Da sunan Allah mai rahama mai jin kai,tsira da aminci su kara tabbata ga ANNABI MUHAMMAD da iyalan gidan sa tsarkaka.
Iyali kamar wata ƙaramar al’umma ce wadda daga farko take samuwa ta hanyar mata da miji, waɗanda suke kasance tare domin su taimaka wa juna wajen samun cikar kamala ta bangaren ma’anawi (lahira) da kuma ci gaban rayuwar duniya.
Kowane ɗaya daga cikin miji da mata zai zama mai cike gibin ɗaya a cikin ƙauna da tausayi. Kuma duk wani abun da yake neman ya zame musu barazana ko hatsari ga lafiya ko akidar su, su duka za su tashi tsaye wajen kare kansu, su yi gwagwarmaya domin tsira da dorewar rayuwarsu, kuma su shirya makoma da dorewar zuriyarsu.
Alƙur’ani Mai Girma a cikin suratur-Room aya ta 21 yana bayyana wannan babbar ka’ida da kalmomi masu kyawun gaske kamar haka:
ومِنْ آیاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَکُمْ مِنْ اَنْفُسِکُمْ اَزْواجاً لِتَسْکُنُوا اِلَیْها وَ جَعَلَ بَیْنَکُم مَوَدَّةً وَ رَحْمَةً اِنَّ فِی ذلِکَ لاَیاتٍ لِقَومٍ یَتَفَکَّرُونَ»
“Kuma ɗaya daga cikin ayoyinsa shi ne Ya halitta muku mataye daga gare ku domin ku sami nutsuwa a gare su, kuma ya sanya ƙauna da jinƙai a tsakanin ku. Lalle a cikin hakan akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani.”
Imam Muhammad al-Baqir (a.s.) ya ruwaito daga kakansa, Manzon Allah (s.a.w.) yana cewa:
«ما بُنِیَ بَناءٌ فِی الاِسلامِ اَحَبُّ اِلی اللّهِ ـ عزّ وَ جَلّ ـ من التزویج
“Babu wani gini da aka gina a cikin Musulunci mafi soyuwa ga Allah madaukaki fiye da aure.”
Daga wannan maganganu za mu gane cewa tafiyar da al’amarin iyali wani abu ne da addinin musulumci bai bar shi kara zube ba sai dai ya sanya masa wasu ka’idoji na asali kamar haka;
Akwai manyan ka’idoji uku wanda su ne asali wajen kafa iyali, ga su kamar haka;
- A) Kauna Zamantakewar aure
Samar da iyali wani abu ne wanda baya faruwa har sai da namiji ya ji a ransa cewa yana son zama da iyalin, ma’ana namiji yaji cewa yana bukatar abokiyar wadda ta wannan hanyar ne za samar da zuriyar su. Wannan ihsasin (son zama da iyali) na daya daga cikin abubuwan da Allah ya sanya su a cikin halittar ɗan Adam, kamar yadda ake iya ganin hakan yana bayyana har a cikin sauran halittu masu rai wadanda ba ‘yan Adam ba, kuma tun a yarinta hakan ke bayyana a siffa mai rauni wanda zaka ga yaro ko yarinya sukan ji babu dadi a sanda suka kasance su kadai wanda hakan ke sanya su neman abokan wasa.
tun kafin a san batun assasa iyali a doron kasa Allah ya riga ya sanya ƙauna da jinƙai tsakanin namiji da mace, wanda ba su samun nutsuwa ba tare da shi ba. Lokacin da namiji da mace suka samu kusanci da juna domin wannan al’amari mai tsarki—wato aure—kuma suka samu tattaunawa, zai zama kamar suna samun wani abu ne da suka rasa tsawon shekaru. Wannan dalili ne da yasa ba sa son rabuwa da juna cikin sauƙi.
Shi ya sa Manzon Allah (s.a.w) ya ce:
Allah Maɗaukaki ya ajiye tushen aure a cikin halittar ɗan Adam, ta yadda mutum yake jin buƙatar sa a cikin ransa.
kuma ya karanta ta wannan ayar:
جَعَلَ بَیْنَکُم مَوَدَّةً وَ رَحْمَةً اِنَّ فِی ذلِکَ لاَیاتٍ لِقَومٍ یَتَفَکَّرُونَ
“Ya sanya ƙauna da jinƙai a tsakaninku, lalle a cikin hakan akwai ayoyi ga mutanen da suke tunani.”
Wannan ƙaunar da take cikin halitta wata ni’ima ce daga Allah, wadda Manzon Allah (s.a.w.) yake alfahari da ita, kamar yadda ya zo a cikin wani hadisi cewa:
النّکاحُ سُنَّتی فَمَنْ رَغِبَ عَنْ سُنَّتی فَلَیسَ مِنّی
“Aure sunnata ce, duk wanda ya ƙi sunnata, to bay a daga cikin mabiya na.”
- B) Nauyin da ke kan maza a cikin zamantakewar aure
Rayuwar duniya wata aba ce dake cike da wahalhalu da jarabawowi iri-iri, wanda jinsin da namiji yafi iya jure irin wadannan abubuwa fiye da na mace, shi ya sa Allah ta’ala ya dorawa da namiji jagorancin tafiyar da iyali.
A wasu ayoyin Alƙur’ani, za mu ga cewa Allah yana magana ne da maza, wajan ganin cewa sun yi ƙoƙari wajen kafa rayuwar aure, su ɗauki nauyin tsara wannan rayuwa da kuma kulawa da ita. Saboda ci gaba da gudanar da al’amuran rayuwa da samar da duk abin da ake buƙata domin tafiyar da ita, wani abu ne da yake tattare da wahalhalu da ƙalubale mai yawa—wanda wannan wani abu ne da baya dorewa sai da kwanciyar hankali, da ƙarfin zuciya. Saboda haka, Allah ya ɗora wa maza nauyin jure waɗannan matsaloli.
A gefe guda kuma, Allah ya halicci mata domin su kasance wata cibiyar ƙauna, soyayya, kyau, da natsuwa a cikin iyali.
Allamah Ṭabaṭaba’i, babban mai tafsirin Qur’ani, yana cewa:
فالنساء هنّ الرکن الاول والعامل الجوهری للاجتماع الانسانی
“Mata su ne tushe na farko da ginshiƙi na asali na gina al’ummar ɗan Adam.”
Alƙur’ani Mai Girma ya ɗora wa maza nauyin karewa da kuma kulawa da wannan ginshiƙi mai girma (wato mata), bisa la’akari da karfin dauriya da su mazan suke da shi, a inda ya ce :
الرّجالُ قَوّامُونَ عَلَی النّساء بِما فَضَّلَ اللّهُ بَعْضَهُم عَلی بعضٍ وَ بما اَنْفَقُوا مِن اموالِهِم
“Maza su ne masu kula da mata, saboda abin da Allah ya fifita wani sashe daga cikinsu a kan wani, da kuma saboda abin da suke ciyarwa daga dukiyoyinsu.”
- C) Kula da Dorewar Rayuwar Aure
Dorewar rayuwar iyali da zaman aure wata ni’ima ce ta Allah wadda ɗan Adam ke ƙoƙari ya kiyaye ta. Ko wane mutum mai hankali yana so ace duk sanda aka kafa alaƙar aure, to ya zama babu rabuwa cikin sauƙi. saboda haka, wajibi ne akan ginshiƙan biyu na iyali—miji da mata—su guji duk abin da zai kawo rabuwar kawuna, su kuma yi ƙoƙari sosai wajen ƙarfafa zaman auren su.
Dangane da haka Al’qurani mai girma ya na cewa;
وَ هُوَ الّذی خَلَقَ مِنَ الماءِ بَشَراً فَجَعَلَهُ نَسَباً وَ صِهْراً وَ کانَ رَبُّك قديرا
Allah ta’ala shi ne wanda ya halicci mutum daga ruwa sannan kuma ya sanya shi nasaba da surukuntaka (ta wannan hanyar ne Allah ya ke yalwata samuwar dan Adam) kuma Allah a kowane lokaci mai iyawa ne.
A takaice lamarin assasa Iyali wani abu ne da Allah ya tsara domin samar da wanzuwar dan-Adam tun ma kafin ya halicci shi Dan-Adam din.
















