Busharar Annabi (sawa) ga Sayyida Zahra a Imam Mahadi (as)
ورد في المجم الصغير للطبراني الصغير: 1 / 37 ، عن أبي أيوب الأنصاري قال : « قال رسول الله ’ لفاطمة : نبينا خير الأنبياء وهو أبوك ، وشهيدنا خير الشهداء وهو عم أبيك حمزة ، ومنا من له جناحان يطير بهما في الجنة حيث يشاء ، وهو ابن عم أبيك جعفر ، ومنَّا سبطا هذه الأمة الحسن والحسين ، وهما ابناك ، ومنا المهدي
Ya zo a cikin Al-Mu’ujams sagir na Xabarani, juzu’i na 1, shafi na 37, daga Abu Ayyub Al-Ansari, ya ce: “Manzon Allah (sawa) ya ce wa Faxima: Annabinmu shi ne mafificin annabawa, kuma shi ne mahaifinki, kuma Shahidinmu shi ne mafificin shahidai, kuma shi ne Ammin babanki Hamzah, kuma a cikinmu akwai yake da fuka-fukai guda biyu zai tashi da su a cikin Aljanna, shi ne ammin babanki Jafar, kuma a cikinmu akwai jikokin wannan al’umma, wato Al-Hassan da Husaini, kuma su biyun ‘ya’yanki ne, kuma daga cikinmu a kwai Al-Mahdi.
وفي مسند فاطمة للسيوطي / 47 و 93 : « أبشري يا فاطمة ، فإن المهدي منك
Kuma a cikin Musnadu Faxima na Suyuxi: a shafi na 47 da 93: “Ki yi Bushara da murna ya Faxima, domin Mahadi daga gare ki yake
وفي ينابيع المودة / 81 ، عن مناقب الخوارزمي : ومنا سبطان وسيدا شبان أهل الجنة ، ابناك ، والذي نفسي بيده إن مهدي هذه الأمة يصلي عيسى بن مريم خلفه ، فهو من ولدك
A cikin Yanbi’ Al-Mawaddah, shafi na 81, bisa lafazin Al-Khwarizmi Annabi (sawa) ya ce: Kuma a cikinmu akwai jikoki biyu, kuma shuwagabnnin samarin Aljannah, su ne ‘ya’yanki guda biyu, na rantse da wanda rayuwata take hannusa, hxixa mahadi na wannan al’umma, Isa xan Maryam zai yi salla a bayansa, shi wannan Mahadin yana daga cikin ‘ya’yanki (zuriyark).
















