TARIHIN IMAM RIDA (A.S) A TAƘAICE
SUNA, NASABA DA HAIHUWA
Imam Ali bin Musa al-Rida (a.s) shi ne Imami na takwas daga cikin jerin Imaman Ahlul Baiti (a.s). An haife shi a Madina a shekara ta 148 bayan hijira, a lokacin mulkin Abbasiyawa. Sunan sa na haƙiƙa shi ne Ali , Mahaifinsa mai girma shi ne Musa dan Ja’afar (a.s), Imami na bakwai, mahaifiyarsa kuma ita ce Najma wadda afi sani da Ummul Banin.
Mafi shaharar laƙabinsa shi ne “RIDA”, sunan shi na alkunya kuma shi ne “Abul Hasan”.
IMAMANCIN IMAMRIDA(A.S)
Bayan shahadar Imam Musa al-Kazim (a.s) Imami na bakwai wato mahaifinsa; Imam Rida (a.s) shine ya zama Imami na takwas.
Kamar yadda muka sani daga cikin hanyoyi da tabbatar mana da imamancin shi akwai:
- Hadisin Jabir:
wanda yake cewa: Manzon Allah (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi da iyalansa) ya ce:
“Imami na takwas kuma khalifan Musulmi shi ne Ali dan Musa (a.s)
Wannan hadisin yana daga cikin shaidu mafi karfi da ke tabbatar da Imamancin Imam Rida (a.s).
- Ruwayoyi daga Imam Musa al-Kazim (a.s):
Akwai ruwayoyi masu yawa da aka ruwaito daga Imam Musa al-Kazim (a.s), wanda suka bayyana cewa dan sa Ali (a.s) ne zai zama Imami bayan sa.
Tsawon Lokacin Imamancin Imam Rida (a.s)
Imam Rida (a.s) ya yi kusan shekara ashirin yana jagorantar al’umma musulmi a matsayin Imami.
Daga cikin wannan lokaci, ya zauna a Madina na tsawon shekaru goma sha bakwai (17), sannan kuma ya kwashe shekaru uku (3) a yankin Khurasan (wanda a yau yake a cikin Iran).
Hakiman da sukayi mulki zamanin Imam rida (a.s) su uku ne kamar haka:
- Harun al-Rashid
- Muhammad al-Amin
- Abdullah al-Ma’mun
Kamar yadda muka sani imam rida (a.s) ya baro madina zuwa kurasan (Mashhad) a lokacin mulkin Ma’amun Abbasi inda shi da kanshi ma’amun ɗin ya nema ga imam (a.s) cewa yazo sakamakon wasu manufofi da yake dasu akan Imam (a.s) din da ma sauran al’umma. ya kira Imam rida (a.s) zuwa birnin mulkinsa ne da nufin ya rinjayi mutane da yaudara, da kuma samun damar sa ido kai tsaye a kan Imam (a.s). Daga nan ya tilasta masa ya karɓi matsayin mataimakin sa (waliyyul-‘ahd). Wannan mataki yana da wasu manufofi da Ma’mun ke ƙoƙarin cimmawa:
- Samun yardar mabiya Shi’a.
- Kashe yawan juyin juya halin da Alawiyyawa ke tayarwa.
- Kafaffen matsayinsa na mulki ta hanyar danganta kansa da Imam Rida (a.s).
- Tsoratar da ‘yan Abbasawa masu tawaye da koyar da su darasi.
- Ƙoƙarin rage darajar da kima ta Imam (a.s) ta hanyar sako shi cikin harkokin siyasa da ƙazanta.
Sai dai Imam (a.s) ya fahimci dukannin manufofin ma’amun din, da dalilan bashi na’ibcin, sabo da haka ne ma yaƙi karɓar wannan naibcin kai tsaye sai da ya sanya sharuɗɗa Ko da yake Imam Rida (a.s) bai da wata hanya ko zaɓi face karɓar matsayin mataimakin halifa (waliyyul-‘ahd), amma ya gindaya wasu sharuɗɗa da suka hana Ma’amun cimma manufofinsa. Wadannan sharuɗɗan su ne:
- Kada ya shiga cikin umarni ko hani na gwamnati
- Kada ya bayar da fatawa.
- Kada ya yi shari’a ko hukunci.
- Kada ya shiga cikin naɗi ko sauke jami’ai.
- Kada ya canza dokoki ko al’adun addini.
A cewar masana tarihi, kafa irin waɗannan sharuɗɗa ya fi ƙin karɓar wannan mukami muni, domin yana nuna rashin halaccin gwamnatin Ma’amun da kuma cewa Imam Rida (a.s) bai da sha’awar shiga cikin irin wannan gwamnati.
A gefe guda kuwa, Imam (a.s) ya samu dama don ya gudanar da aiyyukansa na addini cikin natsuwa. Ya gudanar da muhawara da manyan malamai, har ya kunyatar da Ma’amun da kansa a muhawara. Haka kuma, ya jagoranci sallar idi mai ƙayatarwa wadda ta tilasta Ma’amun dakatar da ita tun kafin a fara. Sallar roƙon ruwa (salat al-istisqa’) da Imam (a.s) ya gudanar ta haifar da saukar ruwa, kuma hakan ya ƙara ƙarfafa soyayyarsa a zukatan mutane.
ILMIN IMAM RIDA (A.S)
Iliminsa
Imam Rida (as) yana da ilimin da ba za a iya kwatanta shi da kowa daga cikin mutanen zamaninsa ba.
A duk lokacin da aka gudanar da muhawara tsakanin shi da manyan malamai ko shugabannin addinai da mazahabobi daban-daban, fasaha da iliminsa suna bayyana karara.
Babu wani mutum da ya taba koyar da shi wani abu ko ya ci galaba a kansa a muhawara.
Daga cikin muhawarorin da Imam (a.s) ya gabatar sun hada da
Muhawarorinsa da Manyan Malamai da Jagororin Addinai,
A Lokacin da Khalifa Ma’mun (kalifan lokacin) ya gayyaci Imam Rida (a.s) zuwa Khurasan (mashhad a yanzu), ya yi hakan ne domin yana so ya rage tasirin Imam din a tsakanin al’umma, da kuma nuna cewa Imam Rida (a.s) ba ya da bambanci da sauran malaman addini.
Don haka Ma’mun ya tara manyan malaman Yahudawa, Nasara, Majusawa, Sabi’awa (masu bautar taurari), da ma falsafawa don su yi muhawara da Imam.
-
MAHAWARA DA MALAMIN NASARA:
Imam Rida (a.s) ya fara tambayar malamin game da Annabi Isa (Yesu). Ya tambaye shi:
“Shin ba ku yarda cewa Isa ba ya cin abinci kuma yana bacci?”
Malamin ya ce: “I, haka ne.”
Sai Imam ya ce: “To ta yaya za ku ce Allah ne, alhali Allah ba ya bukatar abinci ko barci?”
Malamin ya kasa amsa.
-
MAHAWARA DA YAHUDAWA:
Imam Rida (A.S) ya yi amfani da nassoshin Taurat wajen hujja da su, har suka yarda cewa tun daga zamanin Annabi Musa (A.S), akwai annabawa da suka zo, ciki har da Annabi Muhammad (S.A.W), wanda siffofinsa suna cikin littattafansu.
- MUHAWARA DA MAJUSAWA:
Imam ya tambaye su: “Shin kuna da hujja cewa akwai Allah biyu – daya mai kyau, daya mai sharri?”
Suka kasa gabatar da wata hujja mai karfi, kuma Imam ya bayyana cewa Allah daya ne, kuma dukkanin halitta daga gare shi suke.
Duk wanda ya zauna da Imam Rida (a.s) a cikin irin wadannan muhawarori, ya gane girman iliminsa, kuma da dama daga cikinsu sun karbi Musulunci ko suka yarda da Imamancin sa.
