CI GABA….
Cewar Dan-Adam tun farkon halittarsa ya zama cewa mai tsarki ne , hakan ba shi da wata kima, har sai ya zo duniya ya yi aiki tukuna,idan kuwa ba haka ba to bayar da lada ko bada sakamako ga Dam- Adam ba su da wani ma’ana. Misali,Inda za’a ce yau akwai wata makaranta daga cikin makarantu sai a samu cewa a tsarin makarantar ba’a yin jarabawa sai dai kawai aga ana bayar da sakamako ga Daliban wannan makarantar, to lallai za kaga wannan sakamakon ba zai yi wata kima ba har a wajan Daliban kan su, kuma kowane Dalibi na da hakkin cewa bai yadda da sakamakon da aka ba wani ba, amma idan jarabawa aka zauna aka yi kowa ya samu iya kokarinsa to lallai wannan sakamakon zai yi kima da daraja, haka lamarin yake a tsarin wannan Duniyar.
Wannan yana nuna cewa ilimin Allah na tun kafin ya halicci Dan-Adam, da kuma sanin abin da kowa zai aikata tun kafin halittarsa, baya kore cewa jarabtar bayi bata da wani amfani! saboda da jarabawar ne hakikanin Dan-Adam din ke bayyanuwa ta yanda zai samu daraja tun a wannan duniyar da kuma tsira a gobe kiyama ko kuma ya samu akasin hakan. وَمَا تُقَدِّمُوا لِأَنْفُسِكُمْ مِنْ خَيْرٍ تَجِدُوهُ عِنْدَ اللَّهِ
Duk abin da ku ka gabartar na alkhairi za ku same shi a wajan Allah.
فَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ وَمَنْ يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ
Saboda haka duk wanda ya yi aikin alkhairi dai-dai da kwayar zarra zai gan shi. Hakama kuma duk wanda ya aikata sharri dai-dai da kwayar zai ganshi.
Adaidai wannan gabar yana da kyau mu kawo Ayoyin Qur’anin da suke nuna dole ne Dan-Adam ya gamu da jarabawa a cikin rayuwarsa ta wannan duniyar, akwai ayoyi da yawa a cikin Alqur’ni da suke magana a kan jarabawa ga Dan-Adam, amma za mu takaita wajan ambaton ayoyi biyar daga cikin su;
- وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ بِشَيْءٍ مِنَ الْخَوْفِ وَالْجُوعِ وَنَقْصٍ مِنَ الْأَمْوَالِ وَالْأَنْفُسِ وَالثَّمَرَاتِ ۗ lallai za mu jarabce ku da wani abu na daga tsoro da yunwa da karancin kayan Itatuwa da karancin dukiya da rayuka amma ka yi bushara ga masu hakuri (A cikin irin wannan yanayin)
- لَتُبْلَوُنَّ فِي أَمْوَالِكُمْ وَأَنْفُسِكُمْ وَلَتَسْمَعُنَّ مِنَ الَّذِينَ أُوتُوا الْكِتَابَ مِنْ قَبْلِكُمْ وَمِنَ الَّذِينَ أَشْرَكُوا أَذًى كَثِيرًا ۚ وَإِنْ تَصْبِرُوا وَتَتَّقُوا فَإِنَّ ذَٰلِكَ مِنْ عَزْمِ الْأُمُورِ Tabbas za ku jarabtu a cikin dukiyoyinku da kawukanku…..
- إِنَّا جَعَلْنَا مَا عَلَى الْأَرْضِ زِينَةً لَهَا لِنَبْلُوَهُمْ أَيُّهُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا lallai mun sanya duk wani abu da ke doron kasa a matsayin kayan kawa gare ta saboda mu jarabta su muga wane ne yafi kyawawan ayyuka.
- وَلَنَبْلُوَنَّكُمْ حَتَّىٰ نَعْلَمَ الْمُجَاهِدِينَ مِنْكُمْ وَالصَّابِرِينَ وَنَبْلُوَ أَخْبَارَكُمْ lallai za mu jarabce ku har sai mun san su wane ne masu kokari daga cikinku kuma su wane ne masu hakuri kuma zamu jarabci ayyukanku.
- أَحَسِبَ النَّاسُ أَنْ يُتْرَكُوا أَنْ يَقُولُوا آمَنَّا وَهُمْ لَا يُفْتَنُونَ Mutane suna zaton cewa za’a kyale su bayan sun yi Imani ba tare da wata jarabawa ba.
