Haihuwar Imam Mahdi (as)
An haifi Mahdi (A.S) wanda shi ne mai wanda ake yiwa Lakabi da (Munji) wato maiceton mutane na karshe a tsakiyar watan Sha’aban a shekara ta 255 bayan hijira. Kuma riwayoyi daban-daban sun tabbatar da cewa an haifeshi ranar Juma’a, wanda ya yi dai-dai da 29 ga watan Yuli na 869 Miladiyya.
Koda yake wasu sun tafi a kan cewa an haife shi a 254, was su kuma sun ce 256, wasu kuma suka ce an haiofe shi 257 ko 258 Hijiriyya. Amma wannan sbani baya rasa nasaba da boye haihuwarsa da aka yi, saboda yadda sarakunanAbbasiyya suka jiran labarin haihuwar domin su hallaka shi.
Auren Sayyida Narjis Khatun da Imam Hassan Askari
Imam Mahdi (AS) dan Imam Hassan Askari ne da Sayyida Narjis Khatun daya daga cikin zuriyar Kaisar Rum. Mahaifiyar Sayyidina Mahdi (A.S) diyar Yashu’a dan Kaisar na Rum ne. Sunanta na gaskiya shine Malika, bayan haka ta shahara da wasu sunaye kamar: Narjis, Rihana, Saqil, Susan da Hakim, amma Narjis ya fi shahara.
Yana da shekara goma sha uku sa’ad da kakansa, Kaisar na Roma, ya shirya wani biki mai ban sha’awa don a aurar da ita ga ɗan ɗan’uwanta; Amma saboda wani abin mamaki, gadon yayan nasa ya kife kuma ya mutu nan take. Bayan shi kuma aka sake shirya irin wannan biki don Malika ta auri daya daga ‘ya’yan xan uwan babanta, wata wani daga cikin jikokin Kaisar, amma shi ma ya mutu kamar dai wancan na farko.
A wannan daren sai Malika ta yi mafarki Manzon Allah (saww) ya daura mata auri da Imam Hasan Askari (as),tun daga nan si ta kamu da soyayyar Imam Hassan Askari da kauna mai yawa a cikin zuciyarta, har ta kai wannan yana hana ta ci da sha. Bin na ta ya ki kaewa hakan ya sa likitoci suka xebe kauna a kan samun lafiyarta cewa lallai ba za ta wannan rashin lafira ta ta ba za ta warke ba.
Daga karshe dai bisa umarnin Imam Hasan Askari, sai ta shiga cikin wadanda aka kama daga ribatattun yaki na Rumawa, sai Imam Hadi ya saye ta daga hannun Bishr bin Sulaiman, ya koma Samarra. Imam Hadi ya damka Sayyida Narjis ga ‘yar uwarsa Hakima ta koya mata hukunce-hukuncen Musulunci.
A karshen rayuwar Imam Hadi Imam sai Imam Hasan Askari ya auri Narjis, wacce ita ce ta haifi Imam Mahdi a shekara ta 255.
Yadda aka haihuwar Imamuz Zaman ta kasance
A daren 15 ga watan Sha’aban shekara ta 255 Hakima ta tafi gidan Imam Hassan Askari (a.s). Kusan faduwar rana sai ta yanke shawarar komawa lokacin da Imam Hasan ya ce mata ta kwana a can domin an kusa haihuwar Mahdi (as).
Sayyida Hakima da Sayyida Narjis sun yi sallah tare a wannan dare, suka sha ruwa saboda sun yi azumi a wannan rana, dare ya yi suka kwanta bacci, Bayan wani lokaci sai sayyida Hakima ta tashi cikin dare don ta yi sallar dare, sai ta Sayyida Narjis babu wata alamar lamar nakuda a tare da ita, Sannan itama sayyida Narjis ta farka don yin sallar dare, Sayyida Hakim tana cikin damuwa domin kawai tana jiran alkawarin Allah, kadan kadan sai shakku ya kusa mamayeta, sai Imam Hassan Askari ya yi mata magana.
A wannan lokacin Sayyida Narjis tana sallar Witiri lokacin da yanayinta ya canza. Sai Hakimeh ta ce: “Ana wannan halin, sai na ga wani labule ya rufe, don sai na daina ganin Sayyida Narjis. Ba’a dau lokaci ba sai ga labulen ya yaye, sai na ga Sayyida Narjis da wani haske na haskaka mata. Hasken ya yi tsanani har na kasa ganin ko’ina.
A wannan lokacin na ga wani yaro ya dora fuskarsa da gwiwoyinsa a kasa, ya daga ‘yan yatsunsa biyu zuwa sama ya ce: (Ash’hadu an la ilaha illallahu wahdahu la sharika lahu” “Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai ne, ba shi da abokin tarayya;
“wa ash’hadu anna Muhammadan abduhu wa rasuluhu” “Kuma ina shaidawa cewa haqiqa Annabi Muhammadu Manzon Allah ne, kuma Amirul Muminin Ali Babana ne. Sannan ya faxi sunayen limamai daya bayan daya har ya kai ga sunansa. Don haka sai ya ce: “Allah ka cika alqawarin da ka yi mini, ka sa na kammala aikina, Ka tabbatar da duga-dugaina, Ka cika duniya da adalci ta ta hanyata.
















