Follow us in
Follow us in

Falalolin Sayyida Fāṭima (a.s.)

Falaloli, siffofi da halayen ṭima, ’yar Manzon Allah, waɗanda bisa ga akidar Shi’a, an yi nuni da su a cikin ayoyin Al-Kur’ani da ruwayoyi. Ita tana cikin Aṣḥābul-Kisā’ da Ahlul-Baiti (a.s.), kuma dukkan falalolin da suka kasance na bai-ɗaya a tsakaninsu suna shafar Sayyida Zahra (a.s.).

Ayoyi da dama kamar Ayatul Taṭhīr da Ayatul Mawadda, da hadisai kamar Hadisin Thaqalain, Hadisin Safīna da Hadisin Amān, suna bayyana falaloli kamar tsarki (’iṣma), wajabcin kauna, daidaituwa da Al-Kur’ani, jirgin Tsira, da kuma zama aminci ga al’ummar Aṣḥābul-Kisā’ da Ahlul-Baiti (a.s.). Haka kuma Suratul Kawthar tana nuni da cewa Fāṭima ita ce alheri mai yawa, kuma ta hanyar ta ne zuri’ar Annabi ta ci gaba.

Wasu daga cikin falalolin Sayyida Fāṭima (a.s.) da aka ambata a cikin hadisai sun haɗa da: mace mafi girma a dukkan duniya, ɓangare na jikin Annabi, farkon mai shiga Aljanna, mai tattaunawa da mala’iku, abin koyi ga Imam Mahdi (a.j.), da kuma matsayin ceto (shafa’a).

Wasu daga cikin manyan malamai na Shi’a kamar Allama Amini, bisa dogaro da wasu ruwayoyi da ke nuna falalolin ṭima (s.a.), sun ɗauke ta a matsayin mafi daraja bayan Manzon Allah da Imam Ali (a.s.), fiye da dukkan annabawa, Imaman Shi’a da mala’iku.

Malamai na Shi’a da Ahlus-Sunna sun rubuta littattafai na musamman game da falaloli da darajojin Sayyida Zahra (a.s.), daga cikinsu akwai:

  • Manaqib Fāṭimatuz-Zahrā’ wa Wuldiha na Ṭabari Imami,
  • ṭima Zahra (s.a.) na Allama Amini,
  • Fadā’il Fāṭimatuz-Zahrā’ daga mahangar wasu na Nāṣir Makārim Shīrāzī,
  • Fadā’il Fāṭimatuz-Zahrā’ na Hākim Naysābūrī,
  • da Al-Thughūr al-Bāsima fī Manāqib as-Sayyida Fāṭima na Jalālud-Dīn Suyūṭī (malami, masani tarihi, mufassiri, fakihi da marubucin mazhabar Shafi’i; ya rasu shekara 911H).

 

Matsayi da Muhimmanci

Falaloli ko manāqib na Sayyida Fāṭima (a.s.) suna nufin siffofi masu kyau da halaye abin yabo na wannan baiwar Allah.  ṭima (a.s.) (an haife ta shekara ta 5 bayan aiko Annab – yi shahada 11H), ’yar Manzon Allah (s.a.w.a.) da Khadīja Kubrā (a.s.) ce, matar Imam Ali (a.s.), kuma mahaifiyar Imam Hasan (a.s.) da Imam Husain (a.s.), Imamai na biyu da na uku a wajen Shi’a.

Ita tana daga cikin biyar na Ahlul-Kisā’ (Ashābul-Kisā’) tana kuma daga cikin Ahlul-Baiti (a.s.) da Ma’asumai goma sha huɗu (a.s.) Bisa akidar malaman Shi’a, ṭima (a.s.) ma’asuma ce, wato tana tsarkakakkiya daga zunubi da kuskure. Sheikh Mufīd da Allama Majlisi sun bayyana cewa tsarkin (’iṣma) Fāṭima (a.s.) abin ijma’i ne a tsakanin malamai.

A wasu littattafan ruwayoyi na Shi’a da Ahlus-Sunna.  an ware babi na musamman domin bayyana falaloli da manāqib na Sayyida Fāṭima (a.s.), haka kuma an rubuta wakoki masu yawa game da falaloli da darajojinta.

An ambaci sunaye da laƙabi da dama ga Sayyida Fāṭima (a.s.) kamar: ṭima, Ṣiddīqa, Ṭāhira, Zakiyya, Rāḍiya, Marḍiyya da Zahrā’.  An kuma faɗa cewa kowanne suna yana nuni da wata falala ko matsayi na musamman na Fāṭima (a.s.)

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :