Follow us in
Follow us in

Sadaka a Mahangar Al-Kur’ani da Sunna

Zamantakewa da Taimakon Juna

A cikin addinin Musulunci, kamar yadda ba a halatta samun kudin shiga ta kowace hanya ba, haka ma ba daidai ba ne a kashe dukiya a ko wace hanya. Ɗaya daga cikin hanyoyin da addinin Musulunci ya amince da su wajen kashe dukiya ita ce bayar da sadaka a cikin hanyar Allah. Bayar da dukiya dimin Allah a cikin hanyar Allah, wannan dukiyar da aka bayar ana kiranta da “sadaka”.

Ma’anar Sadaka:
Sadaka ita ce wani abu da mutum ke fitarwa daga dukiyarsa da niyyar kusanci da Allah, kamar yadda ake bayar da zakka daga dukiya. A hakikanin gaskiya, sadaka na iya zama wajiba (kamar zakka) ko mustahabbiya (lokacin da mutum yaso ya samu lada). Amma duk lokacin da aka ce sadaka yawancin tunanin mutane ya na tafi ne a kan sadakar mustahabbi.

MUHIMMANCIN SADAKA:
cikin suratul-Attauba aya ta 104, Allah (t) yana cewa:
> “Shin ba su sani ba cewa Allah ne ke karɓar tuba daga bayinsa, kuma Shi ne ke karɓar sadakoki?”
“Haƙiƙa Allah Mai karɓar tuba ne, kuma Mai jin ƙai.”
Wannan aya tana bayani cewa Allah ne kadai ke karɓar tuba da sadaka daga bayinsa.
Saboda haka, ya kamata wanda ke bayar da zakka ko sadaka su kasance da tawali’u(ƙasƙantar da Kai), ladabi da girmamawa, domin wanda ke karɓar sadakar; Allah(t) ne.

Imam Sajjad(a.s) ya ce:
> “Lallai sadaka ba ta shiga hannun bawa har sai ta shiga hannun Ubangiji.”
Abun nufi shine kafin sadaka ta kai ga mabukaci, tana zuwa ga Allah ne farkohaka kuma ladar ta daga Ubangijiya na iso wa ga mutum.
Alƙur’ani da Hadisai sun hore mu da kin yi izgili ga mabukata sabo da yin hakan saɓawa dokar Allah ne da ma addini baki daya.
Ruwayoyi da dama sun ƙarfafemu wajen bayar da sadaka, musamman a lokuta na musamman kamar ranaikun Jumma’a, Arafat, da cikin watan Ramadan, haka ma wannan ruwayar ta karfafemu wajan bayar da sadaka ga mabuƙata na kusa kamar makwabta da ’yan uwa inda take cewa:
> “Ba da sadaka ga na nesa alhalin akwai mabukaci a dangi be dace ba.
Sabo da haka idan mutum yana da mabukata a dangin su; (to kamata yayi lokacin da zai bada sadaka ya fara ta kansu sannan na waje), haka ma kuma makwabci ma damar makwabcin mu na buƙata ua kamata mu fara da shi sannanna nesa.
Hadisi ya zo daga Ma’aiki (s.a.a.w) ya ke ce wa: Ina rantsuwa da wanda babu wani abin bauta sai Shi, lallai sadaka tana kawar da cuta, gobara, da hauka har ya lissafa abubuwa guda saba’in daga sharrukan da mutum ke samun kariya daga su ta hanyar bayar da sadaka
A wata ruwaya kuma an ce:
> “Fara yinin rana da sadaka yana korar bala’in ranar; kuma fara dare da ita yana kawar da bala’in dare.”

Imam Ali(a.s) ce:
> “Albarka ta tabbata ga dukiyar wanda ya ciyar da abin da ya wuce buƙatarsa daga dukiyarsa, ya kuma ƙaurace wa yawan magana.”
(Bihar al-Anwar, j.96, sh.117)

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :