ce, minene riba a cikin jarabawar da Allah ya ke yiwa bayinsa kuma minene mahimmancinta in dai tun tuni Allah ya riga ya san komai a kan cewa wane ne zai ci jarabawa kuma wane ne zai fadi jarabawa?
Kafin mu amsa wanan tambayar yana da kyau mu fahimci cewa rahamar Allah tana da yalwa ta yanda duk wani bawa zai iya zama shiryayye, ba wai Allah Ta’ala ne ya halicci bawa ta yanda wani ya na iya zama shiryayye wani kuma ba shiryayye ba.
Saboda haka Dan-Adan yana da cancantar ya amfana daga rahamar Allah a doron wannan duniyar, samammen da yana da zabin kansa ta yanda zai iya kaiwa ga kamala da tsira, ko kuma ya ki yin amfani da wannan ni’imar da Allah ya yi masa ta hanyar da ta dace wanda hakan na iya kai shi ga faduwa da lalacewa (ثم رددناه أسفل سافلين الا الذين ءامنوا وعملوا الصالحات Sannan za mu mayar da Dan-Adam (saboda sabonsa da kafircinsa) mafi kaskancin makaskanta.
Saboda haka ilimin Allah a kan cewa ya riga ya san komai tun farko a kan cewa wane ne zai ci jarabawa kuma wane ne zai fadi jarabawa, ko kuma wane ne zai bi shiriya ko bata ba zai hana Dan-Adam kaiwa ga samun shiriya da tsira a wajan Allah ba.
Allah ya fada a cikin aya ta zuwa ta uku a suratul-insan cewa;
إِنَّا هَدَيۡنَٰهُ ٱلسَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرࣰا وَإِمَّا كَفُورًا mun nuna wa Dan-Adam hanya kodai ya zama mai godiya ko kuma marar godiya.
Amma idan da za’a tambaya cewa me yasa dan Adam dole sai Allah ya jarabce shi a wannan duniyar mai yasa tun farko ba’a bashi sakamakon wannan jarabawar ba?
Amsar ita ce,hakan ya saba da dalilin halittar Dan-Adam, saboda idan da ace za’a bar Dam-Adam a wannan duniyar ba tare da ko wace irin jarabawa ba,ba tare da ko wace wahala ba kuma ya zama ya kai ga duk abin da yake so to manufar halittar Dan-Adam kamar yadda muka fada a baya ba zata tabbatu ba.
Allah ta’ala bai halicci mutane a matsayin wani dan wuta wani kuma dan Aljanna ba, wuta ko Aljanna wasu abubuwa ne wanda kowa ta hanyar aikin da ya yi yakan iya kaiwa gare su, ma’ana Dam-Adam ne
Zai yi kokari wajan ganin ya samu rabon Lahira ko akasin hakan.cancantar Dan-Adam ko rashin cancantarsa suna bayyanuwa idan yazo wannan doron Duniyar ya bi marhalolin ilimi da aiki ya ketare jarabawowi da dama sannan zai tabbata. ولَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّىٰ نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنْكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ أَخْبَارَكُمْ
Tabbas za mu jarabce ku domin sanin masu kokari da masu hakuri daga cikinku kuma za mu jarabta ayyukanku.