Follow us in
Follow us in

Mutuwa Da Kiyama A Mahangar Al-Kur’ani

Mutuwa kiyama Adalci Allah Annabi

Da suna Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka.

Allah mai girma ya fada a cikin qur’ani cewa” يَا أَيُّهَا الْإِنْسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًا

Ma’ana shi ne “ ya kai dan Adam babu shakka cewa da dagewa da kuma kokari mai tsanani kana gabatuwa ne zuwa ga Allah saboda haka zaka gamu da shi.

‘Ya ku masoya, kalmar “مُلَاقِيهِ ” da ke cikin wannan ayar mai girma ta Suratul Inshiqaq, aya ta shida, na nufin haduwa. Menene haduwa? A cikin Al-Qur’ani Mai Girma, idan ana magana akan mutuwa, yawanci ana amfani da kalmar Larabci “Mawt” الموت . Amma sau da yawa Al-Qur’ani yana cewa “Liqaa’naa” لِقَاءَنَا , wato haduwa da Mu. Menene hakan ya ke nufi? Yana nufin cewa mutuwa haduwa ce da Allah. Wanda ya bar duniya yana tafiya wajan halarar Allah ne.

To, watakila mutuwa na iya zama wani abu mai tada hankali a gare mu. Tsoro ba abu mai kyau ba ne. Wataƙila a cikin taro ko zaman hira, muna cewa kar mu yi magana kan mutuwa. Shin magana kan mutuwa abu ne mai kyau ko mara kyau? Abu na farko da Al-Qur’ani ke koyarwa game da mutuwa shi ne cewa idan Allah yana so ya yi magana game da mutuwa, yana cewa “Liqaa’naa” لقاءنا  – haduwa da mu.

Wannan yana nufin cewa za ka je ka gamu da Allah. Za ka je zuwa wani babban liyafa, kuma babu tsoro ko damuwa a ciki. Misali idan aka ce mutum  yana da wata gayyata zuwa wata babban liyafa, za ka ga yana bukatar yayi wani shiri na musamman,zai tsaya ya ga wane irin tufafi zai  saka, a wane lokacin ya kamata ya tafi saboda kada ya Makara, da wane irin abin hawa ya kamata yayi amfani da shi. To kwatankwacin  hakan  ya kamata mu yi domi zuwa liyafar Allah.

Saboda haka, addini yana koyar da mu cewa mu kasance cikin shirin cewa za mu mutu, ba wai mu tsaya muna jin tsoron mutuwa ba.

Wani mutum ya tambayi Imam Ja’afar Sadiq (A.S): cewa”Me ya sa nake jin tsoron mutuwa?” Sai Imam Sadiq ya ce: “Saboda ka gina duniyar ka amma kuma ka lalata lahirarka. Duk wanda zai bar wuri mai kyau zuwa wuri mara kyau, tabbas zai ji tsoro.”

A Larabci, kalmar “Al’isti’dad lil-mawt” الاستعداد للموت na nufin shiri don mutuwa, ba wai ƙwarewa ko baiwa ba. Abu na farko domin shiri ga mutuwa shi ne a riƙa tunawa da ita akai-akai. Akwai ruwayoyi da yawa da ke koyar da cewa tunawa da mutuwa yana hana mutum aikata zunubi kuma yana rage son duniya.

Wani lokacin sai mu rika tunanin cewa mala’ikan mutuwa wato Az’rail wani mala’ika ne mai aban tsoro, alhali sam sam  ba haka abin yake ba, Mala’ikan mutuwa daya ne daga cikin mala’iku mukarrabai, Shi wani Mala’ika ne da Allah ya wakilta domin daukar rayuka, wanda da zarar lokacin daukar ran ya yi yake zuwa ya dauki ransu kamar yadda yazo a cikin qur’ani mai girma cewa    إِذَا جَاءَ أَجَلُهُمْ لاَیستَأْخِرُونَ سَاعَةً وَلاَ یسْتَقْدِمُونَ

Ma’ana cewa; idan lokacin ajalin bayi ya zo, za su makara ba  ko kuma su yi sakko dai dai da sakan guda.

An ruwaito cewa, wani annabi ya tambayi Mala’ika Azra’il cewa: “Za ka iya sanar da ni kafin ka zo karɓar raina?” Sai Azra’il yace eh zan sanar da kai kafin na zo karbar ran ka. Bayan wani lokaci mai tsawo, Azra’il ya zo domin daukar ran wannan Annabin, sai Annabin ya ce: “Amma ka ce za ka sanar da ni kafin ka zo kuma gashi baka sanar da ni ba!” Sai Azra’il ya ce: “Na sanar da kai har sau uku kuwa: Na farko shi ne lokacin da gashinka ya fara yin fari, na biyu kuma lokacin da iyayenka suka mutu, sannan na uku lokacin da ka ga mutane suna jana’izar gawa amman ba kayi tunanin cewa wata rana kai ne a cikin makarar ba.”

gudun duniya;

Addini yana koyar da cewa kada mu ji tsoron mutuwa, amma mu kasance cikin shiri. Imam Sadiq (A.S) ya ce: “Ku riƙa yawan tunawa da mutuwa, domin tunawa da mutuwa na hana mutum aikata zunubi kuma yana rage son duniya.”

An ruwaito cewa, wani Annabi ya haɗu da wani mutum a cikin wani kogo wanda shi mutumin ya rataye wani kokon kai da aka yi rubutu a jikin sa. Abin da aka rubuta a jiki shi ne: “Ni ne Sarki wane dan wane. Na gina garuruwa da yawa, na mallaki dubun dubatar bayi, amma yau, ga inda na ƙare, na zama dandalin tsutsotsi saboda haka duk wanda yaganni a haka kada duniya ta rude shi”

Saboda  haka, kada mu ji tsoron mutuwa, Sai dai mu kasance cikin shirin tafiya  wannan babban liyafar liyafa a fadar Allah. Daga  ƙarshe, an ruwaito cewa abin so ne mutum ya tanadi likkafaninsa ya ajiye a tare da shi domin ya rinka tunawa da mutuwa, kuma hakan ba wai yana nufin cewa za’a mutu da wuri bane, sai domin ya zama ana tunawa cewa wata rana za mu koma ga Allah. Allah ya sa mu mutu a cikin mafi kyawun yanayi kuma ya karɓe mu cikin rahamarsa Amin.’.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :