Follow us in
Follow us in

Neman Halak A Halittun Allah

Allah Maɗaukaki Ya tsara al’amuran duniya ta yadda duk wani sakamako da ka ga wani mutum ya samu to hakan na da alaka ne da kokarinsa, da kuma dagewarsa.

Komai yana tafiya ne a wannan duniyar bisa ga ƙoƙarin mutum, kamar yadda Allah ya fada a cikin Suratul Najm, Aya ta 39:

أَنْ لَيْسَ لِلْإِنْسَانِ إِلَّا مَا سَعَى  Ma’ana,( lalle ne, ba wani abu da mutum zai mallaka face abin da ya yi ƙoƙari akansa.)

Wato duk abin da kaga mutum ya mallaka a rayuwarsa to kokari da aiki yayi domin samunsa. Rayuwar mutum a wannan duniya tana tafiya ne daidai da ƙoƙarinsa, wahalarsa, da yunƙurinsa. Idan mutum ya yi himma, zai sami alheri da albarka.

Idan kuma mutum bai yi ƙoƙari ba, to ba zai sami komai ba. Wannan shi ne tsarin da Allah Ya shimfida a wannan duniyar.

Mutum ba zai iya samun komai ba face abin da ya yi ƙoƙari a kansa, ko dai alheri ne ko sharri, riba ne ko asara. Komai yana hade da aikinsa ne.

Ba kamar yadda wasu ke tunani ba, cewa wani lokacin wani zai zo ya yi aikin, sai kuma wani daban wanda bai aikata komai ba kuma bai yi wata wahala ba ka ga ya zo ya amfani wannan aikin. To a hakika abun ba haka yake ba, domin kuwa ko da kaga wani mutum ya sami wani alheri tako wace irin hanya kuwa to wannan alherin nada alaka ne da wani ƙoƙari daya taba yi, ko kuma wata gudunmawa da ya taba bayar wa a wani wuri wanda hakan yasa ya cancanci wannan alherin.

A dai dai wannan gabar za’a iya yin tambaya kan cewa to kuma ya batun yake akan ceto ranar alkiyama? Shin shima wannan kai’dar da aka ambata zata hau kansa ko kuwa?

Mun san cewa Allah ya ce: وَأَنْ لَيْسَ لِلْإِنْسَانِ إِلَّا مَا سَعَى

(Kuma ba wani abu da mutum zai samu face abin da ya yi ƙoƙari akansa.)

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :