Da sunan Allah mai rahama mai jin kai, Allah ya yi dadin tsira ga Annabi Muhammad da Iyalan gidan sa tsarkaka.
Nuna farin ciki ko bakin ciki wasu dabi’u ne daga cikin dabi’un da Dan-Adam ya kebanta da su, wanda Allah ta’ala ya sanya su daga cikin gimshiki na yanayin halittar Dan-Adam, idan da za’a ce za’a samu wani Dan-Adam wanda baya iya jin farin ciki ko bakin ciki to da za’a saka shi daga cikin jerin marasa lafiya, saboda hakan wani nakasu ne ga halittar Dan-Adam.
Farin ciki na kasancewa ne ga Dan-Adam a duk lokacin da wani abun da ya yi masa dadi ya faru gare shi, wanda shi kuma bakin ciki akasin haka ne, ma’ana idan wani abu bai yiwa mutum dadi ba yakan ji bakin ciki.
Saboda haka ne bayyana su yake nuni da cewa mutum ya na kan fidrar da Allah ya halicce shi da ita, sai dai kuma ba akan ko wane irin abu ba ne ya kamata a nuna wannan farin cikin ko bakin cikin.
كَيْلَا تَأْسَوْا عَلَىٰ مَا فَاتَكُمْ وَلَا تَفْرَحُوا بِمَا آتَاكُمْ (سورة الحديد 23)
Saboda kada ku yi takaici akan abin da ya kubuce muku, kuma kada ku yi murna da abin da ya zo muku (ku ka samu).
Alqur’ani mai girma ya bayyana mana irin abubuwa da ya kamata a bayyana farin ciki ko bakin ciki akan su.
Bisa la’akari da mukaddamar da ta gabata muna so mu fahimci cewa shin yin murna da farin cikin da Al’ummar musulmi su ke yi akan munasabobi na musamman kamar yin MAULUDIN ANNABI (sawa)da sauran Ma’asumai (A.S) na daga cikin wuraren da Qur’ani ya yi bayani a kan cewa za’a iya yin murna da farin ciki akai ko kuwa ?
Idan muka dubi ayoyin Alqur’ani mai girma za mu ga sun kasu kaso biyu, kashi na farko su na yin umarni da bayyana farin ciki da murna, wanda kashi na biyu kuma su na hani ko suka a kan yin murna akan wasu abubuwa.
Kaso na farko a cikin jerin ayoyin da su ke umarni ko yabo ga masu bayyana farin ciki;
قُلْ بِفَضْلِ اللَّهِ وَبِرَحْمَتِهِ فَبِذَٰلِكَ فَلْيَفْرَحُوا هُوَ خَيْرٌ مِمَّا يَجْمَعُونَ (سورة يونس 58)
Ka fadi da falalar Allah da rahamar sa ne za su yi farin ciki, shi yafi alkhairi daga duk wata dukiya da su ke tarawa.
وَالَّذِينَ آتَيْنَاهُمُ الْكِتَابَ يَفْرَحُونَ بِمَا أُنْزِلَ إِلَيْكَ (سورة الرع 36)
Wadanda mu ka zo musu da littafi suna yin farin ciki da abin da aka saukar zuwa gareka.
ويوْمَئِذٍ يَفْرَحُ الْمُؤْمِنُونَ بِنَصْرِ اللَّهِ (سورة الروم 4-5)
A wannan ranar ne muminai su ke yin farin ciki da nasarar Allah.
فَرِحِينَ بِمَا آتَاهُمُ اللَّهُ مِنْ فَضْلِهِ (سورة اّل عمران 170)
Alhali suna masu farinciki da abinda Allah ya basu na daga falalar sa…
Falala da rahamar Allah, Qur’ani da nasarar Allah, samun falala da baiwar yin shahada a dunkule, su ne abubuwan da wannan ayoyi guda hudu ke bayani akan cewa za’a iya bayyana farin ciki akan su.
Kaso na biyu daga cikin jerin ayoyin da ke hani ko suka a kan yin farin ciki;
إِذْ قَالَ لَهُ قَوْمُهُ لَا تَفْرَحْ ۖ إِنَّ اللَّهَ لَا يُحِبُّ الْفَرِحِينَ
Ka tuna lokacin da mutanan sa (KARUNA) su ka gaya masa cewa kada kayi farin ciki, lallai Allah baya son masu farin ciki (masu bayyana farin ciki saboda su nuna girman kai)
كَيْلَا تَأْسَوْا عَلَىٰ مَا فَاتَكُمْ وَلَا تَفْرَحُوا بِمَا آتَاكُمْ (سورة حديد 23)
Saboda kada ku yi takaici akan abin da ya kubuce muku, kuma kada ku yi murna da abin da ya zo muku (kuka samu).
حَتَّىٰ إِذَا فَرِحُوا بِمَا أُوتُوا أَخَذْنَاهُمْ بَغْتَةً…… (سورة الأنعام 44 )
Har zuwa lokacinda su ka yi farinciki da abin da aka zo musu da shi (a yanayi na girman kai) sai muka kama su ba tare da sun shirya ba…
(سورة الرعد 26) وَفَرِحُوا بِالْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَمَا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا فِي الْآخِرَةِ إِلَّا مَتَاعٌ
Sai su ka farinciki da rayuwar duniya a halinda rayuwar duniya dangane da lahira ba komai ba ce, face wani takaitaccen jin dadi.
Dukiya da duk wani abin duniyar da ku ka samu, rayuwar duniyar da zata mantar da mu lahira, su ne abubuwan da wadannan ayoyi hudun ke bayyana cewa yin farin ciki da su abu ne wanda bai dace ba domin su wadannan abubuwan da ku ke nuna farin ciki akan su, wasu abubuwa ne da ke iya kaiwa ga sabawa Allah.
















