Follow us in
Follow us in

GIRMAMA IYAYE A MAHANGAR AH’LUL BAITI

Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da Iyalan gidansa tsarkaka.

 

Bisa la’akari da cewa ranar zagowar haihuwar Sayyada Fatima ‘Yar Manzon Allah (s.a.w) rana ce da aka yi wa lakabi da ranar uwa ta duniya, ko kuma ranar mata da duniya, haka zalika cewar ranar zagayowar haihuwar Imam Ali (a.s) ita ma rana ce da aka yi wa lakabi da ranar mahaifi ko kuma ranar maza ta duniya, bisa la’akari da wadannan munasabobi guda biyu na zabi nayi wannan rubutu kuma na saka masa suna da;

MAHIMMANCIN GIRMAMA IYAYE A MAHANGAR AH’LUL BAITI

A cikin ayoyin Al-Kur’ani da kuma ruwayoyin Imamai Ma’asumai (a.s),an bayyana dukkanin ayyuka da halayen da idan mutum ya kasance yana aikata su zai shiga Aljanna, kuma suke ɗaga darajar mutum zuwa matsayi mai girma.

Saboda nufin takaita wannan rubutu zamu takaita bayani a kan wasu daga cikin wannan halaye bisa maida hankali akan nuna mahimmancin biyayya ga iyaye, domin ta hanyar aikata hakan ne za mu kasance daga cikin waɗanda suke cin moriyar wannan ni’ima madawwamiya daga Allah.

Girmama iyaye da mutumtasu a cikin ko wace irin al’umma wani abu ne wanda a hankalce da kuma a al’adance ya yi daidai da tsarin da kuma gudanar rayuwar dan adam, shi yasa ma idan muka dubi tsarin addinin musulumci za mu ga yadda qur’ani da kuma ruwayoyi da maganganun malamai su ke karfafa wannan magana, ta yadda har ya zama wani babban ginshiki ne a cikin ginshikan addini.

Ta yadda ya zama cewa duk wanda bai girmama mahaifi da mahaifiyarsa ba, daidai da yi musu magana cikin fushi ko daga musu murya, ba wai kawai zai fuskanci azabar Allah Maɗaukaki a Lahira ba, har ma a duniya ba zai sami wata riba ko alheri daga rayuwarsa ba.

Allah ta’ala ya na cewa dai-dai da “uf” kada ka gaya wa iyayen ka,فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ  da sunan fushi.

Wannan wani abu ne wanda a wannan zamanin, mu ke gani da idanummu, yadda mutanen da ba su yi kyakkyawar mu’amala da iyayensu ba suke fuskantar rugujewar rayuwarsu, kuma kullum suna shiga matsaloli iri-iri.

Saboda haka, duk wanda yake son ya more rayuwa kuma ya rawu cikin jin dadi a wannan duniya, dole ne ya zama ya na mu’amala da iyayensa cikin girmamawa da nuna ƙauna da tausayi.

Saboda girman muhimmancin wannan al’amari (gimama iyaye), Alƙur’ani mai girma ya yi umarni kuma ya yi maganganu masu yawa game da iyaye, har ma a wasu wurare ya kawo batun kyautata da girmama iyaye tare da magana a kan tauhidi (kaɗaita Allah).

وَقَضَى رَبُّكَ أَلَّا تَعْبُدُوا إِلَّا إِيَّاهُ وَبِالْوَالِدَيْنِ إِحْسَانًا إِمَّا يَبْلُغَنَّ عِنْدَكَ الْكِبَرَ أَحَدُهُمَا أَوْ كِلَاهُمَا فَلَا تَقُلْ لَهُمَا أُفٍّ وَلَا تَنْهَرْهُمَا وَقُلْ لَهُمَا قَوْلًا كَرِيمًا 

A cikin wata ruwaya da aka ruwaito daga Imam Sadiq (a.s) ya zo cewa,batun girmama iyaye yana daga cikin jerin mafificin ibadoji a wajan Allah: Sallah a kan lokaci ne mafificin ayyuka, sannan biyayya ga iyaye da kuma jihadi akam tafarkin Allah……أفضلُ الأعمالِ الصَّلاةُ لوقتِها ، و بِرُّ الوالديْنِ و الجِهادُ في سبيلِ

A wani wajan kuma an tambayi manzon Allah (s.a.w) cewa wane aiki ne mafi soyuwa a wajan Allah ? sai ya ce : sallah a kan lokacin ta, ya ce sai kuma me ? sai ya ce : bin iyaye,

سَأَلْتُ النبيَّ صَلَّى اللهُ عليه وسلَّمَ: أيُّ العَمَلِ أحَبُّ إلى اللَّهِ؟ قالَ: الصَّلاةُ علَى وقْتِها، قالَ: ثُمَّ أيٌّ؟ قالَ: ثُمَّ برُّ الوالِدَيْنِ،

Manzon Allah (s.a.w) ya yi bayani game da muhimmancin girmama iyaye, inda ya ce: نظر الولد الی والدیه حباً لهما عبادة “kallon ɗa ga iyayensa saboda ƙauna, ibada ne.”

wato kallon iyaye da ƙauna da tausayi yana da ladan ibada. Haka kuma ya yi nuni da cewa yardar Allah tana cikin yardar iyaye da girmama su.  رِضا اللهِ فی رِضا الوالِدَین ِ

Haka nan kuma Imam Ja‘afar al-Sadiq (a.s) game da girmama iyaye yace: أفضلُ الأعمالِ الصَّلاةُ لوقتِها ، و بِرُّ الوالديْنِ و……

“Mafi kyawun ayyuka a wurin Allah shi ne yin salla a lokacinta, kyautatawa iyaye.

Daga cikin abubuwan da kallon su ma ibada ne akwai kallon Iyaye, da Alƙur’ani, da kuma kallon kyakkyawan kamanni tare da kamalar Amirul Mu’minin Ali (a.s).

Haka kuma Imam Ali (a.s) ya bayyana cewa girmama iyaye yana daga cikin wajiban addinin Musulunci, kuma ya ce kyautatawa iyaye na daga cikin mafi kyawun alheri. Wane alheri ne ya fi girma fiye da mutum ya kasance mai tausayi da kyakkyawar mu’amala ga iyayensa a duniya, kuma kada ya manta da girmama su!?

A ci gaba da haka, Manzon Allah (s.a.w) ya ce: برّ الوالدین یجزی عن الجهاد

“Kyautatawa iyaye yana maye gurbin jihadi.”

Allah ya datar da mu ya saka mu daga cikin wanda su ke kyautatawa iyayensu.

 

Comments

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :