Follow us in
Follow us in

Mahimmancin Shawara

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka.

 

Yin shawara a cikin addinin Musulunci yana da muhimmanci ƙwarai wajen ƙarfafa dangantakar zamantakewa da kuma tafiyar da al’amuran rayuwa. Sai dai kuma yana da kyau a fahimci cewa, akwai wasu ƙa’idoji da ya kamata abi domin yin shawara. Wadanda sai an kiyaye su yadda ya kamata, sannan shawara take iya warware matsaloli. Amma idan aka yi watsi da waɗannan ƙa’idoji da ginshiƙai, kuma ba a kula da dukkan bangarorinsu ba, to babu abin da shawara zata iya gyarawa sai ma dai ta kara dagula lamurra.

Saboda haka, domin fahimta da gane ƙa’idojin da ya kamata abi domin yin shawara, wajibi ne a koma zuwa ga ingantaccen tushe, don kaucewa yin shawara da nau’in mutanen da ba su dace ba. Haka kuma, ya kamata a sani cewa lokaci da wuri suna da tasiri a cikin shawarwari.

Don sanin waɗannan abubuwa da kuma ma’aunai daban-daban na shawarwari, ya kamata a koma ga maganganun Annabi da Iyalan gidansa, wannan rubutu zai mayar da hankali akan maganganun Amirul-mu’unin Ali dan Abi Dalib (a.s), wajan fitar da wadannan ƙa’idoji da ginshiƙan shawara daga maganganunsa musamman a cikin nahajul balaga.

Muhimmancin yin shawara wani abu ne bayyananne a addinin musulumci ta yadda bama wai yana matsayin larura bane kadai a’a har ma ya kai matsayin wani abu wanda ke hana yin kurakurai kuma yake hana kaucewa daga hanya.

Sanannen abu ne cewa gaba dayan ma’asumai sun wadatu daga sai wani ya basu shawara saboda alakar da suke da ita da Allah, amma saboda kiyaye hakki da kuma girmama hankalin wadanda su ke tare da su, zaka samu cewa wasu lokutan suna yin shawara da mutane, amma kuma hakan baya nufin cewa idan sun yi shawarar to kuma dole ne su gabatar da abun da aka gaya musu din.

Shi ya sa Allah ta’ala a cikin suratul-ahzab aya ta 36 ya ce;

وَمَا كَانَ لِمُؤْمِنٍ وَلَا مُؤْمِنَةٍ إِذَا قَضَى اللَّهُ وَرَسُولُهُ أَمْرًا أَنْ يَكُونَ لَهُمُ الْخِيَرَةُ مِنْ أَمْرِهِمْ ۗ وَمَنْ يَعْصِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ فَقَدْ ضَلَّ ضَلَالًا مُبِينًا

baya kasancewa ga mumini ko mumina ya zama suna da wani zabi a sa’ilin da Allah da Annabi suka zartar da wani al’amari…..

akan mahimmancin bada shawara da fadar gaskiya Imam Ali (a.s) yana cewa:

فَلَا تَكُفُّوا عَنْ مَقَالَةٍ بِحَقٍّ أَوْ مَشُورَةٍ بِعَدْلٍ

Kada ku kame daga fadar Magana da gaskiya ko wata shawara ta adalci.

Saboda haka babu wani mutum da zai wadatu da yin amfani da shawarar mutane ko da kuwa ya fisu ilimi, kamar yadda ya zo a cikin wani hadisi cewa:

«لاَ يَسْتَغْنِي اَلْعَاقِلُ عَنِ اَلْمُشَاوَرَةِ »

Mai hankali baya wadatuwa daga yin shawara

Yin shawara da masana alama ce ta hangen nesa wadda ke kiyaye duk mai yin shawara daga yin kuskure.

Kamar yadda a wani wajan Imam Ali (a.s) ya fada cewa:

شاوِرْ ذَوي العُقولِ، تَأمَنِ الزَّلَلَ و النَّدَمَ؛

Ka shawarci ma’abota hankula, zaka kubuta daga kurakurai da nadama.

Lallai yin shawara wani abu ne mai mahimmanci gaske, domin kuwa cike yake da alkhairi da kuma albarka. Kamar yadda Amirul-mu’umina ya fada;

جماع الخير في المشاورة و الأخذ بقول النصيح

Dukkanin alkhairai sun tattaru ne a cikin yin shawara da kuma karbar nasiha.

Wata tambaya da take da muhimmanci wadda ya kamata mu sani shi ne cewa, da wa ya kamata a yi shawara kuma wa ya kamata ya bada shawara ?

Kafin bayar da amsa wannan tambayar yana da kyau mu san cewa yin shawara ko bada shawara yana da ladubba wadanda sai an kiyaye su ake kaiwa ga abin da ake so, saboda akwai irin mutanen da ya kamata ayi shawara da su kuma akwai wadanda bai dace ayi shawara da su ba.

Bisa la’aka da maganganun Imam Ali (a.s) za mu ga irin mutanen da ya dace ayi shawara da su da kuma wadanda bai dace a yi shawara da su ba.

Ga jerin irin mutanan da ya kamata a yi shawara da su:

shawara da mutane masu tsoron Allah

Shawara da mutane masu ilimi

Shawara da mutane masu hankali

Shawara da mutane masu tunani

Shawara da mutane masu hangen nesa

Shawara da mutane masu tajruba.

 

  • Yin shawara da Mutane masu hankali

Yin shawara da mutane masu hankali alama ce ta hangen nesa, wanda yin hakan ba yana kaiwa ne ga samun ci gaba ba kadai, a’a duk wanda ya ke yin shawara zai kubuta daga yin kuskure da kuma kaucewa hanya, saboda hankali shi ne kashin bayan shakhsiyya duk wani mutum, kuma duk wata dabara ko fahimta ko ilimi to mabubbugar sa shi ne hankali, shi yasa Imam Ali ya ke cewa:

شاوِرْ ذَوي العُقولِ، تَأمَنِ الزَّلَلَ و النَّدَمَ

Ka shawarci ma’abota hankula zaka kubuta daga kurakurai da nadama.

A wani wajan kuma ya ce:  مَن شاوَرَ ذَوِي العُقولِ استَضاءَ بأنوارِ العُقولِ

Wanda ya yi shawara da ma’abota hankula zai haskaka da hasken hankula.

 

2) shawara da mutane masu tsoron Allah

Mutane masu tsoron Allah suna daya daga cikin jerin mutanen da ake shawara da su, mutanen da aka sani da tsoron Allah.

Kamar yadda mahimmancin hankali wajan bayar da shawara bai boyar wa kowa ba, to hakama tsoron Allah yana iya kaiwa ga hanya mai kyau a fannin bada shawara kamar yadda tasirin takawa (tsoron Allah) ke iya warware matsaloli da yawa kuma ya kiyaye kauce hanya.

  • Shawara da mutane masu tajruba

Daya daga cikin abubuwa masu mahimmancin da ya kamata a lura da shi a harkar shawara shi ne tajruba da gwaji.

Imam Ali (a.s) ya ce:

أفضَلُ مَن شاوَرتَ ذو التَّجارِبِ

Wanda ya fi cancanta ayi shawara da su su ne ma’abota tajruba, lallai mutumin da yake da tajruba akan abu, to shi ya fi dacewa da ayi shawara da shi kan wannan abun da yake da tajrubar sa, domin kuwa ya gwada abin kuma duk wasu marhalolin da ya kamata abi ya bi.

  • Shawara da mutane masu hangen nesa

Daya daga cikin Kari akan wadanda ya kamata ayi shawara da su, sune mutane masu hangen nesa, hangen nesa alama ce ta hankali Imam Ali (a.s) ya ce:

الظَّفَرُ بِالْحَزْمِ، وَ الْحَزْمُ بِإِجَالَةِ الرَّأْيِ، وَ الرَّأْيُ بِتَحْصِينِ الْأَسْرَارِ

Nasara na tare da hangen nesa, hangen nesa kuma ya na tare da aiki da hankali, ingantancen tunani kuma yana cikin boye sirri ka.

A mahangar addinin musulumci hangen nesa yana tare da abubuwa masu mahimmanci, kamar hankali, tajruba da masaniya, shi ya sa duk sanda mai hangen nesa aka nemi ya bada shawara to ya na kallon abubuwa ne ta kowane bangare sannan ya fitar da natijar da ya ke so ya bada.

  • Shawara da mutane masu tunani

Nazari da zurfin tunani daya ne daga cikin abubuwan da yake da tasiri wajan fitar da sakamako akan al’amura, yin tunani yana kawo kwarin hankalin mutum, kuma yin hakan wata wasila ce ta yin amfani da  masaniya akan abubuwan da ke bukatar gwaji:

Imam Ali ya ce: صَوَابُ اَلرَّأْيِ بِإِجَالَةِ اَلْأَفْكَار

Madaidaiciyar matsaya tana tare da nazartar lamura.

Abin da wannan hadisi ya ke nufi shi ne cewa, idan ya zama cewa mai bayar da shawara yana da wadataccen ilimi cikakken hankali da tajruba to kuma dole ya zama yana iya yin cikakken tunani domin ya iya fitar da sakamako mai kyau.

Amirul-mu’uminina Ali (a.s) a wasika ta 53 a cikin nahajul balaga ya gaya wa  Malikul-ash’tar cewa:

وَ أَکْثِرْ مُدَارَسَةَ الْعُلَمَاءِ، وَ مُنَاقَشَةَ الْحُکَمَاءِ، فِي تَثْبِيتِ مَا صَلَحَ عَلَيْهِ أَمْرُ بِلاَدِك، وَ إِقَامَةِ مَا اسْتَقَامَ بِهِ النَّاسُ قَبْلَکك

ka yawaita tattaunawa da masana, kuma ka yawaita nazari da mutane masu hikima (kuma wannan tattaunawar da nazarin) ya zama akan tabbatar da abubuwan da al’amuran kasar ka suka gyaru ne, kuma da tsayar da abun mutanen da suka gabaceka su ka tsayu a kan shi.

 

 

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp