SHIMFIƊA:
A shekara ta goma bayan hijira (10 AH), da umarnin Allah Maɗaukakin sarki, tafiyar ƙarahe ta Manzon Allah (s.a.w.a) wato Hajjin bankwana zuwa Makka ta faru, domin koyar da yadda ake aikin Hajji da kuma sanar da jagorancin (wilaya) na Imamai (a.s).
A wannan tafiya, fiye da mutum dubu dari da ashirin (120,000) sun tafi tare da Manzon (S.a.w.a) wannan adadi ne mai yawa na mutane wanda bai taɓa faruwa a wancan lokaci ba.
Bayan an kammala ayyukan Hajji, sai Manzon (s.a.w.a) ya bada umarni cewa dukkan mahajjata su fito daga Makka su nufi wani guri mai matuƙar muhimmanci da ake kira Ghadir Khum ; wanda ke kusa da mararrabar mahajjata da juna domin komawa garuruwansu bayan aikin hajji.
Kwana uku bayan an kammala Hajji, mutane suka nufi Ghadir Khum domin halartar wannan shiri na musamman da aka shirya.
Al amarin Ghadir ba wani lamari ne kawai na tarihi ba wanda ya faru a wancan lokaci kadai a a shi Al amarine wanda yake da alaƙa da ƙaddarar dukkanin ‘yan Adam a tsawon tarihi. Saboda haka, bayani da magana a kan Ghadir ya shafi kowa da kowa da kuma ko wane lokaci.
Abubuwan da su ka faru a Ghadir Khum ba daga bakin mutum guda aka samu cikakken bayani ba. Sai dai kowanne daga cikin waɗanda suka halarta ya bayar da bayanin ne daga wani sashe na abin da ya faru, sannan wasu daga cikin abubuwan kuma Imamai (a.s) ne su ka yi bayanin su.
Bayan sun isa Ghadir Khum, sai Manzon Allah (s.a.a.w) ya bada umarni a tsaya. Kowa ya sauka daga abin hawa, ya shirya zama na kwana uku. Da umarnin Annabi(s.a.a.w): Salman, Abu Zarr, Miqdad da Ammar suka tanadi wuri a ƙarƙashin tsofaffin itatuwa, kuma suka lulluɓe saman su da kyallaye domin samar da inuwa.
A ƙarƙashin wannan inuwa, aka haɗa mimbari da shinfiɗun dawakai da raƙuma da duwatsu daidai da tsayin Annabi (s.a.a.w) domin kowa ya gan shi lokacin da zai yi jawabi.
Bayan idar da sallar jam’i, ta Azzahar tare da Annabi (s.a.a.w), Ma’aiki (s.a.a.w) ya hau mimbari, sannan ya kira Ali (a.s) ya tsaya a ɓangatan damarsa ƙasa da shi kaɗan.
Annabi (s.a.a.w) ya waiga hagu da dama don tabbatar da cewa kowa na sauraren shi, sannan ya fara jawabi, wanda shine jawabin shi na ƙarshe ga al umma. kuma yana da matuƙar tarihi da mahimmancin gaske.
Za a iya raba wannan jawabi zuwa kashi goma sha ɗaya:
- Da farko Annabi (s.a.a.w) ya fara ne da godiya da yabo ga Allah (t), sannan ya bayyana ikonsa da rahamarsa ga bayi, sannan ya shaida cewa shi bawansa ne.
- Babban Saƙon: Ya bayyana cewa yana da wani muhimmin Al’amari da zai yi mu su bayani wanda umarni ne daga Allah (t). wato sanar da imamancin da Khalifan ci na Ali ibn Abi Talib (a.s), wanda idan bai isar da wannan sako ba ga al-umma kamar bai isar da saƙon Annabci shi ba baki gaba ɗaya ne. Ya ci gaba da cewa: yana jin tsoron azabar Allah idan bai yi hakan ba(Idan bai isar da wannansakon ba.
3.ya ci gaba da bayani a kan Imamai Goma Sha Biyu: Inda Ya sanar da jagorancin su daga zuriyar Ali (a.s)da Fatima (s.a) har zuwa ƙarshen duniya. ( da Wannan za mu fahimci cewa babu wani lokaci a cikin wannan duniyar da yake kasancewa babu Imami ko Na’ibinsa domin nuna wa Mutane hanyar gaskiya da shiriya)
Ya bayyana cewa jagorancinsu ya shafi dukkan mutane a kowanne lokaci da wuri, ya kuma cewa: sun gaji Annabi (s.a.a.w) a cikin halal da haram.
- Ya Bayyana Ali (a.s) a matsayin Jagora da imami a bayansa: Annabi (s.a.a.w) ya ɗaga hannayen Ali (a.s) har sai da sawunsa ya daidaita da gwiwarsa, sannan ya ce:
> “Duk wanda ni ne shugabansa (maula), to Ali ma shugabansa ne. ( مَنْ كُنْتُ مَوْلَاهُ فَهَذَا عَلِيٌّ مَوْلَاهُ اللَّهُمَّ وَالِ مَنْ وَالاهُ وَ عَادِ مَنْ عَادَاهُ وَ انْصُرْ مَنْ نَصَرَهُ وَ اخْذُلْ مَنْ خَذَلَهُ)
Ya ƙara da cewa: Ya Allah! Ka ƙaunaci duk wanda ya ƙaunace shi, ka ƙi duk wanda ya ƙi shi, ka taimaki wanda ya taimake shi, ka ƙasƙantar da wanda ya ƙasƙantar da shi.”
- Cikar Addini da Ni’ima: Bayan haka, Annabi (s.a.a.w) ya sanar da cewa wannan jagorancin da Khalifancin na Imam Ali (a.s) shi ne cika makon addini, kuma da Wannan kalifancin ne ni’imar Allah ta tabbata. Sannan ya naimi shaidar Allah, mala’iku, da mutane kan isar da wannan saƙo.
- Hukuncin Kin Karɓar Jagorancin Imamai (a.s) Annabi (s.a.a.w) ya ce:
> “Duk wanda ya ƙi karɓar imamancin Imamai (a.s), ayyukansa na alheri za su ɓaci kuma zai kasance a cikin wuta.”
- Furuci da Fushi daga Allah: A ƙarshe, Annabi ya karanta ayoyi daga Alƙur’ani game da azaba yayi bayani a kansu, yana cewa akwai wasu daga cikin sahabbansa da Allah ya umurce shi da ya yi hakuri da su, amma yin hakuri dasu bazai hana azabar lahira ba ta hau kansu ba.
Al’amari a kan ghadir; Al’amari ne mai ɗauke da inganci da hujjoji kan cewa Ali (a.s) ne khalifa bayan Annabi (s.a.a.w), kuma cewa imamancin Imamai (a.a) yana da muhimmanci ga cikar addini da shiriya ta gaskiya.
Sai dai hakan bai sanya munafukai su ƙi aikata abinda sukayi niyya ba bayan wafatin manzo (s.a.a.w), a kan sayyida zahra (s.a) da sauran Imamai (a.s) ba.
- Manzon Allah (s.a.a.w) ya yi bayani game da Imam Mahdi (a.j). Da farko Ya bayyana siffofinsa da matsayinsa na musamman, Ya kuma yi bushara ga duniya cewa: Imam Mahdi(a.j) zai bayyana a karshen zamani domin ya cika duniya da adalci da gaskiya, bayan ta cika da duhun zalunci.
- Bayan kammala hudubarsa, Manzon Allah ya nemi mutane da su yi mubaya’a gareshi da kuma Imam Ali (a.s).
Ya bayyana cewa: wannan mubaya’a ba kamar kowace mubaya’a ba ce wannan itace mubaya’ar da ya yi ga Allaha(t), kuma Imam Ali (a.s) ya yi mubaya’a gareshi. Saboda haka, duk wanda ya yi mubaya’a garesu, yana mubaya’a ga Allah(t) ne.
- A nan Manzon Allah ya yi bayani a kan wasu muhimman dokokin addini da aqeedah (tauhidi).
Duba ga yanayi da lokacin Annabcin Manzon (s.a.a.w) ba zai yuwu ya yi wa al-umma dukkanin bayani a kan abin ya shafi hukunce-hukunce ba. Saboda haka ne ubangiji ya umurce shi ya ya bar Imamai guda goma sha biyu (a.s) domin su ci gaba da bayyana su ga mutane har zuwa ranar kiyama.
Abu mafi girman a cikin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna; shi ne yaɗa saƙon Ghadir, da kuma kiran mutane zuwa biyayya ga Imamai da hana su saba musu.
A ƙarshe, Manzon Allah ya yi mubaya’a ta hanyar faɗa da bakinsa, saboda yawan jama’ar wurin ya hana su yi mubaya’a da hannu gaba ɗayansu. Inda Ya ce:
> “Allah ya umurce ni da karɓi mubaya’ar ku da baki kafin na karɓi mubaya’ar hannunku.”
Biyayya ga Imamai goma sha biyu (a.s),
Alƙawari da amana cewa ba za su canza ba,
Yaɗa saƙon Ghadir ga waɗanda ba su halarta ba da kuma ‘ya’yayen su har izuwa ƙarshen duniya.
Ya ƙara da cewa duk wanda ya aikata hakan, tamkar ya yi mubaya’a da zuciya, bakin, da hannunsa.