Follow us in
Follow us in

Halayen Imam Hasan (A.S)

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka.

Ci gaba da rubutun da ya gabata akan rayuwar Imam Hasan (a.s) wanda a wancan rubutun mun  yi tsokaci akan haihuwar sa da kuma wasu abubuwa da suka shafi ladubban haihuwa, a wannan karon kuma rubutun zai mayar da hankali akan bayanin wasu daga cikin halayen Imam Hasan da kuma abubuwan da za’a iya koya.

  • KYAUTA

Wata rana Imam Hasan da Husaini da kuma mijin Sayyada Zainab (a.s) akan hanyar su ta zuwa aikin haji daga madina zuwa makka guzurin su ya kare musu, ba tare da jimawa ba can sai suka gamu da tantin wata tsohuwa a kan hanya, sai suka isa zuwa gare ta suka yi mata sallama kuma suka nemi taimakon ta ba tare da ta san suba, sai tace musu saidai bani da komai sai waccan akuyar, sai ta tashi ta tatsar musu nonon akuyar ta basu suka sha, sannan tace musu su kama akuyar su yanka bayan sun yanka sai ta hura wuta ta dafe musu wannan akuya ta basu, bayan sun kammala suka ci gaba da tafiya akan hanyar su ta Birnin Makka mai girma.

Jim kadan sai mijin wannan mata ya dawo sai ta kwashe labarin abin da ya faru ta gaya masa, sai ya nuna bacin ran sa akan haka yace;

ta yaya baki san mutane ba za ki kama akuya kwaya daya tilo da muka mallaka ki dafe musu suci?!

Bayan wani lokaci sai yanayin rayuwa ya sanya wannan mata da mijin ta tafiya Birnin madina neman kudi, wata rana matar nan tana yayo a cikin garin madina sai ta wuce ta kofar wani gida sai aka yi sa’a Imam Hasan yana kofar gida sai ya hangi wannan mata amma ita bata gane shi ba, shi kuma ya gane ta, sai ya yi mata sallama ya ce baki gane niba ko ?

sai tace ‘Eh,

sai ya tuna mata abin da ya faru na irin taimakon da ta yi musu, sannan ya kira daya daga cikin hadiman sa ya ce yaje ya bata kyautar dabbobi guda dubu biyu, bayan nan kuma yasa aka kai ta wajan ‘Dan uwan sa Imam Husain shima yasa aka bata kyaitar dabbobi guda dubu biyu, daganan yasa aka kai ta wajan Mijin Sayyada Zainab shi kuma ya bata  kyautar dabbobi dubu daya.

Haka suka sakawa wannan mata da mafi yawan abun da sa yi musu na aikin alkhairi. ALLAHU AKBAR !

Allah Ta’la ya fada a cikin suratul-An’am aya ta 160 cewa;

مَنْ جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أَمْثَالِهَا

Duk wanda ya zo da kyakkyawan aiki guda daya to yana da kwatankwacin  sa guda goma.

Imam Sadiq (a.s) dangane da wannan ayar yace; wannan ayar ta shafi kowa da kowa musulmi da kafiri, duk wanda ya aikata kyakkyawa ga wani to wajibi ne ya saka da kyakkyawa.

A kissar da ta gabata a sama Imam Hasan (a.s) ya koya mana yadda ake saka alkhairi da mafificin alkhairi ,wato idan aka ce yau ga wani mutun ya yi maka wani alkhairi to yana da kyau shi ma a saka masa da mafificin abinda ya yi na alkhairin da ya aikata idan an samu dama, kamar yadda yazo a cikin suraturrahman aya ta 60 cewa;

هلْ جَزَاءُ الْإِحْسَانِ إِلَّا الْإِحْسَانُ هَلْ جَزَاءُ

Ba komai bane sakamakon kyakkyawan aiki face kyakkyawa.

 

   2- HAKURI DA JURIYA YAYIN IBADA

An ruwaito cewa Imam Hasan ya yi aikin haji sau ashirin da biyar kuma ta kasa sannan babu takalmi, kuma sai aka ga duk sanda za’a tafi aikin hajin Imam Hasan yana tafiya a bayan kafilar matafiya aikin hajji ta yanda kurar ababan hawan da ake tafiya da su kamar su rakuma,dawakai,jakuna,ds. take dawowa jikin sa, da yake a zamanin da idan za’a tafi aikin haji akan hadu ne a tafi cikin jama’a saboda yanayin hanya, sai aka tambaye shi dalilin yin haka sai Imam yace; Manzon Allah (s.a.w) yace;

أفْضَلُ الاْعْمالِ أحْمَزُها

Mafificin ayyuka shi ne aikin da yafi ko wane wahala.

Mafi yawan ladar ayyukan ibada tana komawa ne zuwa ga wahalar ita ibadar a jiki ko a ruhi, ma’ana duk ibadar da tafi wahala a jiki ko a ruhi to wannan ibadar tafi yawan lada, saboda wannan dalilin ne Imam Hasan ya yi aikin haji dai dai har guda ashirin da biyar babu takalmi, kuma yana biye da bayan ababan hawan dake dauke da masu aikin hajjin da kuma kayayyakin su domin kurar su ta ringa komawa jikin sa domin neman babban sakamako a wajan Ubangijin sa.

Hakan yana koya mana yin juriya da hakuri akan duk wata ibada da Allah ya dora mana musammam ma irin ibadojin da suke da wahalar aikatawa ga jikin Dan-Adam ko a ruhin sa.

 

 

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :