Hadisin Tuntsu yana tabbatar da babu kamar Ali a wajan Manzon Allah (sawa)
Daga Anas xan Malik ya ce: na kasance ina yi wa Annabi (sawa) hidima, sai aka kawo wa Annabi (sawa) gasasshen tsuntsu, sai ya ce: Ya Allah ka kawo min mafi soyuwar halittarka izuwa gareka, ya ci wannan tsuntsu tare da ni, Anasa ya ce: (sai na ce: ya Allah ka sa mutimin ya zama daga Ansaru –mutanen Madina-
Sai Aliyu -Allah ya kara masa yarda- ya zo, sai na ce: Haqiqa Manzon Allah yana wata buqata –wyana cikin wani uzurin. Sai Aliyu ya qara zuwa, sai na sake cewa haqiqa Manzon Allah (sawa) yana cikin wani uziri. Sai ya sake zuwa, sai Manzon Allah (sawa) ya ce: Buxe qofar, sai Aliyu ya shiga, sai Manzon Allah (sawa) ya ce: mene ne ya tsare ka ba shigo wajena ba?
Sai Aliyu ya ce: haqiqa wannan shi ne karo na uku ina zuwa amma Anas yana komar da ni, yana riya cewa kana kan wata buqata-kawana wani uziri.
Sai Manzon Allah (sawa) ya ce da Anas: Mene ne ya sanya ka aikata haka?
Sai Anas ya ce: Ya Manzon Allah na ji addu’arka, sai na so a ce wannan mutumin da ka roka ya zo wanaka ya zamanto yana daga mutanena.
Sai Manzon Allah (sawa) ya ce: haqiqa mutum yana iya zamantowa ya na son mutanensa.
Hakin Naisaburi ne ya rawaito wannan Hadisi a cikin littafin Almustadrak alas sahihaini, juzu’i na 3, shafi na 143, Hakinim ya ce: wannan hadisi ne ingantacce a bisa sharadin Bukhari da Muslim.
Sharhin Hadisin Tsuntsu
A cikin wannan hadisin za mu iya sanin abubuwa kamar haka:
- Ali shi ne mafi soyuwar dukkanin halittar Allah a wajan Allah bayan Annabi (sawa).
- Wannan kuwa yana nuna cewa babu wanda ya kai imam Ali (as) matsayi a wajan Allah a duk cikin sahabbabn Manzon Allah (sawa).
- Duk wani sahabi ko wani mutum daban idan ya ji wannan matsayi na Imam Ali to zai kwaxayin a ce shi ma yana da wannan matsayi.
















