Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka.
Daya daga cikin abubuwan da Al’qur’ani mai girma ya kebanta da shi, shi ne cewa littafi ne na tarbiyyantar da Al’umma, wanda gaba dayan ayoyin sa wani lokacin kai tsaye wani lokacin ba kai tsaye ba, suke magana akan tarbiyyar mutum a dukkannin matakan rayuwar sa kama tun daga yarinta har zuwa tsufa.
Daya daga cikin bangarorin tarbiyya wanda yake da mahimmancin gaske shi ne tarbiyyar yara, domin kuwa masu iya magana suna cewa; “icce tun yana danye ake tankwara shi” a cikin surorin Al’qur’ani mai girma za mu ga ayoyin da suke magana akan Annabawa da tarihin rayuwar su da ‘Ya’yan su suna magana akan tarbiyyar yara.
MAHIMMANCIN TARBIYYAR ‘YA’YA A MAHANGAR AL’QUR’NI
Nauyin da ya hau kan iyaye na tarbiyyar yara daya ne daga cikin mas’alolin da musulunci ya ke bijuro da su, wanda hakan ke da muhimmanci a mahangar Al’qur’ani.
Nuna mahimmanci ga tarbiyyar ‘Ya’ya da Iyali na daya daga cikin abin da Allah ta’ala a cikin suratul-furqan ya sanya a matsayin siffofi na musamman ga muminan bayi, saboda suna jin cewa suna da nauyi a kan su na daukar tarbiyyar iyalan su, Allah ya ce;
وَالَّذِينَ يَقُولُونَ رَبَّنَا هَبْ لَنَا مِنْ أَزْوَاجِنَا وَذُرِّيَّاتِنَا قُرَّةَ أَعْيُنٍ وَاجْعَلْنَا لِلْمُتَّقِينَ إِمَامًا (سورة الفرقان, الآية 74 )
Wadanda suke cewa, ya Uban gijin mu ka sanya daga cikin matan mu da ‘Ya’yan mu su zama farin cikin idanun mu.
Haka kuma, a cikin aya ta shida a Suratul-Tahrim, yazo cewa fatan alkhairi ga iyali da tarbiyyantar da su a kan addini wajibi ne ga muminai, magana ce ga dukkan muminai, a inda ake umartar su da tarbiyyar mata da ‘ya’ya da iyali.
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا قُوا أَنْفُسَكُمْ وَأَهْلِيكُمْ نَارًا وَقُودُهَا النَّاسُ وَالْحِجَارَةُ (سورة التحريم اللآية 6)
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! Ku kiyaye kanku da iyalanku daga wuta wadda makamashin ta mutane ne da duwatsu.”
‘Ya’ya kamar wani fure ne wanda iyaye ke da alhakin renon shi, kamar yadda mai lambu yake kula da furanni domin ƙamshinsa ya faranta zuciyar iyali da al’umma.
Mai lambu idan yana son ya samar da furanni masu kamshi, dole ne ya yi aikin sa yadda ya kamata, kamar haka abin yake akan Iyaye dole su raini ‘ya’yan da suka haifa yadda ya kamata, kuma su sauke haƙƙin ‘ya’yan su kama tun daga shayarwa, zaɓin suna mai kyau, koyar da Alkur’ani, tarbiyyar addini, girmamawa da mutunta ‘ya’ya, da adalci tsakanin ‘ya’yan su ne abubuwan da iyaye ya kamata su mai da hankali a kai.
Ni’ima na daya daga cikin abubuwan da Allah ke jarabtar bayin sa da ita, kamar yadda za’a iya sanya jarabtar mutane ta hanyar ‘ya’ya a cikin ire – iren wadannan jarabawoyi. Saboda haka ne ma, Allah a cikin wasu ayoyi na Alqur’ani mai girma yake nuni da hakan, kamar yadda ya zo a cikin Suratul-Anfal aya ta 28 inda yake cewa;
وَاعْلَمُوا أَنَّمَا أَمْوَالُكُمْ وَأَوْلَادُكُمْ فِتْنَةٌ
Ku sani cewa lallai dukiyoyin ku da ‘ya’yan ku hanyar jarabtar ku ne.
Haka ma kuma a suratut-tagabun aya ta 14 ya ce;
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّ مِنْ أَزْوَاجِكُمْ وَأَوْلَادِكُمْ عَدُوًّا لَكُمْ فَاحْذَرُوهُمْ
Ya ku wadanda kuka yi Imani lallai wasu daga cikin matayen ku da ‘ya’yan ku (saboda dauke ku da suke yi daga aikata umarnin Allah da Manzo) makiyan ku ne. Dama wasu ayoyin daban, da Allah ya ke yi wa muminai gargadi game da jarabawa ta hanyar ‘ya’ya, domin su zama cikin shiri kuma su tattara hankalin su domin tunkarar irin wannan jarabawa mai wuya da haɗari.
Daya daga cikin hanyoyin tarbiyya mafi kusa wanda ‘ya’ya suka fi saurin dauka shi ne kwaikwayon abin da suke ganin ana aikatawa a gaban su, wanda mutane na farko wadanda ‘ya’ya za su fara kwaikwayo daga gare su su ne iyaye, kuma duk abin da suka koya, to daga baya akan wannan suke dorawa, saboda ma’amalolin da ke tsakanin ‘ya’ya da iyayen su ita ce kashin bayan duk wata tarbiya da za su koya a tsawon rayuwar su.
Shi yasa Alqur’ani mai girma yake sukar wadanda suke umartar mutane da kyakkyawan abu amma kuma suna mantawa da kawunan su, saboda idan har baka aikata abu, to yana da wuya wani ya iya koyar wannan abun daga gare ka, Allah ta’ala yana cewa;
أَتَأْمُرُونَ النَّاسَ بِالْبِرِّ وَتَنْسَوْنَ أَنْفُسَكُمْ وَأَنْتُمْ تَتْلُونَ الْكِتَابَ ۚ أَفَلَا تَعْقِلُونَ (سورة البقرة, الآية 44)
Shin kuna umartar mutane da kyakkyawan aiki amma kuma kuna mantawa da kayuwan ku……
A suratul-saf aya ta 2 Allah ya ce;
يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا لِمَ تَقُولُونَ مَا لَا تَفْعَلُونَ….
Ya ku wadanda kuka yi Imani me yasa kuke fadar abinda bakwa aikatawa..
Shi yasa za mu ga cewa Al’qur’ni mai girma ya bayyana Annabi (s.a.w.a) a matsayin cikakken abin koyi a aikace domin tarbiya a aikace aka fi saurin koya in da yake cewa;
لَقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ
Lallai manzon Allah kyakkyawan abin koyi ne a wajan ku
NUNA SOYAYYA GA YARA
Babu shakka akan cewa nuna soyayya ga ‘ya’ya wata dabi’a ce abar so, domin kuwa kowa yana son a nuna masa soyayya musamman nuna soyayyar Iyaye ga ‘ya’yan su, shi ya sa ma idan muka duba ruwayoyin Ahlu-baiti (a.s) za mu ga mafi yawan lokaci suna magana akan nuna soyayya ga ‘ya’ya, a wani wajan ana nuna fa’idar nuna soyayyar, misali akwai wani hadisi da Manzon Allah ya ce;
إنَّ اللهَ عَزَّوَجَلَّ لَیرْحَمُ الرَّجُلَ لِشِدَّه حُبَّهِ لِوُلدِهِ.
Lallai Allah madaukain sarki yana gafartawa mutum saboda tsananin nuna soyayyar da yake yi ga ‘ya’yan sa.
A wani hadisin kuma Imam Sadiq (a.s) ya bada umarni da cewa a nuna soyayya ga yara inda ya ce;
أحِبُّوا الصِّبیانَ وَ ارحَموهُمْ وَ إذا وَعَدْتُمُوهُم شَیئاً فَفُوا لَهُم فَإنَّهُمْ لایدْروُنَ إلّا أنَّکمْ تَرْزُقُونَه
Ku so yara kuma ku tausaya musu, kuma duk lokacin da kuka yi musu alkawarin wani abu to ku cika musu, saboda ba su sani ba face cewa ku ne kuke azurta su.
GIRMAMA YARA
Girmama yara ma daya ne daga cikin hanyoyin tarbiyyantar da su, kamar yadda muka fada a baya cewa, ma’amala mai kyau da nuna halayen kirki ga yara na sanya su yaran su koyi irin wannan halin kwaran da suka ga ana aikatawa, a sanda yaro ya ga ana nuna masa girmamawa to shi ma zai yi kokarin aikata wannan hali ga sauran mutane.
Kuma saboda shi dama can Dan-Adam abin girmamawa ne kamar yadda Qur’ani, a cikin suratul-isra aya ta 70 ya koyar;
وَلَقَدْ كَرَّمْنَا بَنِي آدَمَ وَحَمَلْنَاهُمْ فِي الْبَرِّ وَالْبَحْرِ وَرَزَقْنَاهُمْ مِنَ الطَّيِّبَاتِ وَفَضَّلْنَاهُمْ عَلَىٰ كَثِيرٍ مِمَّنْ خَلَقْنَا تَفْضِيلًا
Lallai mun girmama Dan-adam …
A mahangar addinin musulumci yara da matasa ma sun cancanci karamci da girmamawa, kuma dole a girmama dabi’ar su, kuma Iyaye suna da alhaki mai girma wajan kula da gina shakhsiyyar ‘ya’yan su, kamar yadda dole ne bisa asalin karama da girman da Allah yaba Dan-Adam Iyaye su yi ma’amala da ‘ya’yan su bisa gimamawa (mutumtaka).
KOYARWA
Koyar da ‘Ya’ya asalin addini da hukunce hukuncen sa, wani nauyi ne da Allah ya ɗorawa Iyaye, sai dai kuma koyarwa kadai ba zata wadatar ba, dole sai an haɗa da kula da juriya da hakuri wajan aikata wadannan ibadoji kamar yadda Allah ya fada a cikin Suratu Ɗaha aya ta 132 ya ce;
وَأْمُرْ أَهْلَكَ بِالصَّلَاةِ وَاصْطَبِرْ عَلَيْهَا
Ka umarci iyalan ka da yin sallah kuma ka yi hakuri akan ta.
WA’AZANTARWA
Hanyar wa’azantarwa tana daga cikin hanyoyin da Allah ya sanya domin tarbiyyantar da dukkanin ‘Yan-adam kamar yadda hakan ya zo a aya ta 125 a cikin Suratun-nahli;
ٱدْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِٱلْحِكْمَةِ وَٱلْمَوْعِظَةِ ٱلْحَسَنَةِ وَجَٰدِلْهُم بِٱلَّتِى هِىَ أَحْسَنُ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِۦ وَهُوَ أَعْلَمُ بِٱلْمُهْتَدِينَ
Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijin ka (addini) da hikima da kyakkyawan wa’azi….
ƘARFAFAWA DA TSORATARWA
Karfafawa da tsoratarwa ta fuskacin samar da fata da samar da karfin gwiwa ga yara da albishir, na daga cikin hanyoyin da ake tarbiyyantar da ‘ya’ya da su.
Abu na ƙarshe da zamu takaita a kan sa shi ne;
KAWAR DA KAI DA YIN AFUWA A YAYIN DA ‘YA’YA SUKA BAYYANA NADAMA BISA KUSKUREN DA SUKA AIKATA
A lokacin da ‘ya’yan Annabi Ya’aqub (a.s) ‘yan uwan Annabi Yusuf (a.s) suka yi ikirari akan laifin da suka aikata na jefa Yusuf a cikin rijiya kuma suka bayyana nadamar su akan hakan kamar yadda ya zo a cikin Al’qur’ani mai girma cewa;
قَالُوا يَا أَبَانَا اسْتَغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا إِنَّا كُنَّا خَاطِئِينَ
Suka ce ya babanmu ka nema mana gafarar zunubanmu lallai mu mun kasance masu kuskure
Suka nemi Baban su ya nema musu gafarar Allah’ sai ya amsa musu da cewa zai nema musu gafarar Allah domin Allah mai gafara ne ya ce;
قَالَ سَوْفَ أَسْتَغْفِرُ لَكُمْ رَبِّي إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ
Idan yaro ya aikata laifi ga iyayen sa kuma daga baya ya yadda yayi laifi kuma ya bayyana nadamar sa a kan haka, to yana da kyau Iyaye su yafe masa kuma su roki Allah ya yafe masa domin yin hakan hali ne na Annabawa.














