Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka.
Adadin “Arba’in” yana da matuƙar muhimmanci a cikin sakafar addinin musulumci. Misali; Amfanin haddace hadisai arba’in, yin aiki da ikhlasi na tsawon kwana arba’in, kammalar hankali a shekara arba’in, yin addu’a ga muminai arba’in, shaidar muminai arba’in ga mamaci, da kuma aiko mafi yawan Annabawa a shekara arba’in duk suna nuna girma da sirrin da ke cikin wannan Adadi na Arba’in a Addinin musulumci.
Ashirin ga watan safar ita ce ranar da tayi dai-dai da Arba’in din Imam Husain (A.S) ma’ana daga goma ga watan muharram din da Imam Husain ya yi shahada zuwa ashirin ga watan safar din bayan shi zai kama kwana Arba’in Kenan.
Wannan wata rana ce da Mabiya mazhabar Ah’lul-baiti (a.s) suke rayawa domin cikar Imam Husain da shahidan karbala kwana Arba’in da yin shahada, to amma abin tambaya a nan shi ne, wane sirri ke cikin wannan adadi na Arba’in da yasa ba’a zabi wani adadin ba sai shi? Me yasa ba’a ce Ashirin ko Talatin ba ? goma sha biyar ko Ashirin da biyar ko Talatin da biyar ba?
Ko wani abu makamancin haka.
Saboda da amsa wannan tambayar akwai bukatar mu fara kawo mahangar Alqur’ani da ruwayoyi akan wannan adadi na Arba’in.
Mahangar Alqur’ani:
وَإِذْ وَاعَدْنَا مُوسَیٰ أَرْبَعِینَ لَیْلَةً ثُمَّ اتَّخَذْتُمُ الْعِجْلَ مِنْ بَعْدِهِ وَأَنْتُمْ ظَالِمُونَ
Ka tuna da lokacin da (saboda saukar da Attaura) mu ka yi alkawarin darare Arba’in da Annabi Musa (A.S) sai kuma (bayan Musa baya nan) ku ka riki Dan Maraki a matsayin abin bautawa a wannan hali ne (saboda wannan aikin marar kyau) ku ka zama azzulumai. ً
Sakon da wannan ayar take isarwa shi ne cewa, Ibadar darare Arba’in a nesa da Mutane yana da tasiri na musamman.( أَرْبَعِینَ لَیْلَة)
Adadin Arba’in yana da muhimmanci wajan karbar wahayi da yin Ilhami.
- قَالَ فَإِنَّهَا مُحَرَّمَةٌ عَلَيْهِمْ أَرْبَعِينَ سَنَةً یَتِیهُونَ فِی الْأَرْضِ فَلَا تَأْسَ عَلَى الْقَوْمِ الْفَاسِقِینَ.»
yace: saboda haka (wannan kasar) ta haramta a gare su har tsawon shekara Arbai’n, za su dimauce a cikin kasa saboda haka kada ka damu a kan mutanen da fasikai ne.
sakon da ayar ta ke isar wa shi ne, Mutanen banu isra’il bayan da Allah ya basu umarni da su shiga Kan’an su yaki mutanen ta domin su kwace ta, sai Banu Israil suka ki aikata haka saboda suna jin tsoron mutanen garin kan’ana da kuma kin biyayya ga umarnin Allah, saboda haka ne Allah ya yi fushi da su kuma ya gayawa Annabi Musa cewa, wadannan mutanen za su yi dimuwa a wannan waje har na tsawon shekara Arba’in, wanda a wannan shekarun za’a samu wadanda za su girma a cikin su har su shiga inda Allah yace su shiga.
Wannan dimuwa ta shekaru Arba’in ita ce natijar kin bin abin da Allah ya umarce su da shi ne.
حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَة
Har zuwa lokacin da ya kawo karfi ya cika shekara Arba’in.
daya daga cikin sakonnin da wannan ayar take dauke da shi shi ne cewa Dan- Adam yana kawo karfi ya cika hankalin sa ne idan ya kai shekara Arba’in.
Akwai maganganu masu tarin yawa akan Adadin Arba’in a sakafar addinin musulumci, amma saboda nufin takaita wannan rubutu zamu wadatu da ambaton kadan daga cikin su;
Shaidar muminai Arba’in
قال الامام الصادق علیه السلام: «إذا مات المؤمن فحضر جنازته أربعون رجلا من المؤمنین وقالوا: اللهم إنا لانعلم منه إلا خیرا وأنت أعلم به منا، قال الله تبارك وتعالی: قد أجزت شهاداتکم وغفرت له ما علمت مما لا تعلمون
Imam Sadiq (AS) ya ce: “Idan mumini ya mutu, kuma aka samu mutane muminai arba’in suka halarci jana’izarsa suka ce: Ya Allah, ba mu san komai akan sa ba sai alkhairi, amma kai ka fi mu sanin sa. Allah Mai girma zai ce: Na karbi shaidar ku kuma na gafarta masa abin da na sani wanda ku baku sani ba.
Haka kuma a wata ruwayar Imam Sadiq (AS) ya ce: A cikin Banu Isra’ila akwai wani bawan Allah da ya kasance kullum yana cikin ibada da addu’a. sai Allah Maɗaukaki ya yi wahayi zuwa ga Annabi Dawuda (AS) ya ce: “Ya Dawuda! Wannan bawan da ke gani ya shagaltu da ibada, to gaba dayan ibadar sa riya ce ba saboda da ni yake yi ba, kuma ba ya jin tsoro na baya da (ikhlasi).
Da mutuwar wannan mutumin ta zo, Annabi Dawuda (AS) sai bai halarci jana’izarsa ba, amma mutane arba’in daga cikin Banu Isra’ila sun halarci wannan jana’iza, kuma sun bayar da shaida akan alkhairinsa, kuma suka nema masa gafara da rahama a wajan Allah.
Haka zalika Lokacin da za a yi masa wankan gawa, wasu mutanen arba’in sun kara halarta, kuma suka ba da irin wannan shaidar. A lokacin binne shima haka, wasu arba’in sun sun kara zuwa suka ba da shaidar kyawawan halayensa, sannan suka roƙi Allah da ya gafarta masa.
A wannan lokaci, Allah ya yi wahayi ga Annabi Dawuda (AS) cewa: Na gafarta masa saboda shaidar waɗanda suka zo, kuma na yafe duk wani munafuncinsa da rashin ikhlasinsa.
.
Cikar kamala a Shekaru Arba’in
Daya daga cikin muhimman abubuwan da ke cikin rayuwar mutum kuma ke da tasiri a cikin ci gaban halayensa shi ne isa ga wani matakin shekaru inda mutum zai zama cikakke kuma ya kai matakin balaga.
Allah Mai girma ya bayyana cewa shekarun arba’in shine kololuwar cikar mutum, ya ce: حَتَّىٰ إِذَا بَلَغَ أَشُدَّهُ وَبَلَغَ أَرْبَعِينَ سَنَةً
“… har sai ya kai cikakken ƙarfi kuma ya kai shekaru arba’in.
Natija…
Bisa la’akari da abubuwan da aka ambata a sama, za mu fahimci cewa Adadin Arba’in wani adadi ne da yake da muhimmanci a cikin dukkanin masadir na addinin musulumci (Alqur’ani da Hadisi).
A dunkule Adadin Arba’in a cikin sakafar Addinin musulumci, yana da ma’ana mai zurfi da fadi wanda a dunkule ya ke nuni a kan cikar kamala da tsarkaka da karfafar niyya da kuma janyo rahamar Allah.