Allah ya halicci mutum ne kuma ya bashi ‘yanci da zaɓi a kan gudanar da al’amuran rayuwarsa, kuma ya ba shi damar zaɓar hanya madaidaiciya ko wadda ba madaidaiciya ba.
Mutum ne da kansa zai iya tsara ƙaddararsa bisa ga irin ‘yancin da Allah ya ba shi. Saboda haka, kowace ƙaddara da ta same shi, to daga gare shi ce. Wannan shi ne kyawun halittar Allah.
A bayyane abin yake, jarrabawar Allah ta bambanta da irin jarrabawar da mutane ke yi. Mutane sukan yi jarrabawa ne domin su gano ilimi da ƙwarewar mutum. Amma jarrabawar Allah kuwa, domin haɓaka mutum ne. A cikin wannan jarrabawa ce mutum ke samun ci gaba, kamar yadda iri ke girma a cikin ƙasa wahalar da iri ke sha a ƙasa ita ce ke sanya shi ya koma shuka. Haka ma wahalhalun duniya da jarrabawar mutum ke kawo masa girma da zama cikakken mutum.
Idan za mu ba da misali na rayuwa, jarrabawar Allah kamar wasanni ne inda ana yin gasa domin karfafa mutane. Ko da yake akwai cin nasara da rashin nasara a cikin gasa, amma sakamakon sa shine karfafa mutane a kan abin da suka iya. (Wannan misali ne kawai domin kusanto da fahimta, ba wai a hakika haka abin yake ba.)
A hakika, ‘yan wuta ba wai suna cikin azabar Allah ko kuma a cikin wutar da Allah ya kunna ba ne kai tsaye; sai dai suna azabtuwa ne da sakamakon ayyukansu da halayensu na banza. A cikin wutar da suka ƙirƙira da kansu ta hanyar ayyuka da tunani marasa kyau suke jin azaba. Duk da haka, mafi yawansu daga baya bayan sun tsarkaka da wutar daga ƙazantattun halaye, sukan shiga Aljanna. Wannan duka alama ce ta adalcin Allah ga bayinsa.
Idan da za’a tambaya cewa: shin mutum yana da ‘yancin zaɓi na gaskiya ?, alhali Allah ya riga ya san abin da zai faru? To, za mu ce: ilimin Allah game da abin da zai faru a gaba ba shi da alaƙa da ayyukan mutum ko sauran halittu, kuma ba ya hana mutum ‘yancin yin zaɓi. Wannan ilimi na Allah ba ya tilasta mutum yin wani abu.
Wannan yana kama da likita wanda ya san da tabbaci cewa wani mara lafiya zai shiga wani yanayi a gaba, ko kuma da la’akari da halin da yake ciki, zai iya hango ko zai warke ko cutar za ta ƙaru. Wannan sanin likita ba ya shafar yadda cutar za ta gudana ko waraka ba.
Haka ma, idan malami tun da farko ya san cewa ɗalibi zai samu sakamako mara kyau a jarrabawa, shin wannan sanin zai shafi yadda ɗalibin zai yi jarrabawar? A’a, hakan ba ya da tasiri.
Tabbas a’a, domin sakamako mara kyau da ɗalibi ke samu yana da alaƙa da dalilai na musamman kamar sakaci da ɓata lokaci daga wajan Dalibin, sanin malami daga farko ba shi da alaƙa da waɗannan dalilan. Haka nan ma, ilimin Allah game da abubuwan da za su faru a gaba ba ya tilasta mana mu aikata su ko mu bi wata takamaimiyar hanya.
Allah yana da cikakken sani game da duk abubuwan da ke faruwa a duniya — ciki har da ayyukan da mutane ke aikatawa. Amma wannan ilimi na Allah yana nufin cewa mutum yana da cikakken zaɓi; wato, Allah ya san cewa mutum ne da kansa ya zaɓi aikata duk wani abu mai kyau ko marar kyau, kuma wannan ba ya nufin cewa mutum baya da zabi ko ‘yanci a rayuwarsa.
إِنَّا هَدَيْنَاهُ السَّبِيلَ إِمَّا شَاكِرًا وَإِمَّا كَفُورًا (Suratul Insan (76), Aya ta 3)
“Lalle ne mun shiryar da shi zuwa ga hanya, ko dai ya zama mai godiya ko kuma mai bijirewa .”
Daga karshe muna rokon ALLAH ya ba mu ikon cinye duk wata harabawa da zata same mu.
Wa sallallahu ala MUHAMMADIN wa Alihiddayyibinaddahirin