Follow us in
Follow us in

RASHIN YIN SHAWARA DA MUTANEN DA BA SU CANCANTA BA

Yin shawara da mutanen da basu cancanta ba, wani abu ne da hankali ke iya fahimta, saboda duk wanda ka ji yana neman shawara, to yana neman wata hanya ce wadda yake so yabi domin aikata wani abu mai mahimmancin da baya so ya fada cikin kuskure, bisa la’akari da hakan, yana bukatar nau’in mutanen da za su bashi shawara ya zama ba su da suffofin da za mu ambata a cikin wannan rubutu. Saboda haka, Imam Ali (A.S.) ya gargadi mutane da kada su yi shawara da mutanen da ba su cancanta ayi shawara da su ba..

Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da iyalan gidansa tsarkaka.

 

Kamar yadda ya gabata a baya mun bayyana nau’in irin mutanan da ya kamata ayi shawara da su, kamar yadda Imam Ali (a.s) ya bayyanawa Malik – Ashtar a cikin wasika mai lamba ta 53 a nahajul- balaga.

A wannan karon kuma za mu kawo jerin kalar mutanen da bai dace ayi shawara da su ba, kamar yadda Imam Ali ya bayyana a cikin wasikar da muka ambata a sama.

 

RASHIN YIN SHAWARA DA MUTANEN DA BA SU CANCANTA BA

Yin shawara da mutanen da basu da cancanta ba wani abu ne da hankali ke iya fahimta, saboda duk wanda ka ji yana neman shawara to yana neman wata hanya ne wadda yake so yabi domin aikata wani abu mai mahimmancin da baya so ya fada cikin kuskure, bisa la’akari da hakan yana bukatar nau’in mutanen da za su bashi shawara ya zama ba su da suffofin da za mu ambata a cikin wannan rubutu.

Saboda haka, Imam Ali (A.S.) ya gargadi mutane da kada su yi shawara da mutanen da ba su da cancanta. Kuma ya bayyana kalar mutanan kamar haka:

 

  1. Mutum mai tsoro

A cikin wasiƙar da Imam Ali (a.s)  ya rubutawa Malikul – Ashtar, game da hani da yin shawara da mutum mai tsoro ya ce:

«وَ لاَ تُدْخِلَنَّ فِي مَشُورَتِکَ … وَ لاَ جَبَاناً يُضْعِفٌك عَنِ الاْمُورِ

“Kada ka shigar da mutum mai tsoro cikin shawararka, zai raunana maka gwiwa wajen gudanar da al’amura.”

  1. Mutum mai rowa

A game da hani da yin shawara ko karbar ra’ayi daga wajan mutum mai rowa Imam Ali (a.s), ya rubuta wa Malik cewa:

«وَ لاَ تُدْخِلَنَّ فِي مَشُورَتِکَ بَخِيلاً يَعْدِلُ بِکَ عَنِ الْفَضْلِ وَ يَعِدُکَ الْفَقْرَ؛

“Kar ka shigar da mai rowa cikin shawararka, domin zai hana ka aikata alheri, kuma zai tsoratar da kai da talauci.”

Daga wannan magana mai jan hankali, za mu iya fahimtar cewa duk wani marowaci ya tasirantu ne da waswasin shaidan, kuma a cikin maganarsa da ayyukansa yana kama da shaidan, kamar yadda Allah ya fada a cikin suratul baqra a aya ta 268 cewa:

الشَّيْطَانُ يَعِدُكُمُ الْفَقْرَ وَيَأْمُرُكُمْ بِالْفَحْشَاءِ

Shaidan yana tsoratar da ku da talauci (a duk lokacin da za ku ciyar da dukiyar ku) kuma yana umartar ku da ayyuka maras kyawu (kamar rowa da kin bayar da zakka da sadaka)

 

  1. Mutum mai kwaɗayi

Imam Ali (a.s) ya hani Malik al-Ashtar da yin shawara da mutum mai kwadayi, kamar yadda ya rubuta masa cewa:

 

«لاَ تُشْرِكَنَّ فِي مَشْوَرَتِكَ حَرِيصاً يُهَوِّنُ عَلَيْكَ اَلشَّرَّ وَ يُزَيِّنُ لَكَ اَلشَّرَهَ؛

lallai ka da ka sanya mutum mai kwadayi a cikin shawararka, domin zai sa zalunci ya zama abu mai sauƙi a gare ka, kuma zai kawata maka son tara dukiya da kwaɗayi.

  1. Mutum mai son ra’ayin kansa

Daya daga cinin rukunin mutanen da ya zama dole a gujewa yin shawara da su, su ne muttanen da ra’ayinsu ne kawai ra’ayi. Saboda su irin wadannan mutanen basa yin la’akari da fannoni daban-daban na al’amura ko ra’ayoyin wasu, su suna nacewa ne akan ra’ayinsu kadai, kuma suna rufe zuciyarsu ga duk wata magana da ta saɓa da tasu. Addinin Musulunci ya yi gargadi sosai game da irin wannan hali da kuma mummunan tasirinsa.

Imam Ali (a.s.) ya ce:

لا تَستَبِدَّ بِرَأيِكَ، فَمَنِ استَبَدَّ بِرَأيِهِ هَلَكَ

Kada ka zama mai son ra’ayinka kawai, domin duk wanda ya dogara ga ra’ayinsa kaɗai zai halaka.”

 

  1. Mutum maƙaryaci

Imam Ali (a.s) ya yi hani da yin shawara da mutum maƙaryaci, wanda ya ke bayyana abubuwan karya da siga mai kyau, kuma yake ganin shi bai cancanci ya fadi gaskiya ba a inda ya ce:

لاَ تَسْتَشِرِ اَلْكَذَّابَ فَإِنَّهُ كَالسَّرَابِ يُقَرِّبُ عَلَيْكَ اَلْبَعِيدَ وَ يُبَعِّدُ عَلَيْكَ اَلْقَرِيبَ

Kada ka yi shawara da maƙaryaci, domin shi makaryaci kamar turirin da ake hangowa ne daga nesan hamada ne, wanda kana kusanto inda yake za kaga ya kara maka nisa (ruwan al’janu), ya na kusanto maka da abin da yake nesa kuma yana nesanta maka da abin da yake kusa.

Imam Ali (a.s.) ya kwatanta maƙaryaci da tiririn da ake hangowa daga nesa, wanda ta hanyar ƙarya yake karkatar da gaskiya, yana kuma jefa mutum cikin ɓata da ruɗani. Babu shakka neman shawara daga irin wannan mutum abu ne mai haɗari kuma bai kamata a yarda da shi ba.

 

  1. Mutum jahili

Jahilci shi ne tushen dukkanin munanan ayyuka da kuma asalin dukkanin munanen halaye. Kuma shi jahilci yana samun asali ne daga girman kai da son kai, kuma yana kai wa ga rashin samun mafita a cikin al’amura. Saboda haka, Imam Ali (a.s) ba suka ga jahilci kadai ya yi, ya ma bayyana neman shawara daga jahili a matsayin abu mai haɗari. Kamar yadda ya ce:

مُشَاوَرَةُ اَلْجَاهِلِ اَلْمُشْفِقِ خَطَر

Yin shawara da jahili mai nuna tausayi abu ne mai haɗari.

 

  1. Mutum mai taurin kai

Daya daga cikin abubuwan da suke hana samun ingantacciyar shawara, kuma ya ke kama da son kai, shi ne taurin kai. Wannan mummunan hali alama ce ta raunin hali, kuma abu ne wanda ya ke hana tunani da yin nazari mai kyau, da kuma hana harshe bayyana gaskiya.

A gaskiya, ba a sa ran mutum mai taurin kai zai ba da shawara ta alheri ko kuma ya gabatar da ra’ayi mai ƙarfi. Kamar yadda Sarkin masu tsoron Allah, Imam Ali (a.s.), ya ce:

اللَّجَاجَةُ تَسُلُّ الرَّأْيَ

Taurin kai yana lalata tunani.

Kasancewar taurin kai yana hana mutum yin tunani mai kyau da bayyana ra’ayi mai amfani da shiryarwa, kuma yana jawo damuwa da hasara, Imam Ali (A.S.) ya bayyana shi a matsayin mummunan hali. Ya kuma bayyana mai taurin kai wanda ba ya karɓar gaskiya da kalmomi kamar: mutum marar hankali mai munanan ɗabi’u, mai karkatacciyar fahimta, mai haddasa fitina da kuma marar hikima.

 

  1. Yin shawara da maƙiyi

Imam Ali (a.s.) ya hana yin shawara da maƙiyi, a inda yake cewa:

لاَ تُشَاوِرْ عَدُوَّكَ وَ اُسْتُرْهُ خَبَرَكَ

Kada ka yi shawara da maƙiyinka, kuma ka ɓoye masa labaranka.

Wannan Magana ta hikima, duk da gajartarta, amma tana ɗauke da ma’ana mai zurfi. Kamar yadda take gargadar mutum da kada ya nemi shawara daga maƙiyi saboda hakan ba zai kawo masa wata fa’ida ba sai dai ma ya jawo masa cutuwa, kuma hakan zai sa sirrin sa ya yadu.

Duk da cewa a wani wajan Imam Ali (a.s) saboda wani yanayi na daban, ya bada umarnin yin shawara da makiyi, ba dan komai ba sai dan saboda da a gane girman kiyayyar da makiyin ke da ita a inda ya ce:

اِسْتَشِرْ أَعْدَائَكَ تَعْرِفْ مِنْ رَأْيِهِمْ مِقْدَارَ عَدَاوَتِهِمْ وَ مَوَاضِعَ مَقَاصِدِهِمْ؛

Ka yi shawara da maƙiyanka domin ka gane gwargwadon ƙiyayyarsu daga ra’ayoyinsu, kuma ka san inda suka nufa da manufofinsu.

Abin da za mu iya fahimta a wannan hadisin shi ne cewa, domin sanin girman ƙiyayyar maƙiyi da kuma samun muhimman bayanai game da ƙarfinsa na soja, da shirye-shiryensa na yaƙi, ana iya tattaunawa da shi. Amma irin wannan aiki wata dabara ce ta yaƙi, kuma ba za a iya kiran ta shawara ta gaskiya ba.

Kammalawa

Daga koyarwar Imam Ali (a.s.) muna iya fahimtar cewa yana da kyau mutum ya yi taka-tsantsan wajen zaɓen waɗanda zai nemi shawararsu. Ba’a shawara da mutum mai tsoro, ko rowa, ko kwaɗayi, ko mai son kan sa, ko maƙaryaci, ko jahili, ko mai taurin kai. Saboda halayen irin wadannan mutane, na iya karkatar da mutum daga gaskiya, ko su jefa shi cikin kuskure da asara. Saboda haka, wajibi ne a nemi shawara daga mutane masu hikima, amana, ilimi da kyawawan ɗabi’u, domin samun sakamako mai kyau da nasara a cikin al’amura.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp