Follow us in
Follow us in

FALALAR WATAN AZUMI

Ramadan ɗaya ne daga cikin watannin Hijira, kuma shi kaɗai ne watan da aka ambaci sunansa a cikin Al-Kur’ani a cikin suratul- baqra aya ta 185 inda Allah yake cewa شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ . Haka kuma yana daga cikin watanni huɗu da Allah Madaukakin Sarki ya haramta yaƙi a cikinsu, sai dai idan yaƙin kariya ne. A inda ya ce; مِنْهَا أَرْبَعَةٌ حُرُمٌ daga cikin watannin shekaru akwai wata hudun da yaki a cikin su haramun ne. (suratut-tauba, aya ta 36)

Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka

Ma’anar Kalmar ) رمضانRamadan( ta samo asali ne daga رمضاء wadda a yaren larabci ta ke nufin tsananin zafi, da ma’anar konewa. An kira wannan wata mai alfarma da sunan Ramadan ne domin a cikinsa ana gafarta zunuban mutane.

Manzon Allah (SAW) ya ce: «انما سمى الرمضان لانه یرمض الذنوب ‘An sanya wa watan Ramadan wannan suna ne domin yana ƙone zunubai.’

Ramadan ɗaya ne daga cikin watannin Hijira, kuma shi kaɗai ne watan da aka ambaci sunansa a cikin Al-Kur’ani a cikin suratul- baqra aya ta 185 inda Allah yake cewa شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ . Haka kuma yana daga cikin watanni huɗu da Allah Madaukakin Sarki ya haramta yaƙi a cikinsu, sai dai idan yaƙin kariya ne. A inda ya ce; مِنْهَا أَرْبَعَةٌ حُرُمٌ daga cikin watannin shekaru akwai wata hudun da yaki a cikin su haramun ne. (suratut-tauba, aya ta 36)

Kuma duk wasu littattafan da aka saukar daga sama to a cikin wannan wata na Ramadan aka saukar da su: Al-Kur’ani Mai Girma, Injila, Attaura, Sahifofi da Zabura.”

Ya zo a cikin ruwayoyi cewa, watan Ramadan ‘watan Allah’ ne kuma watan liyafar al’ummar Manzon Allah (SAW). Allah Madaukakin Sarki yana yiwa bayinsa liyafa a cikin wannan wata, cikin dukkanin karamci da rahama.

Manzon Allah (SAW) ya ce: ‘Watan Rajab watan Allah ne, watan Sha’aban watana ne, kuma watan Ramadan watan al’ummata ne. Duk wanda ya yi azumin wannan wata gaba ɗaya, wajibi ne a kan Allah Ya gafarta masa dukkan zunubansa, Ya tabbatar masa da sauran rayuwarsa, kuma Ya tsare shi daga tsananin ƙishirwa da azabar ranar Alƙiyama.

Babu shakka akan cewa watan Ramadan wata ne mai mahimmancin gaske a tsakanin al’ummar mussulmi a aduk fadi duniya, shi yasa zaka ga musulmai tun daga watan rajab da sha’aban su ke kara dagewa da ibadoji domin taren watan Ramadan, kamar yadda hakan ya zo a cikin ruwayoyi, Da shigowar wannan wata, muminai suna tarbiyyantar da kan su a cikin shi ta hanyar ciyarwa da ba da buda-baki ga mabukata, tsayuwar dare da ibada, karatun Al-Kur’ani, addu’a, neman gafara (istigfari), bayar da sadaka, yin azumi, da sauran ayyukan alheri; ta haka ne suke shayar da ruhinsu da zukatansu daga tushen falalar Allah.

Falaloli da romon da ke cikin wannan wata mai alfarma ba zasu kididdiguba, saboda haka wannan rubutu zai mayar da hankali akan wasu daga cikin su ta wajan kawo ruwayoyi daga Ma’asumai (A.S)

Watan ramadan shi ne wata mafi daraja a cikin  watannin shekarar musulumci.

Watan Ramadan mai albarka ya fi sauran watannin kalandar Musulunci daraja, saboda saukar Al-Kur’ani a cikinsa da kuma siffofi na musamman da yake da su. Al-Kur’ani mai girma ya ce:

شَهْرُ رَمَضَانَ الَّذِي أُنْزِلَ فِيهِ الْقُرْآنُ هُدًى لِلنَّاسِ  ۖ

“Watan Ramadan shi ne watan da aka saukar da Al-Kur’ani a cikinsa domin shiryar da mutane.” (Suaratul’ baqra aya ta 185)

Yazo a cikin doguwar hudubar da Manzon Allah (SAW) yayi game da watan Ramadan cewa:

“Ya ku mutane! Watan Allah ya zo muku da albarka, rahama da gafara. Wata ne da a wajen Allah ya fi dukkan watanni daraja; ranakunsa sun fi dukkan ranaku, dararansa sun fi dukkan darare, sa’o’insa sun fi dukkan sa’o’i. Wata ne da aka gayyace ku zuwa baƙuncin Allah, kuma aka sanya ku cikin falalarsa. Numfashinku a cikinsa tasbihi ne, barcinku ibada ce, ayyukanku abin karɓa ne, addu’o’inku kuma ana amsarsu… Sa’o’i ne mafi alheri da Allah ke kallon bayinsa da rahama.”

Wace falala tafi wannan !!!

Ni’imar da ke cikin samun damar azumi

A watan Ramadan, Allah Madaukaki ya bai wa bayinsa damar yin azumi. A inda ya ce:

فَمَنْ شَهِدَ مِنْكُمُ الشَّهْرَ فَلْيَصُمْهُ ۖ

“Duk wanda ya kai ga ganin wannan wata, to ya yi azumi.”

Mutum ba wai iya gangar jiki kadai yake da shi

yana kuma da ruhi da bangaren ma’ana. Kowanne daga cikinsu yana buƙatar tsari na musamman domin kaiwa ga cikakkiyar kamala. Daya daga cikin shirye-shiryen ƙarfafa da bunƙasa ruhaniya shi ne taƙawa da kiyaye kai. Wato, idan mutum yana so ya bunƙasa ruhinsa, ya kai ga tsarki da kamala, dole ne ya fi karfin zuciyarsa, ya kawar da duk wani shinge da zai hana shi ci gaba ɗaya bayan ɗaya, kuma kada ya shagaltu da jin daɗi da sha’awa.

Daya daga cikin ayyukan da suka fi tasiri a domin kaiwa ga wannan hadafi (kawar da bin sha’awe-sha’awen zuciya) shi ne azumi. Al-Kur’ani mai girma ya ce:

يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا كُتِبَ عَلَيْكُمُ الصِّيَامُ كَمَا كُتِبَ عَلَى الَّذِينَ مِنْ قَبْلِكُمْ لَعَلَّكُمْ تَتَّقُونَ

“Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi, kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku, domin ku zama masu taƙawa.

 

 

 

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :