Watan Ramadan yana da girma da daraja a cikin Al-Kur’ani da Hadisan Ahlul Baiti (A.S). Ga wasu daga cikin falalar wannan wata bisa nassoshin Qur’ani da Hadisai:
Falalar Ramadan a cikin Al-Kur’ani
-
Watan Saukar Al-Qur’ani
- Allah (SWT) ya ce:
“Watan Ramadan ne wanda aka saukar da Al-Qur’ani a cikinsa, shiriya ne ga mutane da hujjoji bayyanannu daga shiriya da rarrabewa (tsakanin gaskiya da ƙarya).” (Suratul Bakara: 185) - Wannan yana nuna cewa Ramadan wata ne na shiriya da haske, wanda Al-Kur’ani ya sauka a cikinsa domin shiryar da mutane.
- Allah (SWT) ya ce:
-
Watan Wajibcin Azumi
- Allah ya ce:
“Ya ku waɗanda kuka yi imani! An wajabta muku azumi kamar yadda aka wajabta wa waɗanda suka gabace ku, domin ku ji tsoron Allah.” (Suratul Bakara: 183) - Wannan aya ta nuna cewa azumi yana da hikima da manufar koyar da takawa.
- Allah ya ce:
-
Darajar Lailatul Kadr
- Allah ya ce:
“Lailatul Qadri ta fi wata dubu.” (Suratul Qadr: 3) - Wannan yana nuna cewa daren Lailatul Qadri, wanda yake a cikin Ramadan, yana da falala mai girma fiye da shekaru 83 na ibada.
- Allah ya ce:
Falalar Ramadan a Hadisan Ahlul Baiti (A.S)
-
Farin Cikin Muminai da Ranar Biyan Ladansu
- Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Mai azumi yana da farin ciki biyu: farin ciki yayin da ya sha Ruwa bayan azumi, da farin ciki yayin da zai hadu da Ubangijinsa.” (Bihar al-Anwar, Juzu’i na 96, Shafi na 256)
- Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
-
Ramadan Wata Ne Na Gafara
- Imam Ali (A.S) ya ce:
“Ku azumci ranakun sa, ku yi tsaye da salloli a daren sa, saboda lalle shi wata ne wanda a cikinsa zunubai ke tafiya kamar yadda ganyaye ke zubewa daga bishiya.” (Bihar al-Anwar, Juzu’i na 42, Shafi na 190)
- Imam Ali (A.S) ya ce:
-
Mafificiyar Albarkar Lailatul Kadr
- Imam al-Baqir (A.S) ya ce:
“Daren Lailatul Kadr shi ne dare mafi alheri, Allah yana rubuta rayuwa, arziki, da kaddarar mutane a cikinsa.” (Al-Kafi, Juzu’i na 4, Hadisi na 2)
- Imam al-Baqir (A.S) ya ce:
-
Ramadan Wata Ne Na Rahama da Ceto Daga Wuta
- Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
“Idan watan Ramadan ya shigo, an buɗe ƙofofin Aljanna, an rufe ƙofofin wuta, kuma shaiɗanu an ɗaure su.” (Bihar al-Anwar, Juzu’i na 96, Shafi na 363)
- Manzon Allah (S.A.W) ya ce:
Kammalawa
Watan Ramadan wata ne mai falala, cike da albarka, inda Allah ke gafarta zunubai, yana karɓar ibada, kuma yana ba wa bayi damar samun rahamarSa. Ahlul Baiti (A.S) sun karfafa cewa a yi azumi da imani, a yi karatun Al-Kur’ani, a nemi gafarar Allah, a yi ibada cikin dare, da kuma taimakawa mabukata don samun ladan Ramadan gaba ɗaya.
Allah ya ba mu ikon amfani da wannan wata mai albarka yadda ya dace.
















