Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka.
Sanannen abu ne cewa lokaci da ranaku a kankan su basu da wata khususiyya ko wani abun ki, amma su ne lokutan da abubuwa masu mahimmanci ke faruwa a cikin su, wanda su waɗannan abubuwan ke sanya lokaci ko ranaku su zama masu tsarki ko marasa kyau. Saboda haka ne ma, ranar haihuwar Annabi ko A’immah (AS) saboda kasancewar ta a wannan lokacin, rana ce mai muhimmanci kuma mai albarka, kamar yadda wasu abubuwa marasa kyau kan iya faruwa wanda za su sanya ranaku su zama marasa albarka ko ranakun bakinciki.
Idan mu ka yi duba zuwa ga ranakun haihuwar wasu ba’adin Annabawan a cikin Alqur’ani za mu ga yadda Allah ya ambaci ranakun haihuwar ta su a matsayin amintattun ranaku ma su albarka, dangane da ranar haihuwar Annabi Yahya (A.S) Allah ya ce:
سورة مريم آية 15«وَسَلاَمٌ عَلَيْهِ يَوْمَ وُلِدَ وَيَوْمَ يَمُوتُ وَيَوْمَ يُبْعَثُ حَيًّا»
“Aminci da albarka su tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, da ranar da zai mutu, da ranar da za’a tashe shi da rai.”
Annabi Isa (a.s) game da ranar haihuwar sa ya ce:
سورة مريم 15«وَالسَّلاَمُ عَلَيَّ يَوْمَ وُلِدْتُ وَيَوْمَ أَمُوتُ وَيَوْمَ أُبْعَثُ حَيًّا»
“Aminci su tabbata a kaina ranar da aka haife ni, da ranar da zan mutu, da ranar da za’a tashe ni da rai.
A cikin Suratul Ma’ida, muna karantawa:
«قَالَ عِيسَى ابْنُ مَرْيَمَ اللَّهُمَّ رَبَّنَا أَنْزِلْ عَلَيْنَا مَائِدَةً مِنَ السَّمَاءِ تَكُونُ لَنَا عِيدًا لِأَوَّلِنَا وَآخِرِنَا وَآيَةً مِنْكَ (سورة المائدة 114)
“Isa ɗan Maryamu ya ce: Ya Allah, Ubangijinmu! Ka saukar mana da abinci daga sama, ya zamar mana biki ga farkonmu da ƙarshenmu, kuma ka saukar mana da Ayah daga gare ka.”
Ranar saukar da abincin sama, rana ce ta biki kuma mai albarka.
Nuna farin ciki da murna da ranar haihuwar Manzon Allah (SAW) abu ne da Musulmai da yawa suke yi, kuma ko da ba a samu hujja ta addini ba, to ba a ɗauka cewa yin hakan (bid’a) ba ne. Domin asalin ƙaunar Manzon Allah (SAW), da Ahlul-Bayt (AS) abu ne daya tabbata a cikin addinin Musulunci wanda Allah ya umurce mu da shi.
قُلْ إِنْ كُنْتُمْ تُحِبُّونَ اللَّهَ فَاتَّبِعُونِي يُحْبِبْكُمُ اللَّهُ وَيَغْفِرْ لَكُمْ ذُنُوبَكُمْ (سورة آل عمران آية 31)
Ka gaya musu ya Muhammad idan kun kasance kuna son Allah to ku bini Allah zai so ku kuma zai gafarta muku zunuban ku.
لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ لِمَنْ كَانَ يَرْجُو اللَّهَ وَالْيَوْمَ الْآخِرَ وَذَكَرَ اللَّهَ كَثِيرًا (سورة أحزاب آية 21)
Lallai Annabi (SAWA) kyakkkyawan abin koyi ne ……
Saboda haka bukukuwan Mauludi da Al’ummar Musulmi su ke yi ba komai ba ne face wata hanya ta nuna soyayya da ƙauna ga Annabi da Iyalan gidan sa. Babu wanda zai ce gudanar da tarurrukan murna da farin ciki da ake karanto abubuwan addini wani abu ne na bid’a face wanda ya jahilci mene ne bid’a.
Allah ta’ala ya ce:
(سورة الشورى آية 23) قُل لا أَسئَلُکمْ عَلَیْهِ أَجْراً إِلا الْمَوَدَّةَ فی الْقُرْبی
“Ka ce: ‘Ba na tambayar ku wata lada game da aikin da nayi sai ƙaunar Iyalan gida na.’”
Kuma Manzon Allah (SAW) ya ce:
“لايمن احدکم لایؤحتی اکون احب الیه من ماله و اهله و الناس اجمعین
Ma’ana:Imanin dayan ku bay a cika har sai na zama mafi soyuwa a wajan sa fiye da dukiyar sa, da iyalan sa da sauran mutane baki daya.
Yin godiya da nuna murna domin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin waɗannan mafifitan bayi (Annabi da Ah’lul-baiti) bai sabawa addini ba, domin kuwa aikata hakan ma shi ne addini, saboda hakan nuna kauna ce gare su.
Ta wani bangaren, akwai wasu abubuwa a cikin addini wadanda su ke a dunkule, amma ana iya aikata su ta hanyoyi daban-daban. Daya daga cikin waɗannan abubuwan shi ne nuna soyayya da girmamawa ga Manzon Allah (SAW) da Ahlul-Bayt (AS). ƙaunarsu da bayyana soyayya gare su wani abu ne da akan iya bayyanawa a kowane lokaci ta hanyoyi daban-daban wanda Murna da zagayowar ranar haihuwar Manzon Allah (SAW) na daya daga cikin wannan hanyoyin, saboda haka ba wani abu bane da za’a kira da bidi’a ko sabawa koyarwar Addinin musulumci.
















