Follow us in
Follow us in

Ina Kabarin Sayyida Zahara? Cigaba…

Yadda aka binne Hazrat Fāṭimah

Abu Ali Muhammad ibn Hammam al-Baghdadi ya ruwaito  cewa: Lokacin da  Fāṭima ta yi shahida, Amirul Muminin (a) ya yi mata sutura; babu wanda ya halarta sai ‘ya’yanta Hasan, Husain, Zainab da Ummu Kulthum tare da Asma bint Umais da Fidda. Daga nan ya ɗauki gangar jikinta cikin duhu na dare tare da Hasan da Husain ya kai ta Baqi‘, ya yi mata sallah, ba wanda ya sani, ba wanda ya yi mata sallah daga sauran mutane. Sai ya binne ta kuma ya boye gurin. Bayan nan sai  ya ƙirƙiri sabbin kabubura guda arba’in. Lokacin da mutane suka san an binne ta a nan, suka je Baqi‘ suka tarar da kabari arba’in da aka ƙirƙira, amma ba su san wanne ne daga cikinsu kabarin Fāṭimah ba.

Sai suka yi kuka, suka zargi juna da gazawa wajen kiyayewa da  girmama ‘yar Manzon Allah (s), suna cewa: “Kaiconmu! Manzonmu bai bar mana yar aba, sai ɗiya ɗaya wato ‘yar sa; wadda ta rasu cikin kadaici kuma an  binne ta cikin dare; ba mu halarci jana’izar ta ba, ba mu yi mata salla ba, ba mu kasance a wajen binne ta ba; yanzu kuma kabarinta a ɓoye yake.”

Martanin khalifofi game da kabarin ɓoye na Hazrat Fāṭimah

Mutanen da ke tafiyar da lamurran (wato Abu Bakr da Umar) sun ji labarin lamarin suka gaya wa mata cewa: “Shin akwai wanda cikin ku zai tona waɗannan kaburburan ya gano kabarin Fāṭimah domin mu yi mata sallah sannan mu sake binne ta a sanannen guri?” Wannan labarin ya je kunnen  Amirul Muminin (a) sai  Ya fusata sosai, idanuwansa suka yi ja, jijiyoyin wuya sun kumbura, ya sa riga mai launin rawaya da yake sanya a lokacin yaki, ya ɗauki takobinsa Zulfiqar ya nufi Baqi‘. Da ya isa, ya yi magana ya ce: “Wallāhi, idan wani ya ɗaga ƙasa ɗaya daga cikin waɗannan kaburbura, zan sare shi da wannan takobi a kansa da wanda ya umarce shi.” A wannan lokaci Umar ibn al-Khattab da mutanensa suka haɗu da Amirul Muminin (a). Umar ya ce masa: “Me ya same ka yā Abul-Hasan! Lallai zamu tona kabarin Fāṭimah mu gano gawarta mu yi mata sallah.” Amirul Muminin (a) ya riƙe rigarsa da hannayensa ya juyar da shi ya jefa shi ƙasa ya ce: Na yi hakuri na hakura da hakkina (na khilāfah) don gudun sabani, mu sa mutane su fita daga addini; amma kabarin Fāṭimah ban zan taba amincewa ba; wallāhi, wani daga cikinku ya taba daya daga wadannan kaburbura to, zan yi wanka da ruwan jinin ku! Idan kana so, gwada, yā Umar!”

A wannan lokaci Abu Bakr (khalifa a lokacin) ya iso yana roƙon Ali ya sassauta, ya roƙe shi ya daina, ya ce babu wanda zai aikata abin da zai ɓata masa rai. Sai Ali ya saki Umar; mutane suka watse, kuma daga wannan lokacin babu wanda ya yi kokarin tona kabarin da Ali ya yi, ko ya fara bincika inda Fatima take.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :