Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka.
Imam Ali (A.S) ya bayyanawa dan sa Imam Hasan (A.S) wasu abubuwa guda hudu, kuma ya ce masa ya kiyaye su saboda bazai taba cutuwa ba matsawar dai ya yi aiki da su.
Irin wannan maganganu da Ma’asumai ke yi a junansu, a hakika su na yi ne domin mutane su fadaka.
A cikin hikima ta 38 daga littafin Nahjul-balaga Imam Ali (A.S) ya bayyana wadannan abubuwa guda hudu, amma idan mu na son ya zama mun ambaci duka wadannan abubuwan guda hudu to akwai bukatar mu karkasa rubutun gudun kada ya yi yawa.
Abu na farko da rubutun zai maida hankali a kai shi ne kashi na farko daga cikin wadanna abubuwa guda hudu da Imam ya ambata.
وَ قَالَ (علیه السلام) لِابْنِهِ الْحَسَنِ (علیه السلام):
يَا بُنَيَّ احْفَظْ عَنِّي أَرْبَعاً وَ أَرْبَعاً، لَا يَضُرُّكَ مَا عَمِلْتَ مَعَهُنَّ: إِنَّ أَغْنَى الْغِنَى الْعَقْلُ، وَ أَكْبَرَ الْفَقْرِ الْحُمْقُ، وَ أَوْحَشَ الْوَحْشَةِ الْعُجْبُ، وَ أَكْرَمَ الْحَسَبِ حُسْنُ الْخُلُقِ…
Imam Ali (a.s) ya gaya wa dansa Imam Hasan (a.s) cewa: ya Da na ka kiyaye wasu abubuwa guda hudu da za ka ji daga gare ni da kuma wasu guda hudun, ba zai taba cutar da kai ba matsawar dai ka yi aiki da su:
إِنَّ أَغْنَى الْغِنَى الْعَقْل
lallai mafi girman wadatar da tafi ko wace wadata ita ce hankali.
Hankali na daga cikin manyan abubuwan da Allah ya banbanta Dan- adam da sauran halittu da shi, domin a cikin halittun Allah babu wanda yake da irin wannan baiwa ta hankali, domin kuwa duk wanda yake da hankali cikakke, to yana da mafificin arziki ta bangare biyu, Maddi da Ma’anawi (duniya da lahira, zahiri da badini).
A BANGAREN MA’ANAWI (badini), hankali na iya jagorantar mutum zuwa ga Allah, da sahihin imani, da kyawawan ɗabi’u da ayyukan alheri;( قِوَامُ الْمَرْءِ عَقْلُهُ وَلاَ دِینَ لِمَنْ لاَ عَقْلَ لَهُ) hankali ne asasin ayyukan mutum, kuma babu addini ga wanda duk baya da hankali.
domin kuwa da hankalin ne ake gane illolin mugayen ɗabi’u, wanda duk mai hankali idan ya gane wannan illolin zai guji aikata duk wata muguwar dabi’a.
Shi yasa Manzon Allah (S.A.W.W) ya ce; مَا قَسَمَ اللَّهُ لِلْعِبَادِ شَیْئاً أَفْضَلَ مِنَ الْعَقْلِ فَنَوْمُ الْعَاقِلِ أَفْضَلُ مِنْ سَهَرِ الْجَاهِل
Allah Ta’ala bai rabawa bayi wani abu wanda ya fi hankali ba, baccin mai hankali yafi raya daren jahili.
Sai dai kuma kada mai karatu ya manta da cewa, akwai abubuwan da a addinin musulunci hankali baya iya kaiwa gare su dole sai da jagoranci da shiriyar Annabawa, saboda idan ba haka ba to aiko Annabawa zai zama abin tambaya, tambayar kuwa ita ce; idan har hankalin Dan-Adam zai ganar da komai to mene ne amfanin turo da Annabawa?
Shi yasa a hudubar farko ta Nahajul- balaga Imam Ali (A.S) ya ce;
فَبَعَثَ فِيهِمْ رُسُلَهُ وَ وَاتَرَ إِلَيْهِمْ أَنْبِيَاءَهُ لِيَسْتَأْدُوهُمْ مِيثَاقَ فِطْرَتِهِ وَ يُذَكِّرُوهُمْ مَنْسِيَّ نِعْمَتِهِ وَ يَحْتَجُّوا عَلَيْهِمْ بِالتَّبْلِيغِ وَ يُثِيرُوا لَهُمْ دَفَائِنَ الْعُقُولِ.
……Allah ya turo Annabawa ne domin su buncuko muku da abin da ya buya ga hankali.
A BANGAREN MADDI (zahiri ko duniya) kuma, hankali ne yake yin jagora zuwa ga samar da kyakkyawan tsari, haɗin kai a tsakanin mutane, gane aboki da maƙiyi,……
Yin shawara wani abu ne wanda Addini da Al’ada suka yadda da shi harma su ka yabi mai yin hakan, ya zo a cikin Al’qur’ani mai girma cewa Allah Ta’ala ya umarci Manzon sa da ya yi shawara, ,وشاور هم في الأمر Hausawa na cewa: mai shawara aikin sa bayabaci.
Shi kan shi yin shawara da ma’abota hankali, hankali ne ke umartar mutum da ya amfana daga ra’ayoyin wasu kuma ya yi aiki da shawarar su, ganin cewa yin hakan tamkar aron hankalin su ya yi kuma ya yi aiki da shi, kamar yadda ake daukar mai aiki musammam na karfi ya yi aiki a biya sa, wanda hakan dai-dai yake da cewa tamkar aron jikin sa aka yi.
















