Follow us in
Follow us in

Dangantaka Tsakanin Arziki Da Anbaton Allah

Dangantaka Arziki zikri tsoron Allah Budin Rayuwa Qur'ani ruwayoyi

suke bude hanyoyin albarka. A wasu wurare a cikin Al-Qur’ani, yazo cewa,idan mutum ya samu kansa a gaban zaɓi biyu – ɗaya ambaton Allah, ɗaya kuma duniya (kamar kasuwanci, kuɗi..) – to ya kamata ne ya fifita ambaton Allah akan duniya.

A mahangar Al-Qur’ani da kuma ruwayoyi , hakan yana kawo yalwatar arziki da kuma albarkatun  rayuwa.

A cikin suratul Jumu’a, Allah ya umarta da cewa:

إِذَا نُودِيَ لِلصَّلَاةِ مِنْ يَوْمِ الْجُمُعَةِ فَاسْعَوْا إِلَى ذِكْرِ اللَّهِ وَذَرُوا الْبَيْعَ

“Idan an kira zuwa ga sallah a ranar Jumu’a, to ku yi sauri zuwa ambaton Allah, ku bar saye da sayarwa.” (Jumu’a: 9)

Wato, idan aka kira sallah, a bar kasuwanci da neman duniya, a gabatar da ambaton Allah. Ko da kuwa lokacin ana cikin tsananin ciniki ne, sai a fifita ambaton Allah akan wannan cinikin.

Idan lokacin kiran sallah ya zo, ya kamata musulmi ya ji cewa ya fi son zuwa masallaci da yin sallah akan kasuwanci.

Kamar yadda Idan ranar Ashura ta zo, dole ne in ji cewar na fi son zuwa zaman makokin Imam Husaini akan aikina da kuma kasuwanci na.

A ko da yaushe, idan aka samu zaɓi tsakanin ambaton Allah da duniya, ya kamata ambaton Allah ya fi mahimmanci, sai dai idan aikin yana da mahimmancin da mai yawa barin nasa na iya haddasa matsala.

Misali, Dan kasuwar dake da shagon shan magani (chemist) kuma ga marar lafiya ya zo sayan magani ta yanda idan ba,a sayar masa ba mai hakan na iya kara hatsari ga lafiyar sa, ko kuma ma duk wani nauin sana’ar da idan aka rufe wajan yin ta hakan na iya cutar da Al’ummar musulmi to a irin wannan yanayin Addinin musulumci ya yi rangwane anan.

Kai bisa umarni na shari’a wajibi ne ma mutum ya bar shagon nasa a bude.

Ko kuma idan hakan na iya kawo tsayawar zirga – zirga kamar tsayawar dukkan motocin haya –  jiragen sama, dana ƙasa, metro – mutane za su sha wahala. A irin wannan yanayin, direba ko ma’aikacin da ya fita aiki ba don duniya ya fita ba, ya tafi ne akan taimakon Al’umma to yin haka na daga cikin wajibin shari’a. Kuma yana daga cikin ambaton Allah.

Manufarmu ita ce mu canza tunaninmu a rayuwa.

Maimakon mu sa burinmu ya kasance kuɗi da kasuwanci da annashuwa, ya zama muna da manufar addini da ɗan Adamtaka a aikace.

Mutum ya kasan ce cewa ako wane irin sana’a burinsa shi ne:

 yin aiki domin samun kuɗi, da kuma ɗaga matsayin rayuwar Alummar Musulmai , da kuma haɓaka tattalin arzikin su, domin ganin sun  fita daga talauci.

 *Ina son in kawo ɗaukaka* da ‘yancin kai ga al’ummata, domin kada mu kasance marasa ƙima a idon makiya.

Akwai ruwayoyi da yawa akan haka da za su zo nan gaba:

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :