Follow us in
Follow us in

Ina Kabarin Sayyida Zahara?

Kabarin Sayyida Zahara

Hazrat Fāṭimah Zahra (s) – ‘ya mace guda tilo ta Manzo, kuma matar Amirul Muminin Ali (a) — wadda ta yi shahada sakamakon wasu matsaloli da suka faru bayan wafatin mahaifinta Manzon Allah (s.a.w.a.). A cikin wannan makala za mu yi ƙoƙarin gabatar da bincike game da shahadar Hazrat Fāṭimah a taƙaice kuma cikin gamsasshen bayani.

Ranar shahadarta

A kan ranar shahadar Hazrat Zahra (s) malamai da marubutan tarihin Shi’a da Ahlus Sunnah ba su da cikakken ra’ayi ɗaya. Abin da ya fi shahara a tsakanin marubutan tarihin Shi’a da masu rubutun sira shi ne cewa, a ranar 3 ga Jamaadi al-Akhir (جمادی الثانی), wato kwanaki 95 bayan wafatin mafificin mahaifi, wato Manzon Allah (s), ta yi shahada sakamakon dukan da aka yi mata daga ma’aikatan tsarin mulkin da aka kirkiro da karfi; bayan ta kwashe kwanaki 40 tana fama da rashin lafiya, daga bisani cikin zalunci aka shahadantar da ita. Saboda haka wannan rana ta zama ranar baƙin ciki da kewar mabiyan gidan Annabta da masoyan Ahlul Bayt (a).

Ina kabarin Hazrat Fāṭimah (s)?

Bayan ranar shahada, batun wurin binne Hazrat Zahra (s) ma bai samu daidaituwar ra’ayi a tsakanin marubutan tarihin ba. Wasu suna cewa an binne ta a makabartar Baqi‘, wasu kuma suna cewa an binne ta a cikin gidanta, yayin da wasu suka ce an binne ta tsakanin kabarin Manzo (s) da minbar dinsa a Masjid an-Nabi (s).

Duk da haka, bisa ga wasiyyarta, Imam Ali (a) a cikin dare ya yi mata sutura, sannan shi da kaɗan daga cikin dangi da sahabbai manya suka yi mata sallah, suka binne ta a wurin mai tsarki ba tare da sanin sauran jama’a ba. Bisa ga wannan ma’anar, Manzon Allah (s) ya ambata a cikin wasu riwayoyi cewa: “A tsakanin kabari na da minbarina dausayi ne na  aljanna”.

Dalilin shahadar Hazrat Fāṭimah (s)

Game da dalili da yanayin shahadar da yadda aka binne ta, al-Tabari a cikin littafinsa Dalā’il al-Imāmah ya kawo riwaya daga Abu Basir cewa Imam Ja‘far as-Sadiq (a) ya ce: Fāṭimah az-Zahra (s) a ranar 3 Jamaadi al-Akhir shekara ta 11 hijira ta yi shahada. Sanadin wannan shahada shi ne cewa Qunfudh, bawa na Umar ibn al-Khattab, a umarnin sa ya buge ta da kashin bakar takobi (tsagin tsini), lamarin da ya sa ciknta (Mahsin) ya zube, kuma ta kamu da rashin lafiya mai tsanani.

Ziyarar khalifofi ga Hazrat Fāṭimah

Sai waɗannan mutanen biyu daga sahabbai (wato Abu Bakr da Umar ibn al-Khattab) suka roƙi Amirul Muminin (a) ya nema musu izinin ziyarar ta, sai Amirul Muminin (a) ya nemi izinin Fāṭimah (s) ta ce a barsu su shigo. Da suka shigo suka tambaye ta: “Yā bint Rasūli-llāh, yaya lafiyarki?” Ta amsa: “Alhamdulillāh, lafiya lau.”

Sannan ta tuna musu maganar Manzo: “Fāṭimah juzi‘un minnī; man aza’aha faqad aza‘anī; wa man aza‘anī faqad aza‘allāh” (Fāṭimah wani ɓangare ce na jiki na; wanda ya cutar da ita, ya cutar dani; kuma wanda ya cutar dani, ya cutar Allah). Suka ce: “Lallai, mun ji Manzon Allah ya faɗi haka.” Sai Fāṭimah (s) ta ce: “Wallāhi, ku biyun kun cutar da ni.” Imam as-Sadiq (a) ya ce: bayan sun fita daga wajen Fāṭimah, ta kasance cikin baƙin ciki da rashin yarda da su.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :