Girmama iyaye na kara tsawon rayuwa
Imam Muhammad al-Baqir (a.s) ya ce:
Duk wanda yake son rayuwarsa ta tsawaita kuma arziki ya ƙaru, wajibi ne a gare shi ya sanya girmama mahaifi da mahaifiya a cikin muhimman ayyukansa.
Haka kuma ya ƙara da cewa: Dan shi’ar mu shi ne, wanda yake bin Allah da umarninsa.
Daga cikin siffofin da ake gane Shi’a akwai tawali’u, sauƙin kai, rukon amana, yawan ambaton Allah, azumi, yin salla, da girmama iyaye.
A wata ruwayar kuma, wadda aka rawaito daga An‘an bin Sarir, ya zo cewa:
Mun kasance tare da Maysar a wajen Imam Ja‘afar al-Sadiq (a.s), muna tattaunawa game da sada zumunta, Sai Imam ya ce:
“Ya Maysar! Lallai lokacinka (na mutuwa) ya kusanto fiye da sau ɗaya, amma da umarnin Allah an jinkirta shi. Dalilin hakan kuwa shi ne saboda kana sada zumunta. Idan kuma kana son rayuwarka ta ƙaru, kada ka manta da girmama mahaifinka da mahaifiyarka.”
Girmama iyaye na hana talauci
Imam Ja‘afar al-Sadiq (a.s) ya ce: فلیکن بوالدیه بارّاً فإذا کان کذلك لم یصبه فی حیاته فقرا أبداً
“…to ya kasance mai kyautatawa ga mahaifansa; idan ya kasance haka, talauci ba zai same shi a rayuwarsa ba har abada.”
Duk wanda yake son Ubangiji Maɗaukaki Ya sauƙaƙa masa tsananin halin mutuwa (sakaratul-maut), kada ya manta da girmama iyayensa. A irin wannan hali, ba zai taɓa fuskantar talauci a rayuwarsa ba, kuma hakan yana zama sanadin ƙaruwa da albarkar arziki da riba.
Girmama iyaye na zama sanadin shiga Aljanna
Imam Ja‘afar al-Sadiq (a.s) ya ce: قال یأتی یوم القیامه شی ء مثل الکبه فیدفع فی ظهر المؤمن فیدخله الجّنه، فیقال: هذا البرّ
“A ranar Alƙiyama wani abu kama da garkuwa zai zo, sai a sanya shi a bayan mumin, ya shigar da shi cikin Aljanna. Sai a ce: wannan shi ne al-bir (mai biayya ga iyaye).”
Ma’anarsa ita ce: a ranar tashin kiyama, girmama iyaye zai zama kariya ga mumini, kuma zai zama sanadin shigar da shi cikin Aljanna. Za a ce wannan sakamako bai da wani dalili face saboda bai manta da girmama mahaifinsa da mahaifiyarsa ba.
Haka nan kuma, a wani hadisi daga Imam Muhammad al-Baqir (a.s) an ruwaito cewa: أربع من کنّ فیه بنی اللّه له بیتاً فی الجنّه: من آوی الیتیم، و رحم الضعیف و أشفق علی والدیه، و رفق بمملوکه.
“Abubuwa huɗu ne; duk wanda ya kasance ya na aikata su, Allah zai gina masa gida a cikin Aljanna: wanda ya kula da maraya, ya tausaya wa masu rauni, ya nuna jinƙai da girmamawa ga iyayensa, kuma ya yi kyakkyawar mu’amala da bayinsa.”
A cikin wata ruwaya an rawaito cewa: a lokacin da Annabi Musa (tsira ya tabbata a gare shi) yake yin munajati da Ubangijinsa, sai ya ga wani mutum ma yana yin munajati. Sai Annabi Musa ya yi mamaki kuma ya yi kishin matsayi da darajar wannan mutum. Sai aka ruwaito cewa ya ce: “Ya Ubangiji! Ta yaya Ka kai bawanka wannan matsayi?”. Sai Allah Ya amsa masa da cewa: “Ya Musa! Wannan mutum yana kyautatawa kuma yana girmama mahaifansa.”