ƘYAWAWAN SUFFOFIN IMAM
1-Bautar Allah (t) da gujewa ruɗun duniya:
Imam Ali bn Musa Rida (a.s) ya kasance mutum ne mai yawan yin zuhudu (wato rashin sha’awar duniya) da kuma bautar Allah da jajircewa sosai kamar yadda muka sani dukkanin Imam mu suna bada kaso mafi yawa na rayuwar waurin yin ibada ga Allah (t); haka ma imam Rida (a.s) ya kasance.
Yana da kiyaye tsabtasosan gaske kamar yadda muka san cewa dukannin Imamai sun samo tsabtar su daga kakan su wato Annabi Muhammad (s.a.a.w), yana yin rayuwar sa cikin sauki da kaskantar da kai.
Harshen sa kullum yana cikin karatun Al-Qur’ani, yana yawan azumi, kuma yana yawan ibada da salloli da dare.
Sabo da haka daya daga cikin suffofin mabiya su na gaskiya shine jajircewa da bada himma wajan yin ibada da kasance da kyawawan ɗabi’u.
2- ƙasƙantar da Kai
Imam Rida (a.s) ya kasance cike da tawali’u a tsakanin mutane.
Bai taba ɗaga murya ko daka tsawa akan wani ba, bai taba katse maganar wani ba a yayin da yake cikin yin magana.
3- Karamci
Kamar yadda kakanninsa suka kasance masu karamci da girmama al’umma baki ɗaya, Imam Rida (a.s) shima ya yi fice wajen karamci da kyautatawa al’umma, har ma abokan gaba sun yarda da hakan.
A wani lokaci a rana ta Arafah, ya ba da duk dukiyarsa sadaka.
Sahabbansa suka tambaye shi da mamaki: “Shin wannan ba yafi yawa ba?”
Sai ya ce:
“Ba wai kawai ya dace ba ne, har ma wata dama ce mai girma domin samun lada da falala daga Allah.”
4– Fasaha da Hikima a Magana
Lokacin da Imam Rida (a.s) ya yi magana kan wani abu, kowa yakan natsu yana saurare.
Kalaman sa su kan taba zukata, kuma kamar iyayensa na Ahlul Baiti (a.s), ya kasance cike da fasaha, hikima da iya bayyana magana cikin kyau da nutsuwa.
SHAHADAR IMAM (A.S)
Ma’mun, bayan da ya ga kansa cikin wahala sakamakon sharuɗɗan da Imam Rida (a.s) ya gindaya, masa kuma bai kai ga manufofinsa ba, sai ya yanke shawarar kashe Imam (a.s). A shekara ta 203 Hijira, ya shahadan tar da Imam (a.s) a wannan lokacin Imam yana da shekaru 55 da haihuwa.
Ƙabarin sa mai daraja yana cikin garin Mashhad a Iran, wanda a yanzu haka ya zama cibiyar ziyara da ibada ga mabiya Ahlul Baiti (a.s).
Rayuwar Imam Rida (a.s) ta kasance cike da gwagwarmaya da hikima wajen kare addini da bayyanar da gaskiya. Duk da cewa Ma’amun ya yi ƙoƙarin amfani da Imam (a.s) don cimma manufofinsa na siyasa, sai dai Imam Rida (a.s) ya nuna cewa ba ya goyon bayan gwamnati mara adalci, kuma ya tsaya tsayin daka wajen kare martabar Imamanci da akidar Ahlul Baiti (a.s).
Shahadar Imam ba wai kawai ta jaddada zaluncin gwamnatin Abbasawa ba ce, har ma ta ƙara haskaka matsayin Imam Rida (a.s) a zukatan musulmi. Ƙabarin shi a Mashhad ya zama wani babbar cibiyar ruhaniya da tarihi, inda miliyoyin masu ziyara ke zuwa kowane lokaci domin girmama sa da kai masa ziyara.