Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai
Tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka
Magana a kan Wilayatul-Faqih tana daga cikin ginshiƙan maganganu a cikin fikihun Shi’anci, Jagoran Juyin Musulunci, marigayi Imam Khomaini (Allah ya jikansa) shi ne wanda a wannan zamanin ya farfado da ita wannan nazariyya mai mahimmancin gaske.
A fahimtar Shi’a, Wilayat ul-Faqih a zamanin gaibar Imam Mahdi kamar ci gaba ne da jagorancin wilayar Ma’asumai, kamar yadda Imamancin Ma’asumai ya kasance ci gaba ne da jagorancin annabtar Manzon Allah (S.A.W.W).
Falsafar wannan wilayar shi ne samar da tsarin mulki ga al’ummar Musulmi, wanda Idan akwai samuwar ma’asumi a tsakanin su, to shi ne jagora, idan kuma babu, to fakihi mai cikakkun sharuɗɗa ne zai ɗauki nauyin jagorancin Al’umma.
A mahangar Musulunci, babban aikin hukuma shi ne yaɗa dokokin Allah a cikin al’umma. Wanda idan ana son kaiwa ga wannan hadafi, wajibi ne ya kasance akwai wani mutum mai cikakken sani a kan addini (malami) wanda zai zama mai hukunci a cikin al’amuran tafiyar da wannan hukuma.
Dalilai akan tabbatar da nazariyyar wilayatul-faqih
Za’a iya kawo dalilai guda biyu wanda su ke tabbatar da wannan nazariya;
Dalili na Hankali
Dalili na Nakali (kur’ani da Hadisi)
- Dalilin hankali
Allah ya tsara rayuwar mutane akan bukatuwa zuwa ga zamantakewa da juna, wanda hakan ke lazimta buƙatar rayuwa tare da sauran mutane da kuma kafa al’umma. Wanda Babu shakka akan cewa domin aiwatar da irin wannan rayuwar, al’umma tana buƙatar doka da kuma shugaba (mai aiwatar da doka) don gudanar da ita.
Babu shakka akan cewa mafi kyawun doka domin tafiyar da rayuwar al’umma ita ce dokar da Allah ya saukar a cikin Alkur’ani mai girma , domin kuwa Allah Shi ne mafi sani game da bukatu da matsalolin halittunsa.
A gefe guda kuma, aiwatar da wannan doka da shugabanci a cikin al’ummar Musulmi wajibi ne ya kasance a hannun wanda ya fi kowa sanin wannan doka, kuma ya fi kowa ƙwarewa wajen aiwatar da ita.
Wanda Manzon Allah (S.A.W.W) shi ne mafi sani akan haka, sannan Imamai Ma’asumai (A.S) su biyo bayan sa, sannan a lokacin gaibar Imam Mahdi (A.S) Fakihai masu cikakkun sharudda.
Wadannan su ne jagororin al’umamah na gaskiya a jere.
Domin a iya aiwatar da waɗannan dokoki yadda ya kamata, wajibi ne a lokacin gaiba (idan an samu cikakkun sharudda) a kafa Gwamnatin Musulunci.
Hankali yana hukunta cewa wanda ke da matsayi mafi girma a cikin irin wannan gwamnati dole ne ya kasance mutum wanda yake da cikakken ilimi game da dokokin Musulunci, kuma zai iya shugabantar mutane.
Idan Ma’asumi yana cikin mutane, hankali zai tabbatar da cewa shi ne mafi cancanta ga wannan matsayi. Amma a lokacin gaibar Ma’asumi, fakihi mai adalci kuma mai iya tafiyar da al’umma shi ne ya cancanci wannan matsayin.
A takaice, matsayin wilaya tabbatacce ne, kuma a ko da yaushe dole ne ya kasance akwai mutum ɗaya da yake da sharuddan da suka wajaba domin ya ɗauki nauyin jagoranci da shiryar da al’umma.
Abin da ke canzawa kawai shi ne Malaman da suke rike irin wannan matsayi, amma matsayin kansa ba ya canzawa ko gushewa.
- B) Dalilan Naƙali ( ruwaya):
Akwai ruwayoyi da dama wanda ke Magana a kan tabbatar da Wilayat ul-Faqih, amma saboda taƙaice rubutun, za mu ambaci hadisai uku kadai.
Shaikh Saduq ya ruwaito cewa, I mam Mahdi (A.S) ya ce:
وَ أَمَّا الْحَوَادِثُ الْوَاقِعَةُ فَارْجِعُوا فِیهَا إِلَی رُوَاةِ حَدِیثِنَا فَإِنَّهُمْ حُجَّتِی عَلَیکمْ وَأَنَا
حُجَّةُ اللَّهِ عَلَیهِم
Ma’ana: “Amma dangane da sababbin abubuwan da zasu rika faruwa, ku koma ga masu ruwaito hadisanmu a cikin su. Su ne hujjata a kanku, ni kuma hujjar Allah a kansu.”
Imam Mahdi (A.S) a cikin waɗannan jimlolin biyu « فَإِنَّهُمْ حُجَّتِی عَلَیکمْ » da « وَأَنَا حُجَّةُ اللَّهِ عَلَیهِم
ya bayyana cewa hukuncin masu ruwaito hadisai – wato fakihai – daidai yake da hukuncin Imam. Wato, fakihai sune wakilan Imam Mahdi (A.S) a tsakanin mutane.
2 – Hadisi daga Imam Ja’afar al-Ṣadiq (A.S), wanda ake kira Maqbulat ‘Umar ibn Ḥanẓala:
«مَنْ کانَ مِنْکمْ مِمَّنْ قَدْ رَوَی حَدِیثَنَا وَ نَظَرَ فِی حَلَالِنَا وَ حَرَامِنَا وَ عَرَفَ أَحْکامَنَا فَلْیرْضَوْا بِهِ حَکماً فَإِنِّی قَدْ جَعَلْتُهُ عَلَیکمْ حَاکماً فَإِذَا حَکمَ بِحُکمِنَا فَلَمْ یقْبَلْهُ مِنْهُ فَإِنَّمَا اسْتَخَفَّ بِحُکمِ اللَّهِ وَ عَلَینَا رَدَّ وَ الرَّادُّ عَلَینَا الرَّادُّ عَلَی اللَّهِ وَ هُوَ عَلَی حَدِّ الشِّرْک بِاللَّه
Ma’ana: “Duk wanda daga cikinku ya kasance mai ruwaito hadisanmu, kuma ya san halal da haram ɗinmu, kuma ya fahimci hukumce-hukumcenmu, ku amince da shi a matsayin maihukunci. Lallai ni na sanya shi mai hukunci a kanku. Saboda haka, idan ya yi hukunci da hukuncinmu amma aka ƙi karɓa daga gare shi, to hakan raina hukuncin Allah ne, kuma raddi ne a kanmu. Shi kuma raddi a kanmu, raddi ne a kan Allah, kuma hakan dai-dai yake da shirki da Allah.
Saboda haka, idan ya zama akwai Ma’asumi amma kuma ba za’a iya kaiwa gare shi, to nauyin al’umma ya doru a kan fakihai masu cikakken sharadi. Kamar yadda a lokacin gaiba ma, dole al’umma su mayar da al’amuran su zuwa ga waɗannan fakihai.
















