Watan Ramadan wata ne na gyaran kai da tsarkake ruhin dan Adam. Allah ya tanadi hanyoyi da dama don tsarkake zuciya da ruhin mutum daga zunubai, kuma ya bude kofofi da hanyoyi don samun tsarkaka da ci gaban Ruhi da Zuciya. Wannan wata dama ce mai girma ga mutane domin su zauna a kan teburin rahama da albarka, su ciyar da ruhinsu da abinci mai gina ruhi.
Manzon Allah (S.A.W.A) ya ce:
“Lallai Ubangijinku yana da lokuta na rahama a rayuwar ku, ku yi kokari ku kasance a cikinsu.”
A wani Hadisi na Qudsi, Allah ya yi wahayi ga Annabi Dawud (A.S) yana cewa:
“Lallai Allah yana da lokuta na rahama a rayuwar ku, ku neme su kuma ku ribace su.”
Watan Ramadan lokaci ne na gyaran zuciya da tsarkake kai daga duk wata cutar ruhi. Ba kawai azumi ne kadai hanyar samun gyaran kai ba, har da karatun Alqur’ani, yin addu’a da rokon Allah, taimaka wa mabukata da marasa galihu, samun hakuri da juriya, da kuma tunawa da Allah da ranar lahira. Dukkan waɗannan suna da rawar da suke takawa wajen gyaran kai.
Muhimmancin Addu’a a Musulunci
A cikin Alqur’ani da hadisan Annabi (S.A.W.A) da Imamai (A.S), an yawaita bayar da muhimmanci a kan yin addu’a.
Allah yana cewa a cikin Al-kur’ani:
“Ku ce: Ubangijina bai damu da ku ba idan ba don addu’arku ba.” (Suratul Furkan: 77)
Hakanan yana cewa:
“Ubangijinku yana cewa: Ku roke Ni, Zan amsa muku. Wanda suka yi girman kai wajen bautata, za su shiga Jahannama cikin ƙasƙanci.” (Suratul Ghafir: 60)
Daga cikin hadisan Manzon Allah (S.A.W.A):
“Addu’a makamin mumini ce, ginshikin addini, kuma hasken sama da ƙasa.”
Imam Ali (A.S) ya ce:
“Addu’a ita ce mabudin nasara da makullin samun rabauta.”
Ka’idoji da Laduban Addu’a
Kamar yadda kowace ibada take da sharuɗanta, haka nan yin addu’a yana da wasu ka’idoji da ladubba domin ta fi tasiri. Wasu daga cikinsu sun hada da:
- Fara addu’a da ambaton sunayen Allah da siffofinsa.
- Yin salati ga Manzon Allah (S.A.W.A) da iyalansa.
- Yin tawassuli da Annabi da Imamai (A.S) wajen addu’a.
- Yarda da zunuban da aka aikata tare da neman gafara.
- Yin kuka da rokon Allah cikin rashin girman kai.
- Yin sallah raka’a biyu kafin addu’a.
- Kada a yi wasa da kowace addu’a.
- Yin addu’a da zuciya mai tsafta.
- Yin addu’a a wurare da lokuta masu albarka.
- Maimaita addu’a da dagewa a kanta.
Dukkan waɗannan suna taimakawa wajen karɓar addu’a da kuma gyaran kai.
Darussa Uku daga Addu’a
Addu’a ba kawai don samun bukata ba ce, amma tana da wasu muhimman darussa guda uku:
- Yin addu’a don gujewa bala’i da samun biyan bukata.
- Yin addu’a yana motsa zuciya don samun kusanci da Allah.
- Fahimtar ma’anar addu’a da ilimin da ke cikinta domin samun ci gaban ruhi da zuciya.
Idan mutum yana addu’a amma ba a amsa masa ba, to yana da kyau ya tambayi kansa ko ya san Allah da gaske? Imam Ja’afar Assadiq (A.S) ya ce:
“Ana hana karɓar addu’arku ne domin ba ku san Wanda kuke roƙo ba.”
Watan Ramadan dama ce mai girma don yin addu’a, gyara hali, da samun kusanci da Allah. Ana bukatar mu yi amfani da wannan wata domin samun tsarkaka da inganta dangantakarmu da Ubangiji.
















