Follow us in
Follow us in

AMFANIN YIN AZUMI

Babu shakka akan cewa yin azumi wani abu ne dake da matukar amfani ga lafiyar dan - adam kari akan abubuwan da Allah ya yi alkawari zai bawa duk wani mai yin azumi a ranar gobe kiyama. A yau a fannin ilimin likitanci da kiwon lafiya da yanayin halittar jikin mutum, an tabbatar da cewa azumi yana da tasiri mai yawa wajen bawa ruhi da tunanin dan- Adam natsuwa da kwanciyar hanakali, da kuma lafiyar jiki.

Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidan sa tsarkaka.

Amfanin yin azumi ga lafiyar Dan-Adam

Babu shakka akan cewa yin azumi wani abu ne dake da matukar

amfani ga lafiyar dan – adam kari akan abubuwan da Allah ya yi alkawari zai bawa duk wani mai yin azumi a ranar gobe kiyama.

A yau a fannin ilimin likitanci da kiwon lafiya da yanayin halittar jikin mutum, an tabbatar da cewa azumi yana da tasiri mai yawa wajen bawa ruhi da tunanin dan- Adam natsuwa da kwanciyar hanakali, da kuma lafiyar jiki.

Azumi yana taimakawa wajen kawar da kitsen da ya wuce kima, daidaita hawan jini, daidaita sukarin jini, da sauransu. Wannan duk hujja ce a fili dake nuna ingancin hadisan da suka zo da bayanai akan haka.

Manzon Allah (a.s) ya ce: “Ku yi azumi domin ku kasance cikin koshin lafiya.”

Ya kuma ce: “Ciki shi ne gidan dukkan cututtuka, kuma kamewa (azumi) shi ne mafi girman magani.”

Ga kadan daga cikin fa’idojin yin azumi a mahangar Ah’lul-baiti (A.S)

  • Ƙarfafa taqwa, tsoron Allah da ikhlasi:

Daya daga cikin abubuwan da yin azumi ke karawa wa mutun shi ne karfin Imani,wanda duk wanda ke da karfin Imani to ba shakka zai zama mai biyayya ga dokokin Allah ta’ala. Akwai hadisai da daman gaske wanda su ke magana akan haka ga kadan daga cikin su.

Imam Sadiq (a.s) ya ce; Allah Madaukaki Ya faɗa: الصِّيامُ لي وَأَنَا أَجْزي بِهِ. “Azumi nawa ne, kuma Ni ne zan ba da ladansa.”

Sayyada Fatima (s.a) ta ce: “Allah Ya wajabta azumi domin ƙarfafa ikhlasi.

2-Kariya daga azabar duniya da ta lahira:

Babu shakka akan cewa yin azumi na bada kariya daga shiga wutar lahira, kamar yadda duk mai yin azumi yana rabuwa daga musibun duniya, domin kuwa bijirewa dokokin Allah abu ne wanda ke jawo masibu tun a nan duniya.

Imam Ali (a.s) ya ce: “Azumi yana rage nauyin ciki, yana narkar da nama, kuma yana nesanta mutum daga zafin wutar Jahannama.”

Manzon Allah (s.a.w) ya ce: “الصَّومُ جُنَّةٌ مِنَ النَّارِ. Azumi garkuwa ne daga wuta.”

3- Natsuwar hankali da jiki:

Azumi yana kawo natsuwa ga ruhi, zuciya da gangar jiki, kuma yana zama sanadiyyar lafiyar ruhi da ƙarfin jiki.

Manzon Allah (a.s) ya ce: “Ku yi azumi domin ku kasance cikin koshin lafiya.”

Ya kuma ce: “Ciki shi ne gidan dukkan cututtuka, kuma kamewa (azumi) shi ne mafi girman magani.”

Imam Baqir (a.s) ya ce: “Azumi da Hajji suna sanyaya zukata.”

Imam Ali (a.s) ya ce: “Allah yana kiyaye bayin sa muminai ta hanyar salla, zakka da azumin watan Ramadan domin kwantar da gabobinsu, rage girman kai, tawali’u, da kaskantar da zukatansu.”

4- Kariya daga sharrin Shaidan:

قَالَ أَمِيرُ الْمُؤْمِنِينَ عَلِيٌّ عليه السلام قُلْتُ: يَا رَسُولَ اللَّهِ، مَا يُبْعِدُ الشَّيْطَانَ مِنَّا؟

قَالَ: الصَّوْمُ يُسَوِّدُ وَجْهَهُ، وَالصَّدَقَةُ تَكْسِرُ ظَهْرَهُ

Imam Ali (a.s) ya tambayi Manzon Allah (s.a.w) cewa: “Ya Manzon Allah! Wane abu ne yake nisantar da Shaidan daga gare mu?”

Sai Annabi (s.a.w) ya amsa da cewa: “Azumi yana baƙanta fuskar shaidan, sadaka kuma tana karya bayansa.”

Saboda haka, azumi yana hana Shaidanun aljanu da na mutane samun damar yin tasiri, kuma yana lalata waswasinsu.

5- Daidaito tsakanin mawadata da matalauta:

Mutum mai azumi, a lokacin yunwa da ƙishirwa, yana tunawa da talakawa da mabukata, kuma hakan yana sa ya hanzarta taimaka musu.

قَالَ الْإِمَامُ الْحَسَنُ الْعَسْكَرِيُّ عليه السلام إ ِنَّمَا فَرَضَ اللَّهُ الصِّيَامَ لِيَجِدَ الْغَنِيُّ مَسَّ الْجُوعِ، فَيَعُودَ بِذَلِكَ عَلَى الْفَقِيرِ.

Imam Hasan Askari (a.s) game da dalilin wajabcin azumi ya ce: “Domin mai arziki ya ɗanɗana zafin yunwa, ko hakan ya sa ya taimaki mabukaci.”

6- Raya kyawawan halaye da ɗabi’u masu kyau:

ِنَّمَا أُمِرُوا بِالصِّيَامِ لِيَعْرِفُوا أَلَمَ الْجُوعِ وَالْعَطَشِ، فَيَسْتَدِلُّوا عَلَى فَقْرِ الْآخِرَةِ،

:عليه السلام قَالَ الْإِمَامُ الرِّضَا

وَلِيَكُونَ الصَّائِمُ خَاشِعًا مُتَوَاضِعًا ذَلِيلًا، صَابِرًا، طَالِبًا لِلثَّوَابِ،

وَلِيَعْرِفُوا مَا يُصِيبُ أَهْلَ الْفَاقَةِ وَالْمَسْكَنَةِ، فَيُؤَدُّوا إِلَيْهِمْ حُقُوقَهُمْ

 

Imam Rida (a.s) game da dalilin wajabcin azumi ya ce: “Domin mutane su ɗanɗana wahalar yunwa da ƙishirwa, su gane buƙatarsu a Lahira; kuma mai azumi, sakamakon yunwa da ƙishirwa, ya zama mai tawali’u, mai ƙasƙantar da kai, mai haƙuri, mai neman yardar Allah da ladansa, mai ilimi da juriya, ta haka ya cancanci lada…

Azumi yana hana bin sha’awa; kuma yana zama nasiha ga mutane a duniya, yana horar da su wajen aiwatar da wajibansu, yana zama jagora zuwa ga lada; haka kuma yana sa su fahimci irin wahalar yunwa da ƙishirwa da mabukata da miskinai ke fuskanta a duniya, domin su biya haƙƙoƙin da Allah Ya wajabta a cikin dukiyoyinsu…”

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :