Follow us in
Follow us in

Sayyida Zainab Alkubra yar Imam Ali (as)

Malamar da ba ta da Malami

Wace ce Sayyida Zainab (as)

Sayyida Zainab wacce aka fi sani da Zainab Kabri, ita ce: ‘ya  ta uku daga ‘ya’yan Sayyida Fatima Az Zahra da Imam Ali bin Abi Xalib (as).

Wato kenan jikar Manzon Allah (sawa) ce kai tsaye an haife ta a zamanin kakanta Annasbi Fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (sawa), kuma shi ne ya sanya mata wannan suna Zainab

Jaririya  mai albarka

Sayyida Faxima Az Zahra, (as), ta haifi wannan jaririyarta mai albarka, wacce ba a tava haihuwar mace irinta ba a Musulunci, wajan imani, da daraja, da tsarki, da tsafta, da jihadi sauran,  Ahlul baiti sun yi farin cikin da murna na samun wannan jaririya mai albarka.

Mahaifinta  Sarkin muminai Imam Aliyu (as) ya yi wa ‘yarsa bubuwab da sunna ta tanada don yi wa xa idan aka haife shi, don haka ya yi kira salla a kunnenta na dama, ya yi iqama a kunnenta na hagu. Sauti na farko da ta fara ji shine: (Allahu Akbar, Allah mai girma ne, babu abin bautawa da gaskiya sai Allah), kuma waɗannan kalmomin karatun annabawa ne.

Shekarar haihuwarta

A bisa zance mafi inganci an haifi Sayyida Zainab (as) a Madina, a ranar biyar ga watan Jumada Ula shekara ta biyar bayan Hijirar Annabi Muhammad (sawa).

Bakin ciki da kukan Annabi (sawa).

A lokacin da Manzon Allah (sawa) ya sami labarin wannan jaririya mai albarka, sai ya garzaya zuwa gidan iyalansa, yana cikin baqin ciki, sai ya xauke ta, hawaye yana zubo masa a kan fuskarsa mai albarka ya rungumeta a kirjinsa, ya fara sumbatarta, Sai Mahaifiyarta Sayyida Faxima, yi mamakin kukan mahaifinta.

Ita ma sai ta kama kuka, tana cewa: “Ya babana, me ya sa ka yi kuka? Sai ya amsa mata cikin sanyin murya mai ban tausayi: “Ya Fatima ki sani bayana da bayanki bala’o’i za su same ta…”(1).

Manzon Allah (sawa) ya san irin mugun bala’i da zai samu jikarsa, wadda za su sauka akan duwatsu da sun firgita za su narke, kuma za a yi mata jarrabawar da ba a tava gwada wa wata mace daga cikin ‘ya’yan Hauwa’u ba.

Sai ga Salmanul Farisi ya ya nufi wajan Imam Ali (as) yana yi masa murnar na samun wannan jaririya mai albarka

Sai Sayyida Zahra ta xauketa ta kai wa Imam, sai ya dauke ta, ya sumbace ta, sai Sayyida zahra ta jiya ga Imam Aliyu ta ce: Ka sa wa wannan jaririya suna. Sai Imam ya amsa mata cikin ladabi da kaskantar da kai da cewa: “Ba zan riga Manzon Allah (sawa) ba…”. Sai Imam Ali ya nemi Annabi da ya sanya mata suna, sai Manzon Allah (sawa) ya ce: “Ba zan gabaci Ubangijina ba…”

Sai Mla’ika ya sauka a zuwa ga Annabi, ya ce masa: “Ka sa wa wannan Jarirya Zainab, domin Allah ya zabar mata wannan suna…”

Ya gaya masa abin da jikarsazai sami wannan jikar tasana bala’o’i, shi duk Ahlul Baiti suka rushe da kuka (3).

Lakabobin ta

Sayyida Zainab (as) tana da lakabobi wadanda suke nuna irin falala da darajarta, da kuma irin kyawawan halayenta, wadannan lakabobi su ne kamar haka:

1.Aqeelatu Bani Hashim

Aqeela ita ce: Mace mai daraja a wajen jama’arta, kuma abar kauna a cikin ahallinta, kuma don haka ita Sayyida Zainab ita ce macen da ta fi kowa mace daraja a duniyar Larabawa da Musulunci, wannan lakabi ya zama wani tambari ga zuriyarta ana yi masu laqabi da (Banu Al-Aqeela).

2. Al’alima mai ilimi

Sayyida Zainab ta kasance daya daga cikin malamai a cikin iyalan gidan manzon Allah, kamar yadda wasu malaman tarihi ke cewa: “ta kasance matan musulmi suna komawa izuwa gareta a cikin lamurransu na addini (5).

3.Abida Aali Ali

Sayyida Zainab ta kasance daya daga cikin masu yawan bautar Allah a cikin mata musulmi, kuma ba ta bar wata sallar nafila ba face sai ta yi ta. Wasu maruwaita suna cewa: (har a cikin dare mafi tsanani kuma mafi daci, shi ne daren sha daya ga watan Muharram sai da ta yi sallolin nafila) (6).

4. Alkamila

Sayyida Zainab (as) Ita ce mafi kamalar mace a Musulunci bayan mahaifiyarta Sayyida Zahra da kuma kakarta Sayyida Khadija (as), a cikin kyawawan dabi’unta, da tsarkinta.

5.AlFadhila.

Tana daga cikin mafifitan matan musulmi a jihadinta, da hidimarta ga musulunci, da kuma irin jarabawoyin da ta fuskanta saboda Allah.

Aurenta da Abdullahi bn Jaafar

Abdullahi bn Jaafar bn Abi Xalib ya kasance daya daga cikin fitattun mazaje a

Musulunci kuma masanin Banu Hashim, kuma ana kiransa da “Bahrul judi” wato kogin kyauta(8).

‘Ya’yanta

Allah ya azurta Sayyida Zainab (as) maxaukaka masu daraja a musulunci su ne:

1.Aun. 2. Muhammadu sun yi shahada a ranar Ashura tare da Imam Husaini (as). 3. Abbas. 4. Ali Az-Zainbi. 5. Ummu Kulsum, wacce Imam Husaini (a.s) ya aurar da ita ga dan amminta Al-Qasim bin Muhammad bin Ja’afar.

Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Best Topics

Hotest Now

اشترک فی الاجتماعایت

Facebook
Twitter
LinkedIn
WhatsApp

للتحمیل اضغط هنا

الرابط المباشر

شارک مع الآخرین :