Follow us in
Follow us in

Illolin rashin aiki da hankali a mahangar Nahajul- balaga

Rashin aiki da hankali wata babbar illa ce da ke iya kaiwa ga mutum ya rasa duniya da lahirar sa, babban talauci shi ne karancin hankali da rashin sanin ya kamata (wawanci), Mutum mai wauta da karancin hankali (wawa) ya na iya lalata lahira da duniyar sa a lokaci guda. ta hanyar fifita dadin duniya mai gushewa akan farin cikin lahira na har abada.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka.

 

Na biyu daga cikin ci gaba da bayani akan abubuwa guda hudun da Imam Ali (a.s) ya gayawa Dan sa Imam Hasan (a.s) shi ne:

Babban talauci shi ne karancin hankali da rashin sani (wawanci); (أَکْبَرَ الْفَقْرِ الْحُمْقُ).

Domin mutum mai wauta da karancin sani (wawa) ya na lalata lahirarsa da duniya a lokaci guda.

Yana fifita riba ta ɗan lokaci akan farin ciki na har abada,

kuma yana zaɓar jin daɗi na dan lokaci akan farin ciki na har abada.

Wanda yin hakan na iya kai shi ga zuwa  gaban Allah a ranar tashin kiyama, al’hali babu ayyukan alheri a tare da shi, kuma dauke nauyin zunubi.

Wanda a duniya ma haka abin yake, rashin hikima na iya kaiwa ga ya rasa abokansa , kuma ya rika fifita riba ta gaggawa akan abin da zai amfane shi a nan gaba.

Rowa  da rashin hangen nesa, su kan sa mutanen da ke tare da mutum mai wauta su guje shi kuma su daina yarda da shi,

Mutum mai wauta yana rasa basirar gudanar da al’amuran rayuwa duniya.

Saboda haka, rashin hankali da waita suna haifar da talauci a rayuwar duniya.

Ɗaya daga cikin manyan matsalolin mai waita (wawa) shi ne cewa ba’a samun maganin ciwon sa da sauƙi.

domin yana kama da marar lafiyar da ba ya shan magani kuma ba ya kiyaye abinci.

Kamar yadda marigayi Shaykh al-Mufid ya kawo a cikin littafinsa al-Ikhtiṣaṣ,an ruwaito daga Imam Jaʿfar al-Ṣadiq (A.S) cewa:

«إنَّ عیسَى بْنَ مَرْیَمَ قالَ: دَاوَیْتُ الْمَرْضَى فَشَفَیْتُهُمْ بِإِذْنِ اللَّهِ وَأَبْرَأْتُ الاَْکْمَهَ وَالاَْبْرَصَ بِإِذْنِ اللَّهِ وَعَالَجْتُ الْمَوْتَى فَأَحْیَیْتُهُمْ بِإِذْنِ اللَّهِ وَعَالَجْتُ الاَْحْمَقَ فَلَمْ أَقْدِرْ عَلَى إِصْلاَحِه.

Annabi Isa ɗan Maryam (A.S)  ya ce: Na yi wa marasa lafiya magani kuma na  warkar da su da izinin Allah;

Kuma na warkar da makaho da mai cutar kuturta da izinin Allah;

na tayar da matattu da izinin Allah; amma da na yi ƙoƙarin warkar da mai wauta (wawa), ban iya warkar da shi ba.”

Wato, Annabi Isa (A.S) yana cewa:

Na iya warkar da cututtuka masu wahalar magani da izinin Allah,

amma cutar wauta ce da ba ta da magani,

saboda wawa ba ya karɓar nasiha, ba ya bin umarni, kuma ba ya fahimtar gaskiya.

Akwai ruwayoyi da dama daga Ahlul Bayt (A.S) wanda suke bayani game da wanda ake kira da mai wauta (wawa) a wani wajan na littafin Nahajul-balaga  Imam Ali (A.S) ya ce:

«مَنْ نَظَرَ فِی عُیُوبِ النَّاسِ فَأَنْکَرَهَا ثُمَّ رَضِیَهَا لِنَفْسِهِ فَذَلِکَ الاَْحْمَقُ بِعَیْنِهِ

 “Wanda yake ganin kura-kuran mutane, kuma ya ƙi su, amma sai ya yarda da irin waɗannan kura-kuran a kansa, wannan shi ne wawa da kansa.”

Wato, wanda ya ke ganin laifin wasu amma kuma ya aikata makamancin irin wannan laifin na su da kansa, shi ne cikakken wawa.

A wannan fassarar ne, za’a iya gane dalilin da yasa wawa ya ke rasa addininsa da duniyarsa.

Tarihi ya kawo labarai da dama game da wawaye waɗanda ke nuna yadda rashin hankali yake jawo musu rauni a imani da al’amuran zamantakewa.

Ga misali a kan haka:

A cikin Sharhin Nahajul-Balaghah na ‘Allamah Shushtari, an ruwaito cewa:

wata rana ɗaya daga cikin halifofi ya kasance yana tafiya zuwa masallaci a ranar Idi (karamar sallah ko babba), Mutane suna ta buga ganguna a gabansa, ga kuma tutoci suna ta filfilawa a sama.

Sai wani mutum marar sani (wawa) ya ɗaga kai sama ya ce: للّهُمَّ لا طَبْلَ إلاّ طَبْلُك

Sai wani a kusa da shi da ya ji, ya ce masa: “Kada ka faɗi haka; domin shi Allah ba shi da ganga. Sai wannan Mutumin (Wawan) ya yi ta kuka ya ce: “To, kuna nufin idan Allah zai zo, ba za ya zo da ganguna a gabansa ba, sannan kuma babu tutoci suna filfilawa a saman sa? to, idan kuwa haka abin yake, hakan yana nufin cewa Allah ƙasa yake da halifanmu.”

 

Haka nan, a cikin littafin ʿUyun al-Akhbar na Ibn Qutaybah ad-Dinawari, kamar yadda ‘Allamah Shushtari ya nakalto, wani mutum wawa ya ce:

“Na san sunan kurar da ta cinye Annabi Yusuf.” Sai Mutane suka ce masa:“ ai kuwa dai kura bata cinye Yusuf ba!”Sai ya amsa da cewa:

“To, wannan sunan kurar da bata cinye Yusuf din ba ne!”

A wannan misalan da suka gabata ma’anar Ahmaq (Wawa) shi ne mai raunin hankali, mai raunin tunani, wanda baya iya aikin da hankalin sa a cikin da yawa daga abubuwan da su ke iya taso masa.

Saboda haka irin wadannan mutane su ake kira da wawaye

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :