Da sunan ALLAH mai rahama mai jin kai, tsira da aminci su kara tabbata ga Annabi MUHAMMAD da iyalan gidan sa tsarkaka.
Matsayi da darajar da Sayyida Faṭima (SA) take da ita a wajen Imam Ali (AS) na nuna irin girman da mace za ta iya samu. Mace na iya kaiwa wani matsayi mai girma har ta zama abin alfahari da ƙima ga Imam (AS).
Girma da zurfin matsayin Sayyida Faṭima (SA) a wurin Imam Ali (AS) wani abu ne bayyananne a maganganun Imam Ali, a wurere da daman gaske Imam Ali (AS) ya bayyana matsayin Sayyida Zahra (SA) domin nuna fifikon sa da sauran Sahabbai, wannan rubutu zai kawo kadan daga cikin wuraren da Imam Ali ya bayyana girman nata a takaice.
A cikin amsar wata wasiƙa da Imam Ali (AS) ya rubuta wa Muʿawiya, ya ambaci wasu daga cikin falaloli da darajojin Sayyida Fatima (AS) kamar haka:
“Imam Ali ya kafawa Mu’awiya hujja da cewa kada ka manta da cewa mafi daukakar matan duniya (Sayyida Fatima) daga gare mu take, ku kuma su Mu’awiya حمالة الحطب wadda ke ɗaukar itacen wuta a Jahannama — daga gare su take.” Wannan wata Magana ce dake nuna matsayi irin wanda Allah ya bawa Annabi da zuriyar sa, a lokaci guda kuma yake nuna kaskanci da tabewar tsayan bangaren.
Imam Ali (AS) a cikin amsar wata wasikar da ya rubutawa Mu’awiya ya bayyana cewa: ’Yar Manzon Allah (SAW) ita ce matata, wadda naman jikinta ya gauraye da jinina da naman jikina. Jikokin Annabi Muhammad (SAW) ’ya’yana ne daga Faṭima (SA). Wane ne a cikin ku yake da rabo ko daraja irin tawa?”
A lokacin taron majalisar mutane shida da khalifa na biyu wato Umar bin khaddab ya naɗa don zaɓar magajin sa, Imam Ali (AS) ya ce wa sauran ’yan majalisar shura:
“Shin akwai wani a cikinku banda ni da matarsa ita ce shugabar mata ta duniya? Dukkansu suka ce: A’a.
A lokacin da aka yi batun Saqifa, Imam Ali (AS) yana lissafa falalolinsa da kamalansa, yana kuma bayyana cewa bayan Manzon Allah (SAW) shi ne ya fi cancantar shugabancin al’umma, sai ya ce wa Abubakar:
“Ina roƙon ka da sunan Allah! Shin wanda Manzon Allah ya zaɓa ya auri ’yarsa, ya kuma ce Allah ne Ya haɗa aurensu—ni ne ko kai?”
Abubakar ya amsa: “Kai ne.
Faṭima ginshiƙin Ali ce
Faṭima ginshiƙi ce ga Imam Ali
Daga cikin manyan darajojin da suka kebanta da Sayyida Fatima wanda Manzon Allah (SAW) ya gayawa Imam Ali akwai cewa Faṭima ginshiƙi ce ga Imam Ali (AS). A cikin wani ḥadisi mun karanta cewa Manzon Allah (SAW) ya ce wa Imam Ali (AS):. «سلام علیك یا ابا الریحانتین، فعن قلیل ذهب رکناك» aminci ya tabbata a gare ka, ya uban furanni biyu (Zaynab da Ummu Kulthum). Ba da jimawa ba ginshiƙanka biyu za su gushe.
Wannan magana lafazi ne mai daɗi da ya yi daidai da maganar Imam Ali (AS) game da mace lokacin da ya ce: “ إن المرأة ريحانة وليست بقهرمانةMace fure ce mai kawata gida ba wai hadimar namiji ba ce.
Bayan shahadar Sayyida Fāṭima (SA), Imam Ali (AS) ya ce mata:
بِمَنِ العَزاء یا بِنتِ مُحمد؟ کنت بِك اتعزی فَفیم العَزاء من بعدك؟»
Da me zan sami nutsuwa, ya ’yar Muhammad? Ni da ke nake samun sanyi da kwanciyar hankali. Bayan ki, da me zan sami sukuni?”
Bayan wafatin Manzon Allah (SAW) Imam Ali (AS) ya ce: Wannan shi ne ɗaya daga cikin ginshiƙaina biyu, bayan shahadar Sayyida Faṭima (SA) ya ce,wannan kuma shi ne ginshiƙi na biyu.
Mai Taimakawa wajen Biyayya ga Allah.
Annabawa da A’imma (AS) sun san cewa hanya guda daya ta samun tsiran mutum a duniya da lahira ita ce bin umarnin Allah. saboda haka, mafi kyawun aboki ko mataimaki gare su, shi ne wanda zai basu goyon baya a wannan tafarki na bautar Allah. Muna karantawa cewa lokacin da Annabi (SAW) ya tambayi Imam Ali (AS),Yaya ka samu matarka? (Sayyida Fatima) sai Imam Ali (AS) ya ce: نعم العون على طاعة الله
Madalla da mataimakiya akan biyayya ga Allah.
Wannan kadan ne daga cikin dubunnan wuraren da Imam Ali yake bayyana matsayi da girma na wannan shugaba ta matayen duniya da lahira kuma yake alfahari da hakan madallah da wannan zuri’a.
Allah ya bamu albarkacin su duniya da lahira.
















