Wane ciwo ne yake sa a ajiye azumi?
A zahirin ayar tana nuna kowane irin ciwo yana sa a sha azumi, kuma wannan ciwo kaɗan ne, wanda za a iya daurewa ko mai yawa wanda ba za a iya daurewa ba, kamar yadda aka naƙalto cewa Ibn Sirin saboda yana ɗan jin ciwo a yatsar sa ya karya azumin sa; da wannan dalilin cewa ma’auni shine duk wani abu da ake cewa ciwo, kamar tafiya saboda haka ya kamata mu bincika ra’ayoyi daban-daban da suka shafi wannan mas’alar.
RA’AYOYI
AHLUS-SUNNA
Ƙurɗabi ya rubuta cewa: Ciwo ya kasu kashi biyu:-
Na farko: shine ciwo mai tsanani, wanda ya kai ga baza a iya jurewa azumi ba. A wannan yanayin, wajibi ne a ajiye azumi.
Na biyu: shine mara lafiya da duk tsanani da wahala zai iya yin azumi. A wannan yanayi mustahabbi ne kar yayi azumi, haka nan kuma ya naƙalto daga Abu Hanifa cewa:
“اذا خاف الرجل على نفسه وهو صائم إن لم يفطر أن تزداد عينه وجعاً أو تزداد حمّاه شدة أفطر”.
Sannan ƙurɗabi ya fifita ra’ayin Ibn Sirin kuma ya rubuta:
“قول ابن سيرين اعدل شيء في هذا الباب”
Jaziri ma a wajen naƙalto nazarorin ahlus-sunna a cikin I’izarul mubiha ya rubuta cewa: “Abu Hanfa da Shafi’i da Maliki sun ce: Idan mai azumi ya kamu da rashin lafiya kuma yana jin tsoron rashin lafiyar tasa ta ƙaru, ko kuma a sami jinkiri wajen warkewarta ko kuma azumi yana da wahala mai tsanani a gareshi, ya halatta ya karya azumi. amma shafi’i yana ganin karya azumi a wannan yanayi sunna ce, kuma yin azumi a wannan yanayi bidi’a ne. amma idan yin azumin mara lafiya ya kai ga ana tunanin hallaka ko cutauwa mai tsanani wanda ya kai ga gushewan hankali, karya azumi wajibi ne, kuma yin azumi haramun ne.
Sakamakon waɗannan ra’ayoyi shi ne kamar haka:
- Hana karya azumi a ciwuka ƙanana.
- Halacci ko mustahabbancin karya azumi a ciwo mai tsanani.
- Dole da wajibcin karya azumi a ciwo mai wahala.
MALAMAN FIƘIHU MABIYA AHLUL BAIT
Daya daga cikin fuƙahan shi’ar ahlil bait (a.s) muhaƙƙiƙi Hilli ya yi nuni da wannan mas’alar inda ya rubuta:
“المرض الذي يجب معه الافطر،ما یخاف به الزیاده بالصوم”،
Rashin lafiyar da yake sanyawa a buɗa baki, shine: “ciwon da
yake ake jin tsoron karuwarsa saboda yin azumi, Mai jawahir Ma a sharhin
ibarar muhaƙƙiƙ ya rubuta:
“لو صام مع تحقق الضرر متكلفا قضى.”
Kuma a wani wurin ya rubuta:
“ضرورة عدم جواز الصوم للمريض الذي يتضرر بالصوم يزيادة مرضه أو بطؤ برئه أو حدوث مرض آخر أو مشقة لا تحمل أو نحو ذلك،و انه اذا تکلفه مه ذلك لم يجزه،بل کان آثما بلا خلاف.”
Ayatullah Tabayaba’i,mai littafin urwa ma yana ganin azumin da yake haifar da rashin lafiya (cuta) shima yana daga cikin azumi da aka hana.
A gungun waɗannan fatawoyi za a iyi cewa mara lafiya zai iya buɗe baki ne da sharaɗin cutuwa, dole ne kuma, idan yayi azumi, ba wai kawai bai sauke takalifinsa bane, a’a sai ma kasancewarsa mai laifi.
Zahirin aya ma haka take nuna wa; saboda tana cewa:
“فمن كان منكم مريضا…فعدة من أيام أخر…”،
Wannan aya tana cewa a kwanakin rashin lafiya, ba a nemi mara lafiya yayi azumi ba.
IYA KANCE AYA (تخصیص آیه)
Na’am, kamar yadda aka faɗi: iɗilaƙin ayar, an iyakance shi da ruwayoyi, kuma abin da ta ƙunsa ya iyakance ne ga ciwo mai tsanani, ko ya kara tsananin ciwo, ko ya kawo wani ciwon da makamancin haka, kamar yadda yazo a ruwayar Aliyu ɗan Jafar daga Imam Kazim(a.s):
“سألت عن حد ما يجب على المريض ترك الصوم؟ قال: كل شيء من المرض اضر به الصوم فهو يسعه ترك الصوم.”
Kuma yazo a ruwayar Muhammad ɗan Muslim:
“قلت لأبي عبدالله ما حد المريض اذا نقه في الصيام، فقال: ذلك اليه، هو اعلم بنفسه اذا قوی فلیصم”.
B- MARA LAFIYA A NAN GABA
Aya tana cewa: “…فَمَنْ كَانَ مِنْكُمْ مَرِيضًا” yanzu tambayar da za ta biyo baya ita ce, shin ayar tana nufin wanda yanzu ne bashi da lafiya ko kuma ta haɗa da wanda akwai yiwuwar rashin lafiyarsa a nan gaba?
Daga fatawoyin malaman fiƙihu za a iya fahimtar cewa babu bambanci tsakanin wanda ake tunanin rashin lafiyarsa da wanda bai da lafiya a halin yanzu.
Jaziri bayan bayanin fatawoyi a kan mara lafiya ya rubuta: “waɗannan suna cikin waɗanda basu da lafiya yanzu, kuma game da mutum mai lafiya wanda akwai yiwuwar zaiyi rashin lafiya nan gaba shine:
– Hanbaliyya suna cewa: ajiye azumi sunna ne kuma yin sa makaruhi ne
– Malikiyya sunyi imani da cewa: ajiye azumi wajibi ne.
– Hanafiyya sun ce: buɗe baki halas ne.
– Shafi’iyya sunyi imani da cewa: ajiye azumi bai halasta ba a lokacin da ba a tabbatar da cutuwa daga yin azumi ba.
Malaman Shi’a sun nuna rashin yardan su a wannan batun kuma sun ce: Abin da yake sa a ajiye azumi, tsoron cutarwa ne; ba tare da wani bambanci ba tsakanin mai lafiya da mara lafiyaba.
Saboda haka za a iya cewa: mace mai shayarwa da mace mai ciki wanda yin azumi zai iya cutar da ita ko ɗanta, za a haɗa ta ne da mara lafiya da kuma wanda zai cutu idan yayi azumi.
BINCIKE
Duba ga zahirin ayar azumi da mahallin ta, hukuncin mara lafiya da matafiyi duk iri ɗaya yake bayanin su, wannan hukunci ba za ayi amfani da ita ba, saboda amfani da (كان), yana bayyana ne a wanda ba shi da lafiya a halin yanzu. amma a dalilin kore wahala da cutarwa
دليل نفي عسر,حرج و ضرر
Daɗi da wannan ruwayar a matsayin cikakkiyar doka, da yake nuni da wannan (tsokaci) kamar ruwayar Saduƙ da ya ruwaito daga ma’asum (a.s) yana cewa:
كلما أضر به الصوم فاالافطار له واجب
Saboda haka a sakamakon karshe za a iya cew: a mas’alar da ta shafi azumi a ƙur’ani, wannan abu ya bambanta da iyakakkun da aka buɗaɗasu a cikin aya.
















