Follow us in
Follow us in

TAKAITACCEN TARIHIN WAKI’AR KARBALA

Ranar Ashura (10 ga watan muharram) shekara ta 61 bayan hijira ne sojojin Yazidu dan Mu'awiya suka kashe Imam Husain (A.S) a filin Karbala

DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI

Allah ya yi dadin tsira ga Annabi Muhammad (SAWA) da Iyalan Gidansa tsarkaka

 

Abin da ya faru a filin Karbala a takaice

Abin da ya faru a Karbala shi ne abu mafi muni da tayar da hankalin da ya taba faruwa a cikin tarihin Addinin Musulunci. Saboda haka ne ‘Yan Shi’a ke gudanar da zamammakin makoki a kowace shekara domin tunawa da wannan rana, da kuma nuna alhini da jimami.

Lamarin waki’ar Karbala ya fara ne bayan rasuwar Mu’awiya ɗan Abu Sufyan a ranar 15 ga watan Rajab, shekara ta 60 bayan Hijira, lokacin da ɗansa Yazid ya hau mulki.

Gwamnan Madina na lokacin ya yi ƙoƙarin tilastawa Imam Husain (A.S) a kan ya yi mubaya’a ga Yazid; saboda haka, Imam Husain ya bar Madina cikin dare domin guje wa wannan mubaya’a, inda ya nufi Makka. A wannan tafiya, iyalan Imam Husain (A.S), da wasu daga cikin dangin Banu Hashim, da kuma wasu daga cikin mabiya Shi’a sum kasance tare da Imam Husain (A.S).

Imam Husain (A.S) ya zauna a Makka na kusan watanni huɗu. A cikin wannan lokaci na zamansa a Makka ne, ya samu wasiƙu daban-daban daga mutanen garin Kufa dake kasar Iraqi suna gayyatar sa da ya taho wajansu. Imam ya aika Muslim ɗan Aqil zuwa Kufa, domin tabbatar da sahihancin abin da ke cikin wasiƙun, sannan ya aika da Sulaiman ɗan Razin zuwa Basra.

Duk da haɗarin da ke akwai na yiwuwar shahadantar da Imam Husain (A.S) a Makka ta hannun wakilan Yazid, da kuma gayyatar da mutanen Kufa suka yi masa, tare da tabbacin da dan aikensa ya bayar game da gaskiyar wannan gayyata, hakan ya sa Imam ya bar Makka a ranar 8 ga Zul-Hijja yana mai nufin zuwa Kufa.

Kafin Imam ya kai ga Kufa, labaran karya alkawari daga bangaren mutanen kufar da suka turo masa da wasiku sun same shi.

Bayan haduwarsa da rundunar Hur bin Yazid Al-Riyahi, Imam Husain ya koma zuwa hanyar Karbala. A inda a can ne ya fuskanci rundunar Umar bin Sa’ad, wadda Ubaidullah bin Ziyad ya aiko domin ya yaƙi Imam.

A ranar 10 ga watan Muharram, wanda aka fi sani da ranar Ashura, an gwabza yaƙi tsakanin rundunar Allah (Rundunar Imam Husain) da Rundunar Shaidan (Rundunar Yazid). Bayan da Imam Husain (A.S) da mabiyansa suka yi shahada, sai rundunar Umar bin Sa’ad da yazidu ya turo suka tattake gawarwakinsu da dawaki.

Haka kuma, da yamma a ranar Ashura, sojojin Yazid sun kai hari kan Mata da kananan yaran da ke zaune cikin tantuna cikin garjin rana a inda suka cinnawa tantunan wuta suka ci zarafin Mata da kananan yara.

Suka ƙone tantunan, sannan suka kama iyalan Imam a matsayin bayi. Imam Sajjad (A.S), wanda rashin lafiya ya hana shi shiga yaƙin, da Sayyada Zainab (A.S) suna daga cikin waɗanda aka kama.

Sojojin Umar bin Sa’ad bayan sun shadantar da shahidan karbala sun cire kawunan shahidan suka sossoke kawunan a masu, sannan suka tafi da su tare da sauran wadanda su ka kama a matsayin bayi zuwa Kufa, inda suka miƙa su ga Ubaidullah bin Ziyad, daga nan kuma aka tura su zuwa Sham domin gabatar da su ga Yazid.

Bayan sojojin Umar bin Sa’ad sun tafi, wasu mutane daga cikin mutanen kabilar Bani Asad suka je cikin dare suka binne gawarwakin shahidan Karbala.

YIN KUKA A KAN KISAN HUSAIN SUNNAR ANNABI NE

Wata rana Mala’ika Jibril (A.S) ya zo wajan Annabi (SAWA) zai gana da shi, sai Annabi ya ce wa matarsa Ummu Salama (R.A) kada tabar kowa ya shiga wajan da za su gana da Mala’ikan, jim kadan bayan sun fara ganawa sai ga Imam Husain (A.S) ya zo, sai ya bude kofa ya shiga, yana shiga sai ya fara wasa a inda su Annabi suke ganawa, sai Mala’ika Jibril ya tambayi Annabi cewa kana son sa ? sai Annabi ya ce Eh ina son sa, sai Jibril ya ce Al’ummarka za ta kashe shi, sai Mala’ika Jibril ya dumko kasa ya bawa Annabi ya ce masa wannan ce kasar wajan da za’a kashe shi (kasar karbala), a nan ne Annabi ya yi kuka, jim kadan bayan tafiyar Jibril sai ga Imam Ali (A.S)  ya shugo wajan Annabi, sai ya samu Annabi ya na kuka sai ya ce masa mai ya sa ka kuka ya Manzon Allah? Sai Annabi ya gaya wa Imam Ali duk abin da Jabra’il ya gaya masa a inda shima Imam Ali ya yi kuka.

Wannan na daga cikin dalilan da suka sanya yin kuka a kan kisan Imam Husain ya zama Sunna ne a duniyar musulunci, shi’a ko sunna domin kuwa duk bangarorin biyu sun ruwaito wannan ruwayar.

Daga baya Annabi ya bawa Ummu salama wannan kasar ya ce mata ta ajiye ta duk lokacin da ta ga wannan kasar ta zama jini to a ranar ne aka kashe Husain.

Assalamu alal Husain wa ala Aliyib- nil Husai wa ala Auladil-Husain wa ala As’habil- Husain wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :