- Haihuwarta da Nasaba
An haifi Sayyida Fatima Ma’asuma a ranar 1 ga watan Zul-Ki’da shekara ta 173 Hijiriyya (ko kuma 183 H) a Madina. Ita ce ‘yar Imam Musa al-Kazim (A.S), Wato Imami na 7 a cikin Imaman Ahalulbaiti 12, kuma ‘yar’uwar Imam Ali al-Ridha (A.S), Imami na 8. Mahaifiyarta ita ce Sayyida Najma (Tuktam), wadda ta samu tarbiyya a gidan Imam Jafar al-Sadik (A.S).
- Sunaye da Lakabi
Ana kiran ta da sunaye da yawa, ciki har da:
- Ma’asuma (wanda ke nufin “marar laifi”) – wannan lakabi Imam Ali al-Ridha (A.S) ne ya ba ta.
- Karimatu Ahlulbait (Kyautar Ahlul Bayt)
- Sauran sunayenta sun hada da Dahirah, Hamidah, da Barra.
- Rayuwarta da Ilimi
Ta girma a cikin gidan imamanci, kuma ta kasance mai himma wajen ibada da ilimi. An ruwaito cewa tun tana karama, ta kasance tana amsa tambayoyin masu neman ilimi lokacin da babu mahaifinta Imam Musa al-Kazim (A.S) ya tabbatar da cewa amsoshinta sun dace da hukuncin Allah.
- Tafiyarta zuwa Qom da Wafati
Bayan an kira Imam al-Ridha (A.S) zuwa Khurasan da umarnin halifa Al-Ma’mun, Sayyida Ma’asuma ta tashi don ziyartarsa. A kan hanya, ta kamu da rashin lafiya a garin Sawa, kuma ta nemi a kai ta Qom. Indata yi wafati a can bayan ‘yan kwanaki (a shekara ta 201 H) kuma an binne ta a Qom.
- Matsayinta a Wajen Masoya Ahalulbaiti
Tana da matsayin mace mai tsarki, wadda ake tawassuli da ita, kuma ana kwatanta ta da Sayyida Fatima Zahra (A.S). Ziyarar kabrinta a Qom tana da lada, kuma an ruwaito hadisi daga Imam al-Ridha (A.S) cewa: “Duk wanda ya ziyarci Ma’asuma a Qom, kamar ya ziyarci ni ne” Kabarinta ya zama cibiyar al’adu da ilimi na Addini.
- Gidan Tarihi da Cibiyar Ziyara
An gina Haraminta a Qom a cikin shekaru da yawa, kuma yana daya daga cikin muhimman wuraren ziyara na Shi’a a duniya.