Follow us in
Follow us in

Sirar Imam Hasan (A.S)

Imam Hasan da rayuwarsa.

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai,tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da iayalan gidan sa tsarkaka

Imam Hasan Al’mujtaba (a.s) shi ne Imami na biyu daga cikin jerin Iimaman shiriya, kuma shi ne da na farko ga Imam Ali da Sayyida Fatima (a.s), duk da cewa akwai sabani akan tarihin ranar haihuwar sa amma mafi shahara shi ne cewa an haifi Imam Hasan a shekara ta uku bayan hijirar Annabi daga maka zuwa madina ranar goma shabiyar ga watan Ramadan.

Ranar bakwai ga haihuwar sa Mahaifiyar sa da Mahaifin sa da Manzon Allah (s.a.w) ba su riganyi Allah wajan saka masa suna ba, sun saurara ne har sai da Mala’ika Jibrilu ya zo da wahayi daga wajan Allah cewa a sakawa jaririn da aka haifa sunan Hasan, sannan Annabi (s.a.w) ya yi masa aski kuma ya yi kiran sallah a kunnan sa, kuma ya san ya masa suna Hasan a inda daga nan ya bayar da sadakar azurfa gwargwadon gashin kan Imam Hasan mai albarka, bayan nan kuma ya yanka masa ragon suna.

Al’mujtaba ne kadai al’kunyar da ake kiran Imam Hasan da shi, Imam Bakir ya ce:

إنا لنكنى أولادنا في صغرهم مخافة النبز أن يلحق بهم

Lallai mu muna yi wa ‘ya’yan mu alkunya  tun a yarintar su  domin gudun kada sunan banza ya same su.

Mafi yawan alkunya suna ne da a sa yake farawa da “Abu” ko “Ummu” miisali, ( Abu-Muhammad, Abul-kasim,Abul-Hasan….. Ummu-aiman, Ummu-Kulthum)

Amma akan abin da ya shafi lakabi Imam Hasan yana da lakubba da dama wanda mafi shahara a ciki su ne; Mujtaba, Takiy, Waliy, Sibd, Sayyid.

Mafi yawa daga cikin lafuzzan da ake amfani da su wajan yin lakabi da su, suna nuni ne akan wata sufa ta musamman da shi mai lakabin yake da ita, (Sajjad, Bakirul-Ulum…..)

Imam Hasan ya rayu da Manzon Allah kusan tsawon shekaru bakwai kuma Annabi ne da kan sa ya jibinci lamarin tarbiya da ilmantar da Imam Hasan (a.s), kuma ya kasance mai nuna kauna da yawa akan Imam Hasan, Manzon ya kasance yana dora Imam Hasan akan kafadar sa yana cewa, ya Allah ina son shi kaima ka so shi,kuma ka so duk mai son shi.

kuma ya fada akan Imam Hasan da Imam Husain cewa; duk wanda yake son su to ni yake so, haka kuma duk wanda ya bata musu to ni ya batawa.

An ruwaito daga Anas dan Malik cewa;

Babu wanda ya fi Imam Hasan (a.s) kama da Annabi (s.a.w).

Imam Hasan tun yana dan shekara shida ya fara shiga lamuran siyasa da kuma sakafa, a inda ya halarci mubahala.

Lamarin ya faru ne lokacin da wasu daga cikin wakilan  kiristocin najran,  suka zo Madina sai Manzon Allah ya yi musu tayin yin mubahala kuma su ka yadda, amma sanda shugaban wakilan kiristocin yaga cewa a ranar mubahalar Annabi ya zo da Imam Ali da Sayyada Fatima da Hasan da Husaini sai ya ce sun fasa, domin kuwa wanda ba akan gaskiya yake ba idan zai yi mubahala to bazai zo da ‘ya’yan sa ba, saboda haka zuwan da Annabi yayi da Ali da Fatima da Hasan da Husaini ya nuna cewa akan gaskiya yake shi ya sa su ka fasa yin mubahalar.

Batun mubahala ya zo ne a ciki Al’qur’ani a cikin suratul-Aali Imran aya ta 61, inda Allah Ta’ala y ace;

فَمَنْ حَاجَّك فِیهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءَك مِنَ الْعِلْمِ فَقُلْ تَعَالَوْا نَدْعُ أَبْنَاءَنَا وَأَبْنَاءَکمْ وَنِسَاءَنَا وَنِسَاءَکمْ وَأَنفُسَنَا وَأَنفُسَکمْ ثُمَّ نَبْتَهِلْ فَنَجْعَل لَّعْنَتَ الله عَلَی الْکاذِبِینَ

Imam Hasan yana dan shekara bakwai ya rasa Kakan sa – Annabi Muhammad (s.a.w) da Mahaifiyar sa-Sayyada Fadima (a.s), kuma ya kasance tare da Mahaifin sa a dukkanin abubuwa.

Imam Hasan ya yi musharaka a yakin Jamal, Siffin, da Nahrawan, kuma bayan shahadar Mahaifin sa ya zama shi ne Imami na biyu daga cikin jerin limaman shiriyar gidan Annabta bisa nassi da kuma nadi daga Allah ta hanyar Annabi (s.a.w)

 

 

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :